← Book details Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 111 OF 190

Sashe 111

Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

kuma nasan ba iya tukin dare nayi ba kuma Mommy bata san ma na daukar mata mota ba dan duk a tunanin ta tare muka fita. Na fito na zagaya na shiga seat din baya na zauna, har yanzu dariya yake ya tayar da motar muka tafi. Har muka je gida ba wanda yayi magana. Muna packing na fito, ya fito shima ya sha gabana yace "thank you for today, I really had I great time" bai samu amsa ba na zagaye shi na shige gida. Seriously ni Sultan tsoro yake bani. Tuesday Yaune kunshi da bridal shower. Tun sassafe akayi shimfidu a compound, madu kunshi suka zo, ni kam sam bacci bai ishe ni ba haka aka taso ni wai lallai ta kaina za'a fara kunshin. Jan lalle aka fara yi min, ana fara wa 'yammata suka zagaye ni aka fara wakar gada ana tafi. Hannu da kafa duk akayi min, ni kaina lallen yayi min kyau musamman saboda gyaran da fata ta tasha. Ana gamawa nace Amina ta daukar min shi a hoto ta turawa Sultan, tana ta dariya nace tayi shiru kar mutane suji. Tana tura masa ya turo min reply din kisses. A baki Hafsat ta zauna taba bani abinci ina ci har na koshi. Nan akayi ba'ki shima akan jan. Ai fa nan take na fito amarya ta sak. Tsofaffi sai guda, 'yammata sai waka. Ana gama wa dani aka koma kan sauran 'yammata. Mai kunshin ce ta dawo gurina tace "bara inyi miki wani abu as my wedding gift" nace "me fa?" Tace "wait and see" riga ta ta daga tana min wani abu a kasan kafada ta, ni dai dariya nake yi har ta gama, Amina nasa ta dauko min hoton gurin in gani, ina dubawa naga wani design tayi da bakin lalle mai kyau, a tsakiya ta rubuta S & M. Yayi kyau sosai, nayi mata godiya. Sai wajen la'asar aka gama kunshin dan har su daada dai da aka yiwa, wai suma sai sunyi gayu,lol. Ni dai ana cire min nawa na tafi daki nayi wanka na shirya cikin wata doguwar riga ta ta lace orange color, tayi bala'in yi min kyau dan kana gani na ba sai an gaya maka ba kasan nice amaryar. Dakina a cike yake da 'yammata ana ta shirye shiryen bridal Shower, su Hafsat kuwa ana waje ana making arrangements na gurin da za'a yi event din. A garden din gidan mu za'ayi, decorators already sun shirya gurin sai dan abinda ba'a rasa ba. Ana sallar magrib mai kwalliya tazo, Fauziyya tace "to ina kayan da amaryar zata saka ne wai?" Amina ta tabe baki tace "oho, sai ku tambaye ta, nima ban sani ba" na kira sultan nace ya aiko min da kayan yau, duk suka saki baki suna kallona, Hamidda tace "wai kina nufin kayan da zaki saka suna gurin angon?" Nace "yep" basu karasa mamaki ba sai da Maryam ta shigo da kayan a 'yar karamar jaka, suka buda duna kallo, doguwar riga ce fara tas, mai hannun vest, wuyanta ya shiga ciki sosai both gaba da baya, sai wani dogon siririn veil mai kamar jela irin wanda ake nannadawa a wuya ash color, takalmi da jaka ta ma duk ash ne, suna fito da kayan sai ga brazier da pant a kasa, a tare suka saka salati, ni kaina sai da nayi dariya, suka juyo suna kallona nace "wallahi ban san ya siyo da underwears ba" Hasiya tace "amma wannan angon shine number one a marasa kunyar Nigeria" Amina tace "Ai in da akwai number zero to Sultan ne" Sai da nayi sallah sannan ta fara yi min, a kawayena har da masu recording kwalliyar a video. Na saka kayana sannan muka fita ta kofar baya gurin event din, muna zuwa Hafsat ta dora min crown a kaina sannan ta rataya min tag da aka rubuta 'Bride' a jikinsa. Ni nayi shigar fari tas sauran duk mutanen da suke gurin kuma sunyi shigar baki, kowa a ganni a ranar sai ya sake kallo. An saka securities sun tare hanyar garden din babu namijin da zai shiga. Gaskiya tun a ranar nasan ina da kawaye masha Allah, dan har wadanda ban saka ran zasu zo ba sun zo. Ina jin waya ta tana ta kara a cikin jaka kuma nasan Sultan ne amma naki dauka na rabu dashi. Aka kawo min cake dina shima fari da kwalliyar baki, Hafsat ta taya ni muka yanka, akayi ta pictures daga nan kuma aka fara dancewa. Muna ta enjoying kan mu bamu san lokaci yaja ba sai da Mommy ta aiko tace ya kamata a tashi haka tunda da akwai masu nisa, sannan muka duba time muka ga after 11. Mommy ta saka drivers din gidan suka yi ta jigilar kai mutane gida. A gajiye na shiga daki na fada kan gado duk jikina yana min ciwo. Gashi banyi sallar isha ba, wanka na fara yi sannan nayo alwala na fito nayi sallah sannan nayi shirin kwanciya. Sai da na kwanta sannan na dauko waya na kira sultan, yace "wato yau wannan matar kin manta dani ko?" Nace "ni na isa? Gurin da hayaniya in ma na dauka ba zaka jini ba" yace "to kuma shine ni ko a nuna min kwalliyar ko?" Nayi dariya nace "wannan kwalliyar ta yau tafi karfin idonka, ka bari zan ajiye maka pictures, randa duk ka kai matsayin gani sai in nuna maka" yayi ajjiyar zuciya yace "I can't wait" ban bashi amsa ba nace "good night Sultan" yace "fi amanillah" Wednesday Bacci nayi sosai da safe na huta, Sultan ne ya tashe ni da waya wai lallai yana son ganina kafin ya fita, da sauri sauri muka gaisa ya fita saboda mutane. Ranar anti Zaliha tazo, na gaisheta tace "Moon an samu abinda ake so ko? To baza muyi miki baki ba, Allah ya sanya alkhairi" sum sum na tashi na fice daga dakin. Rumfar motocin gidan aka gyara aka kwashe motocin gidan, anan za'ayi kamu. Ranar shigar atamfa nayi purple mai adon pink, sosai kalar atamfar ta kara haska fata ta, plain zani ne, na daura shi akan rigar, ana gama yi min kwalliya na shiga toilet na saka shower cap na rufe gashina tsaf da ita sannan aka daura min dankwali aka saka net aka rufe fuskata. Suna ta mamakin me yasa na saka shower cap a kaina ni kuwa nasan dalili. Nani ce tazo tare da mata da yawa daga fada. Dubu dari biyu suka ajiye da akwati guda na turaruka, sannan suka feshe ni da turare, daga nan aka bude fuskar amarya aka tayi min ruwan kudi, both dangin sultan da nawa. Sai da aka kusa gamawa sannan Hajja tazo tace sam kamu bai yi ba tunda ba'a zuba min nono ba, ai ni bafulatana ce dan haka da nono za'a kama ni. Kamar yadda tayi alkawarin sai tayi min wanka da nono haka tayi min, Mommy ta kule kamar zata yi kuka ni kuwa dariya ma nake yi abina, sai yanzu kawayena suka gane amfanin shower cap din dana saka. Ana gamawa direct toilet na shiga nayi wanka da special sabulu na, babu wani sauran karni daya rage a jikina. Bayan munyi sallar magrib kuma aka shirya tafiya walima. Doguwar riga na saka yellow mai adon golden stones, na saka jaka da takalmi suma golden, ina shiryawa na kira Sultan video call na nuna masa kwalliya ta, nan fa yace shi baiga dalilin da za'ace babu maza a walima ba, ai suma suna bukatar ayi musu wa'azin yadda zasu rike matan su, nace masa ai anayi amma suma du kadai banda mata, da kyar muka rabu wai bai gaji da ganina ba. A abuja national mosque akayi walimar, anyi wa'azi sosai da nasihohi masu ratsa jiki kuma duk akan zaman aure, da kuma sirrika na rike miji bisa sunna. Naji wa'azin sosai dan jikina gaba daya dai da yayi sanyi. Muna dawowa gida na tarar Sultan yana jira na waishi lallai bai gama ganin kwaiya ta a waya ba sai ya gani a fili. A mota muka zauna ya fito mana da fura da nono mai sanyi da tsire, muna ci muna hira, ni har na manta ma bikin mu ake yi dai da amina ta kira ni tace "kinsan dai in baki yi bacci ba zaki tashi da kumburaren ido, kuma kwalliyar ki ba zata yi kyau ba" a raina nace 'oh Amina ko passion design kika karanta sai haka'
Chapter 111 · 0% Book details