Sashe 187
Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
"No doctor, ka saka mata kawai" na gyara kwanciya ina kallon doctor ya gama arranging komai, yayi connecting tube din da cannula din hannuna sannan ya bude jinin, na bi jinin da kallo yana tahowa har naji ya fara shiga jikina. Na kwanta na lumshe idona, ina jin doctor din yayi min allura suka gama maganganun su da sultan sannan ya fita. Sultan ya dawo ya zauna a bakin gadon yana shafa kitsona yace "hey, har kinyi bacci?" Na dan bude ido bacci yana dauka na nayi masa murmushi, ya sunkuyo dai dai kunnena yace "it is not his blood". Abinda naji kenan bacci ya dauke ni. Sanda na farka kamar tsakiyar dare ne. Na kalli inda baby yake naga bayanan. Na fara dube-dube sai na Sultan a zaune kawai ya rike babyn a hannunsa yana kallo fuskarsa dauke da murmushi. Na jima ina kallonsu amma bai ma san na farka ba. Sai da nayi gyaran murya sannan yayi sauri ya juyo. Sai kuma ya kalli babyn yace "hey Al'ameen, let's go greet Mom" ya taso ya dora min shi a chinya sannan ya taimakamin na tashi zaune. Na dauki babyn na fara feeding dinsa, yana kallon mu ya jawo kujera ya zauna yace "Maimunatu, meet Muhammad Al'ameen. Yaci sunan Daddy, Muhammad, zamu kirashi da Al'ameen saboda gaskiya, rikon amana da jajircewa irin na masu sunan sa. Ina fatan Allah yasa yayi gadon not only their name but har halayyarsu" nace "Ameen. Nagode" yace "don't mention. Daddy yayi min komai a rayuwa, yayi min abinda babu wani wanda ya taba yi min kuma babu wanda zai kuma yi min nan gaba. Babban abinda yayi min shine ya bani ke. He gave me a life. Because you are my life." Nace "Sultan, kafin inyi bacci, naji kamar kace it is not his blood, whose blood is it?" Yace "daddy's. Muna fita zamu je gurin daukan jinin yace ba zai bayar ba. He said idan shine yasan ba zai so jinin tsohon saurayin matarsa a jikin ta ba. So, he wish for me what he wish for himself. I owe him that. Bazan manta ba" naji dadi a raina da hakan ta kasance. God is really amazing. Washe gari na fara tafiya, aka saka ni exercise na yi ta zagayawa a asibitin. Bayan na dawo daki Takawa yazo. Ummee dama tun sassafe tazo. Takawa ya dauki Al'ameen yayi masa addu'ah. Yana gama wa sultan ya mika hannu zai karbe shi, Takawa yace "au rowar sa zakayi min sultan? Daga dauka har zaka wani miko hannu a baka ko" sultan ya bata fuska "tun safe fa ban dauke shi ba, Ummee tunda tazo ta hana ni shi" Takawa yace "kwantar da hankalin ka, in aka sallameku kuka koma gida har sai ka gaji da daukan sa" Ummee tace "chafdi, ai bin su zanyi gidan nasu" Sultan har da bubbuga kafa a kasa kamar me shagwaba, Takawa yana yi masa dariya har da kyakyatawa. Hajiya ma tazo har asibiti ta duba ni, duk tayi sanyi babu wannan mulkin da dagawar. 'Yan'uwa da abokan arziki kuwa da basu samu zuwa ba sai waya suke min ana min barka, dan har kashe waya ta nake yi in dai ina son in samu bacci. Kwanan mu hudu a asibitin aka sallame mu. Tare muka tafi da daada tunda tana Abuja bata koma Niger ba. Muna koma wa gida ma bamu samu hutu ba, dan kullum gidan a cike yake da mutane. Ummee ta kasa ta tsare, daga baya ma hana daukan Al'ameen tayi sai dai duk wanda yazo ya kalle shi a hannunta ya tafi. Daddy yaji dadin saka sunan sa da aka yi sosai, Takawa kuma yace sunan yayi. Ana jibi suna Amina tazo zamuyi plans na taron sunan. Muna babban palo tare da sultan daya saka ni a gaba sai na cinye uban abincin da Ummee ta zuba min kafin ta tafi gida. Amina ta shigo da sallama, tun kafin ta zauna sultan yace "yana ganki ke kadai?" Tace "gashi can yana juya mota zai tafi" Sultan yace "ba zai shigo mu gaisa ba zai tafi?" Ya tashi ya fita sai gashi ya dawi shi kadai, yace "ya tafi, in ya dawo zai same ni" ni dai kawai kallon sultan nake ina mamaki. Amina tace "ina babyn kuma?" Sultan yayi ajjiyar zuciya yace "ummee ta tafi dashi" nayi dariya nace "kwantar da hankalin ki, in dai wannan acicin ne yanzu zaki ga an dawo dashi. Ai kuwa ba'ayi awa daya ba sai ga Fa'iza ta dawo dashi, tun suna daga waje muka jiyo kukan sa mukayi dariya, tana shigowa ta miko min shi tace "da kyar Ummee ta bani shi, wai ban iya daukan babies ba, wai sai dai ta kawo shi da kanta, Takawa ya hana shine ta bani shi da kyar" na karbe shi ina yi mata sannu na fara feeding dinsa. Su Hafsat ma duk ranar suka zo muka gama plans din suna. Ranar suna yaro yaci sunan Daddy kamar yadda akayi masa huduba, za'a ke kiran sa da Al'ameen. Raguna guda biyu Daddy ya aiko dasu na suna, Takawa ma ya kawo biyu. Taf palace ya cika da mutane, both daga part dina da kuma part din sultan. Da sassafe jirgin su Zayed ya sauka, yace akwai aiki a gabansa amma ba za'a barshi a baya ba gurin taron sunan nan, besides shima yayi missing family dinsa, yace wannan karon a England Hafsat zata haihu sai dai duk mai son ganin babyn ya bi su can. Kamar daga sama sai ga Amira sun zo tare da Mahdi, ya gama final exams dinsa ya zo gida, an saka bikin su wata uku masu zuwa. Muka rungume juna da Amira, ta dauki Al'ameen tayi kissing dinsa, na sa aka raka Mahdi gurin su Sultan bayan mun gaisa shima ya dau baby. Kayan barka kam su Hafsat sai karba suke suna ajjiyewa, mun sha kaya sosai dani da baby. 'Yan uwan ummi sunzo sosai daga Riyadh. Wadansu mutanen da suka zo ma ni ban san su ba sai anyi min bayani. Masoya ta ko ina bulluwa suke dan taya mu murnar samun little love din mu. Sultan shima nasa taron daban yake yi a part dinsa, abokan sa sunzo sosai daga parts da yawa na Nigeria. Gang bang sunzo suma, amma kamar yadda sultan ya taba gaya min, they are no longer a gang, kowa daban yazo, kowa ya girma ya samu rayuwarsa, babu sauran ganging kuma. Amira ma tazo tare da mamanta, ta gaya mana an saka bikinta nan da wata uku, kafin nan mahadi ya karasa final exams dinsa ya dawo. Sai dare sannan aka fara raguwa. Bamu muka samu zama ba sai wajan karfe goman dare. Nan kuma aka zauna hira a palo. Ibrahim yazo daukan Amina tare da little Moon, Sultan da kansa ya fita ya shigo dashi, suka shigo suna dariya kamar abokai, sultan ya dauki little moon ya dora akan cinyarsa yana tsokanarta yana ce mata matarsa, ita kuma bata san ma me yaki nufi ba. Amira ta gaishe da Ibrahim kuma ya amsa mata da sakakkiyar fuska sosai, suka gaisa da Mahdi a matsayin mijin da zata aura. Aka zauna aka cigaba da hira. Kadan kadan nake saka baki a hirar. Gaba daya hankali na ya tafi akan lissafin rayuwa, na kalli duk mutanen da suke zagaye dani, they are my friends and family, they are my life. And most importantly, they are happy. One episode more, and we are done Insha Allah.