← Book details Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 184 OF 190

Sashe 184

Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Episode Ninety Eight: My Baby Pre-eclampsia rare ciwo ne na masu tsohon ciki. Shine ciwon da yake saka mata convulsions (jijjiga) during labor. Alamominsa sune matsanancin hawan jini, kumburi, jiri, matsanancin ciwon kai, sensitivity to light, blurred visions etc. Matan da suke at risk of samun ciwon sune wadanda already suke da hawan jini kafin su samu ciki, wadanda mahaifiyar su ko sister din su ta taba yi, yara kanana da suka samu ciki da wuri ko kuma manya wadanda shekarun su suka ja sosai. In kina da ciki kuma kika ga kina da wadan nan alamomin dana lissafa a sama to kada ki yarda ki fara labor, it is very deadly, za'a iya rasaki ko babyn ko duk ku biyun, ko kuma ki samu wani mugun ciwon, wani lokacin har hauka ake haduwa dashi. In baiyi tsanani ba kuma cikin ki bai tsufa sosai ba, ana iya control dinsa, in yayi tsanani best solution shine ki tafi asibiti ayi miki aiki a cire babyn. Shikenan. Na rintse idona ina lissafa condition dina, a take na yanke shawara. Na bude idon na sauke su akan sultan, a hankali nayi magana "sultan stop the car" ya dan kalle ni yaga am serious sai yasa signa yayi packing a gefen titi. Ya juyo gaba daya yana kallona "Moon menene? What do you need? Jikin ne?" Na danyi masa murmushi kadan nace "asibiti zaka kaini ba gida ba" ya dan tsorata kadan "is the baby coming?" Na girgiza masa kai, "asibiti zamuje, za suyi min aiki su fitar da babyn" a take naga tashin hankali a rubuce a fuskarsa, na rike hannunsa sosai nace "don't do this sultan please, I need your support and strength. Please don't freak out" ya dan nutsu kadan yace "me yasa kika ce zasu yi miki aiki? Kince kuma ba labor kike ba" nan nayi masa bayanin duk situation dina da risks din da naje facing. Sosai naga hankalinsa ya tashi, ya daki stirring wheel da hannunsa yace "damn it, I hate that Ibrahim" na bata rai nace "Ibrahim bai dora min ciwo ba Allah ne ya dora min. Ba akaina aka fara ba ba kuma akaina za'a gama ba. Tunda na samu ciki lafiya lau nake, ko mugun laulayi banyi ba, wadansu matan daga ranar da suka samu ciki ba zasu samu lafiya ba har sai sun haihu. Wadansu matan talauci ya saka ko abinci mai kyau basa samu a lokacin da suke da ciki, wadansu matan basa samun medical care, wadansu matan zasi hadu da ciwo irin nawa amma basu san menene ba kuma su zo su fara labor a haka, a karshe su samu matsala koma su mutu gaba daya. Amma ni na samu komai, komai da nake bukata na samu, abinda nake bukata a yanzu shine support dinka, together we will get through this" ya dan nutsu ya dakata yana kallona, na mayar da idona na rufe inajin kaina tamkar zai rabe gida biyu, ga wani jiri da nake ji duk da cewa a zaune nake. Naji hannun sultan yana shafa fuskata, na dan bude idona ina kallonsa, na rike hannunsa da yake kan fuskata nace cikin sanyin murya "I need you to be strong" ya hadiye wani abu a makogwaronsa yace "yanzu me zamuyi" nace "asibiti zamuje. Amma please bana son ka kira kowa, Mommy da ummee in suka zo zasu kara min pressure ne. We can do this alone. Everything is going to be alright" da hannu daya ya dauko wayarsa yayi dialing, na fahimci doctor na yake kira, yana dauka ya fara masa bayanin abinda nace masa da kuma symptoms dina, banji mai doctor din yace masa ba yace "alright, we are on our way" ya kashe, hannun na yana cikin nasa ya kunna motar yayi reverse muka dau hanyar hospital, na koma na kwanta na rufe idona. Sama sama naji shigowar mu asibitin, naji sultan yana gayawa doctor a waya cewa gamu mun iso, hannunsa daya a rike da nawa dayan kuma ya saka yana shafa fuskata, na dan bude ido da niyyar in kalleshi amma hasken fitulun cikin asibitin ya saka na mayar da idona na rufe ba tare dana kalle shi din ba, naji zuwan doctor gurin mu, ya kunna fitilar wayarsa ya haska ni, na kara runtse idona saboda bana son hasken, yace da sultan "gwara da Allah yasa kuka taho yanzu baku zauna kunce sai safe ba, she is in critical condition and we will have to take the baby out now" sultan yace "yes, haka tace". Doctor din ya tafi sai ga wasu nurses sun kawo gadon daukan marasa lafiya, sultan ya chika hannuna ya zagayo ya dora ni akan gadon aka tura ni zuwa cikin asibitin. Ko sau daya sultan bai cika hannuna ba har aka kaini dakin da za'a shiryani. Doctor ya kawo wa sultan takardu yayi signing, har zai fita sultan ya tsayar dashi ya fara magana muryarsa kamar wanda zaiyi kuka yace "doctor please, nasan kasan aikinka ba wai koya maka zanyi ba, but please if anything should arise, in kana ganin Moon zata iya samun wata matsala, please doctor just forget about the baby and save my wife. Gwara in rasa shi akan ace wani abu ya same ta" doctor ya dawo ya tsaya a gaban sultan ya dora hannunsa akan kafadar sa, fuskarsa da murmushi yace "Our Prince, insha Allah nayi maka alkawarin zan kawo maka matarka da dan ka lafiya lau, babu abinda zai same su duk su biyun" sultan ya danyi murmushin yake yace "thank you doctor" doctor yace "amma nima ina bukatar wani taimako daga gareka, akwai maganar da zamuyi ka biyo ni office yanzu" sultan ya dan juyo ya kalleni yace da doctor din "bazamu iya maganar anan ba? Cos I don't want to leave her alone" doctor yace "OK, sai muyi anan din" suka zauna akan kujera doctor ya fara magana yace "kaga dai halin da take ciki yanzu, dan haka dole ba zamuyi mata anaesthesia ba, muna bukatar control over her bp, in muka yi mata allurar bacci ba zamu samu wannan control din ba, we need to keep her awake through the entire operation. Da akwai aikin da ake yi na ido biyu, zamu kashe lower part of her body yadda ba zata ji zafin komai ba har mu gama. Taimakon da nake nema a gurinka shine ina so ka shiga operation room din a tare damu ka zauna a kusa da ita kana yi mata magana mai dadi wacce zata kwantar mata da hankali" sultan yayi saurin girgiza kansa yace "I can't watch" doctor yace "you won't. Zamu saka labule a saman cikin ta mu raba ta biyu, her upper part tana gurinka zaku ke maganar ku, her lower part yana gurin mu muna aikin mu, baza kusan ma muna yi ba sai in mun gama muyi muku magana. Just don't let her sleep" sultan ya gyada kai yace "OK. I can do that" doctor ya mike tsaye yace "and we will need blood, just in case" da sauri sultan yace "you can take mine" doctor yayi murmushi yace "in yayi matching da nata ba. Zamu gwada mu gani in yayi dai dai sau mu dauka, in baiyi dai dai ba kuma sai ka samo mana wasu 'yan'uwanka ko nata a gwada a cikinsu ko za'a samu". In less than one hour da zuwan mu asibitin har an shirya ni suma doctors din sun shirya, duk abinda suke ina jinsu amma bana cewa komai saboda magana ma kara min ciwo take, idona kuma a rufe saboda bana son haske. Sai da aka tura gadona cikin theatre room sannan nayi nadamar cewa da nayi kar a kira kowa, ji nayi babu abinda nake son gani irin Mommy na da Daddy na, kuka naji yana taho min, nayi sauri na mayar dashi dan nasan ina fara kuka zan kara wa kaina ciwo kuma sultan zai kara rikicewa, so far dai yayi abin kirki sai dai ko dai dai da second daya bai matsa daga kusa dani ba. Muna shiga suka yi min wata allura a tsakiyar bayana mai dan karen ciwo, amma tana shiga naji kamar an yanke min daga cikina zuwa kafafuwana, kamar ba'a jikina suke ba, na juya ina kallon sultan wanda idonsa ya kada yayi jawur nace "ka kira daddy ka gaya masa. At least they will pray for me" ya dauko wayarsa, na lura hannunsa har rawa yake, bai iya kiran Daddy ba sai text ya tura masa. Aka sauko da labule aka raba jikina biyu. Sai ya zamana kamar ba'a daki daya muke da doctors din ba, jikina ya bani sun fara aikin amma banji komai ba. Na kalli sultan daya kankame hannuna kamar za'a kwace ni, nace "naji kamar cewa akayi kayi min hira" ya danyi murmushi nervously yace "labarin me kike in baki" nace "anything. Kamar the best day of your life" yace "da akwai ranaku da yawa da zan iya kira da best days of my life. Kuma duk days din da akwai ki a ciki. Because you are my life. Rana ta farko ita ranar dana fara ganinki. It was the day that my life begun. Daga nan sai days din da muka yi spending a America, I will never forget those days. Daga nan sai ranar daurin auren mu and then our first night, you took away not only my body but also my soul. Then, ranar da Takawa ya kira ni da his little love and asked for my forgiveness. Sai ranar dana fara ganin Ummee na. Sai kuma ranakun mu a Maldives" yayi murmushi yace "seriously ban so muka dawo ba" nayi murmushi nima, yace "rana ta karshe a yanzu ita ce yau, ranar da zamu ga result of our love. Zamu raine shi together, mu bashi tarbiya da soyayya da kulawa, we will give him all the things that I missed in my childhood. He is going to grow up to be better than me saboda he have the best mother in the whole world" I was so lost a maganganun sultan har na manta ma aiki ake min, sai kawai kukan baby muka ji, muka yi murmushi a tare, doctor ya dan daga labulen yace da sultan "a miko
Chapter 184 · 0% Book details