← Book details Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 185 OF 190

Sashe 185

Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

maka shi ka rike?" Sultan yayi saurim girgiza kai yace "babu hannun da zan rike shi dashi, I won't let go of her hand. Sai dai ku ku rike shi a wajanku" doctor ya saki baki yana kallon sultan, shi kuwa ko a jikinsa, nace "doctor kawo min shi ni in rike shi" doctor yace "ke kina ji da kanki ina ke ina rike baby? Ka rike ta da hannu daya sai ka dau babyn da dayan hannun, shi yasa Allah yayi maka hannu biyu saboda kayi two things at the same time. Kuma idan yaron nan ya girma sai na gaya masa" ya koma sai gashi ya dawo da baby a cikin towel, har yanzu kuka yake ta tsanyara wa, sai kuma naga sultan ya cika ni ya tashi ya karbe shi, fuskarsa cike da farin ciki, na fara lissafin yanzu fa dinke ni akeyi sai kuma nayi sauri na kawar da wannan tunanin daga raina, sultan ya zauna ya juyo min da fuskar babyn yace "look Moon, he is perfect. Dake yake kama" na kalli babyn, ba dani yake kama ba, hancinsa da bakin sa irin na sultan, idonsa da kuma kalar fatarsa irin nawa ne. Na saka hannu na shafa kansa nace "Allah yayi maka albarka". Sai da aka gama dinke ni tas, suka gwada bp dina suka ga cewa is almost stable sannan sukace zan iya yin bacci yanzu, suka yi min allurar bacci. Tun kafin a gama zare allurar nayi bacci. Sanda na farka a wani dakin daban na ganni, babu ciwon kan kuma gani na ma ya fara dawowa dai dai, sai azaba da naji a gurin da aka bude cikina, na dora hannuna a gurin naji kamar inyi ihu saboda zafi, na hango sultan a zaune akan sallaya, daga alama sallah ya idar, babu kowa a dakin sai shi kadai. A hankali nace "Sultan" ya juyo da sauri ya taso yazo gurina "Moon? Wani abu yana miki ciwo? Me kike so?" Na nuna masa gurin aikina yace "bara in kira doctor" nace "Mommy tazo?" Yace "suna can sun hada kai ita da Ummee suna kuka a waje" na danyi murmushin yake, kafin ya bar gurin wani baccin ya sake dauke ni. Farka wa ta ta biyu Mommy ce a zaune a kusa dani, idanuwanta sun kumbura kamar zasu fado kasa, fuskarta tayi jawur. Na jima ina kallonta bata san ma na farka ba. A hankali nace "Mommy ki daina kuka, ba mutuwa zanyi ba, the worst part is over. Allurar bacci ce kawai take dibana" ai kuwa kamar cewa nayi Mommy yi kuka, nan da nan hawaye ya fara zuba, ta rike hannuna "Moon na shiga uku, ina can ina wurin dinner ke kina asibiti ana bude cikinki. Why didn't you tell me?" Nace "am sorry mother" na kalli agogon dakin naga 4:30, amma kuma ga rana ina kallo ta taga, this means har gari ya waye yamma tayi kenan. Na duba naga drip a hannuna, shi yasa banji yunwa ba. Akwai sauran ciwon kan kadan amma ina gani tas yanzu. Kumburin ma ya ragu. Nace "Mommy ina Daddy?" Tace "dazu ya tafi, ya zo sau biyu yana ganin ki, sun hana shigowa ne saboda kar a tashe ki. Shima wancan rigimammen an fita dashi yana ta tsala kuka, daga ganin sa acici ne. Bara inje in karbo shi sai a gwada feeding disa ko zai sha" har takai bakin kofa sai ta juyo tace "Allah yasa Khairat ta bani, dan ta hana kowa, duk wanda zai ganshi sai dai ya kalle shi a hannunta" nayi murmushi, dama nasan abinda zai faru kenan. Ai kuwa Ummee bata bawa Mommy ba, sai gata da kanta ta taho dashi, ta zauna tana yi min sannu, ina so in sake ganin fuskarsa amma ta kudundune shi a jikinta, tace "kafin ince komai, tell me, idea din waye a cikin ku kuka taho asibiti ba tare da kun gaya wa kowa ba?" Nayi shiru bance komai ba, tace "you almost give us a heart attack. Mun dauka kuna gidan biki, du kuma sun dauka kun dawo gida" nace "we are sorry Ummee" ta shafa kaina tana murmushi tace "ya jikin ki? Menene yake miki ciwo yanzu?" Nace "babu komai" tace "gurin aikin fa?" Nace "yana yi kadan. Nasan zasu zo anjima suyi min allura" sai a lokacin ta miko min babyn, sai kuma naji inajin kunyarta naki karba, Mommy ce tazo ta dan daga ni kadan tasaka min pillows a baya na sannan ta karbi babyn ta dora min a kan kirjina, na saka hannu na tare shi dan kar ya sauka kan ciwo na, ni duk kunyar Ummee nake ji ita kuma taki ta gane ballantana ta fita. Mommy ta fahimci kunya nake ji tace "Khairat ko zaki zo muje mu gano masu gwajin jinin can ko an dace an samu wanda yayi?" Ba tare data kalle taba tace "jeki kawai Fatima, gwara in zauna a gurinta kar mu barta ita kadai" Mommy tayi ajjiyar zuciya ta daga kafada ta fita. Na rasa yadda zanyi gashi shi kuma har ya fara kusur kusur yana tabe baki zaiyi kuka, Ummee tace "what are you waiting for? Feed him gashi nan zaiyi kuka. Tun da yazo duniya baici komai ba sai dan dabino da zam zam da babansa ya bashi" ya na iya da raina, dole na gyara riga na bashi, ai kuwa da sauri ya karba kamar yasan menene, ya nutsu sosai yana sha, na kura masa ido ina kallo, I can't believe wannan perfect halittar daga jikina ta fito, Allahu Akbar shine abinda kawai zan iya fada. Na bashi ring finger dina ya rike da hannunsa, sai kawai naga ya bude ido yana kallona, nayi masa murmushi sai kace yasan me nakeyi. Ummee ta zagayo ta bayana ta lakuce masa hanci tace "like father like son" Sultan ne ya shigo ya tsaya daga bakin kofa yana kallon mu, fuskarsa filled with feelings, Ummee tayi masa alamr ya shigi da hannunta, ya karaso ya ajiye ledar hannunsa yana kallona yace "ya jikin?" Na sunkuyar da kai nace "da sauki" ya matso kusa da gadon yana kallon babyn yace "an samu abinda ake so kenan, za'a bar kunnen mu ya huta" sai da ya gama sha dan kansa ya cika sannan na gyra rigata, Ummee ta karbe shi ta saka shi a kafada yayi gyatsa sannan ta bawa sultan shi tace "zauna in yi muku pictures" ba musu ya zauna a gefen gadon ya jawo ni jikinsa da hannu daya, daya hannun kuma ya rike babyn a jikin mu, Ummee tayi mana pictures da yawa. Ya dauko ledar daya shigo da ita ya fito da fruits, ya dauko ayaba ya bare ya miko min yace "doctor yace zaki iya cin fruits" na karba na fara ci sai muka ji anyi knocking kofa, Ummee ta saka min mayafi aka turo kofar, mutane suka fara shigowa kamar va zasu kare ba. Hafsat tana kan gaba, da sauri tazo ta dauki babyn daga kan cinyata tana cewa "shine ka hanamu karasa bikin mu ko?" Hatta amare da angwayen jiya duk sunzo, a raina nace 'jiya na hana first nights da yawa' Amina tazo tana yimin sannu, Zainab da Fadila, saratu da Faiza, Huda da Aishan Amir duk suka zagaye ni, mazan kuma suka tafi suna gaisawa da Sultan. Ina kallon Ibrahim ya mika wa Sultan hannu amma yaki karba, sai ya wayance da bare min ayaba. Ana ta hayaniya ana daukan hotu a ba baby, Ummee kuwa sai cewa take a daina jagwalgwala shi kar yayi ciwon jiki. Ni kam sai kallon su nake ina jin dadi a raina. Daddy yayi sallama ya shigo, ji nayi kamar in tashi inje in rungume shi, bai kula kowa ba har masu gaishe shi ya taho gurina bakinsa har kunne, ya sunkuyo yayi kissing dina a goshi yace "well done my daughter. Barakallahu fi ki" ya zauna a kujera yace ku kawo min wannan ragon mazan daya kasa jure taron biki" akayi dariya gaba daya. Aka mika masa shi ya karba yayi masa addu'ah sannan yace "Sultan wannan ai kayi wa Moon yawo" Sultan ya karasa kusa dashi ya leka fuskar babyn yace "wannan idon ba nawa bane Daddy, kuma daga dukkan alama sai yafi ni haske" duk akayi dariya, ya Habeeb yace "Sultan in surukai suna magana aka akan dan mutum baya amsawa" Sultan yace "Daddy ai ba suruki na bane" a raina nace 'koma waye yayi magana amsa zaka bashi'. Doctor ya bude kofa ya shigo. Yana kallona yace "Maman baby an tashi kenan, at last" nayi murmushi na gaishe shi, ya zo dudduba ni ya bani magungunan da zansha, yayi min allura a hannu, yace "zamu sake miki allurar bacci in an jima, saboda kamata yayi ace kinyi 24hours kina hutawa" sannan ya dauko takarda yana kallon mazan gurin yace "ga result din tests din da akayi muku na jini. Abbakar Sadiq Abdallah, jininka bai yi dai dai ba" su ya walid har da yiwa sultan dariya ganin yadda ya bata rai. Doctor yace "Lawan Muhammad Dikko kaima naka baiyi ba, Habeeb muhammad dikko naka kaima baiyi ba, Faruk Muhammad dikko kaima zero" akayi musu dariya suma gaba daya "Abbas sadiq abdallah kaima baiyi ba, Abdullahi Abdallah kaima zero, Adeniran Ibrahim, congratulations, kai kayi winning, naka yayi matching, mun gwada kuma munga it's free of all blood transmitted diseases, in ka shirya sai muje mu diba" gaba daya aka juya ana kallon Ibrahim, shi kuma ya kalli sultan, sultan kuma ya kalleni, ni kuma na sunkuyar da kaina.
Chapter 185 · 0% Book details