Sashe 13
Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan munyi wata daya da fara term din su mommy suka zo mana visiting. Tun da aka kira mu gaba na yake faduwa dan bansan me Hafsat zata kulla min a gurin mommy ba. Muna tafiya zamu je gurinsu na matsa kusa da Hafsat nace mata "what are you planning to tell mommy? " ta kalleni da murmushin mugunta tace " that's my business, me kike ci na baka na zuba? " na hadiye yawun tsoro cikina ya kulle kamar zanyi zawo a wando amma na daure na cigaba da binta a baya kamar munafuka. Muna zuwa visitors room sai muka tarar da daada da faruk, nan da nan na manta da damuwar da nake ciki na fada kan cinyar daada ina murnar ganinta, Hafsat ma tazo ta rungume ta muna ta dariya daada tace da yaren buzanci "kai ni karku ji min ciwo, ku baku san kun zama 'yan mata bane" nace mata "haba daada, ina abin yake? Sai dai ki gaya wa Hafsat bani ba" Hafsat kuma tace "ai komai girman da zanyi bazan daina hawa cinyar kiba daada" muka sake yin dariya. Faruk yana zaune yana kallon mu nace "autan mommy ko magana babu?" Yace "au kuna gani na? Na dauka ai ni invisible ne tunda babu wacce ta kula ni a cikin ku" nan kuma muka tafi da gudu a tare muka rungume shi yana turemu wai yayi fushi. Hafsat ce tace daada wai ina mommy n ne? Daada tace "muna zuwa principal dinku ta kira ta" nan take wani gumi ya karyo min, tunda muka shigo ban ga mommy ba na dauka bata samu damar zuwa ba har hamkali na ya kwanta. Nayi saroro har wani daci nake ji a baki na. Hafsat ta dafa ni tace "yayane moon? Ko bakya murnar ganin mommy ne? " na ture hannunta na koma kusa da daada ina tambayar ta su ya Habeeb. Muna cikin haka sai ga messenger daga principal's office wai ana kiran mu nida Hafsat. Muka tashi muka tafi, nice a gaba Hafsat tana bina. Ina tura kofar office din naga mommy a zaune a kujerar gaban table din pc daga can gefe kuma Ibrahim ne a zaune yayi folding arms dinsa yana kallon mommy. Sandarewa nayi a gurin na kasa motsi, komai nawa ya tsaya hatta bugun zuciya ta. Hafsat naji tana fadin in matsa in bata guri ta shigo tunda ni bazan shiga ba. Sai a sannan lumfashi na ya dawo si kuma zuciyata ta fara bugawa da karfi, dacin da nake ji a baki na ya karu, Hafsat ta karewa office din kallo sannan tazo dai dai kunnena tace min "whatever goes up must come down" tana yi min murmushin mugunta ta shige ciki da sallam. Ba yadda zanyi dole na bita a baya. Ga mamaki na sai naga mommy ta juyo da fara'a sosai a fuskar ta ta mike tsaye ta buda hannayenta tare da cewa "come here my darlings" ban san sanda na manta da komai ba na fada jikin mommy ina murna. Ta rungume mu sosai a jikinta na wani lokaci sannan ta sake mu, muka gaisheta, muka gaida pc sannan na juya na gaida Ibrahim. Hafsat ko kallon inda yake bata yi ba mommy kuma bata lura ba dan suna magana da pc a lokacin. Sun jima suna magana amma ni hankali na ya tafi akan tunanin dalilin wannan kiran da akayi mana kuma gashi an kira Ibrahim shima, lokaci lokaci inna daga ido na sai mu hada ido da Ibrahim sai ya sakar min murmushi amma ni kam ranar bani da damar mayar masa dan gaba daya hankali na a tashe yake.
Sai da suka gama hirar su sannan mommy tace " I am very proud of you Moon. Tun ina gida aka aika min da report na yadda karatunki yake progressing, naji dadi sosai. PC ta gaya min cewa ashe kun dai daita da sabon copper din da da kike complaining akansa, tace yanzu har extra lessons yake yi miki kuma kina samun cigaba sosai" bani ba hatta Hafsat sakin baki mukayi muna kallon mommy na juya na kalli Ibrahim shima sai naga bakin ya saki yana kallon ta" principal ce tayi dariya tace "au mamaki kukeyi yadda nasan kuna yin extra lessons? This is my school, I know everything going on in it. Ina da security da suke zagayawa koda yaushe, kuma kullum sai sun kawo min report cewa sun ganku kuna karatu a gaban library, sai na fara tambayar teachers din ku akan performance din moon kuma suka tabbatarmin da cewa she is doing much better than before. Dan haka na rubuta report na aika gidan ku" Mommy ta juya tana kallon Ibrahim tace masa " bawan Allah, thank you so much. I really appreciate what you are doing. Kuma ina so in nemi favor a gurin ka akan ka hada da Hafsat please. I know she can be annoying sometimes but please bear with her. Zanyi making arrangements zamuke baka allowance duk wata" Ibrahim ya kalleni, he looks compused. Ya chire glasses dinsa sannan yace "Thank you so much maam for the offer but it is not what you are thinking. Actually I am not giving maimunatu any extra lessons. In fact she teaches me sometimes, kawai muna karatu ne tare. She is very intelligent and always ahead of her class so we are both benefitting. There is no need for any allowance Maam because I am gaining as well. As for Hafsat, it will be my pleasure " ya karasa yana kallon Hafsat da murmushi ita kuma da dauke kanta sai da mommy ta harare ta sannan tace masa " thank you sir". Ya amsa da you are welcome. Mommy ma tayi masa godiya sosai sannan ya fita. Daga nan muma mukayi sallama da pc muka koma gurin su daada Hafsat tana ta zumburar baki reshe ya juye da mujiya. Ita dai bata da wani evidence da zata nuna wa mommy cewa soyayya muke da Ibrahim tunda report ya nuna cewa karatu muke yi. Nan mommy ta saka Hafsat a gaba da fada cewa lallai itama ta ringa fita muna karatun tare da ita, tace min duk sanda bata fita ba in gayawa principal nace mata to, nace mata to sannan na faki idon Hafsat nayi mata gwalo. Bayan su mommy sun tafi muka aika da kayan da suka kawo mana muka koma class.
Luckly muna da period din Ibrahim. Ya shigo muka fara maths to question din da muke yi jiya munyi ta da daddare ni da shi. Muna cikin yi sai muka kakare sai yace min " maimunatu check your jotter and see how we got the answer yesterday " yana fadan haka Hafsat tana daga baya sai ji muka yi taja wani dogon tsaki. Tsit ajin yayi. Ibrahim yayi folding hannunsa a kirjinsa yace " who did that?" Kowa yayi shiru, ni nasan Hafsat ce amma nayi shiru nima. Ya sake cewa "who did that?" Fuskarsa ta nuna tsananin bacin rai wanda ban taba gani a tare da shi ba. Ga mamaki na sai kawai naji Hafsat tace masa"I am" duk ajin aka juya ana kallonta, fuskarta babu alamar tsoro ko fargaba. Kallonsa kawai takeyi ido cikin ido. Yace mata "walk out of my class and never come in in my period " bata ce komai ba babu sorry sir babu komai ta fice" ni kaina abin ya daure min kai, wai Hafsat wacce irin mutum ce ita? Da kansa yazo ya karbi jotter din hannuna muka cigaba da calculation din mu amma ni duk hankali na yana kan Hafsat. Muna nan kawai sai ga senior master nan sun taho tare da Hafsat, ya shigo ya kira Ibrahim suka fita waje. Ni dai gaba na sai faduwa yake yi kamar in bisu inji me suke cewa. Can sai ga su sun shigo har da Hafsat. Ga mamakina sai naji senior master yace mata tayi kneel down a gaban class. Hafsat tayi nan ya fara yi mata fada ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba, wai dama staff da yawa suna kawo masa complain akan rashin kunyar Hafsat yana basu hakuri amma yau da kanta taje tayi reporting an kore ta a aji bayan ita tayi masa rashin kunya. Nan yace lallai sai ta bawa Ibrahim hakuri. A ciki ciki ta bashi hakurin yace ta dada da karfi taki. Ya dauko yawarsa ya kira discipline master. Ina jin haka na fara kuka amma Hafsat ko a jikinta. Ibrahim yace its OK shi ba sai ta bashi hakuri ba, amma senior master yace ai badan shiba ne, hakkin makaranta ne ta koya mata tarbiyya. Ni dai na kifa kaina a kan seat dina ina ta kuka na. Ina jinsu suka fara dukanta. Tun tana daurewa har saida ta fara kuka, na manta rabon da inga Hafsat tayi kuka, sannan suka kyaleta, kuma suka cewa da Ibrahim inyaga dama ya barta ta zauna in baiga dama ba kuma ya koreta. Ina jinsa ya tsaya a gabana yana kiran sunana nayi banza na rabu dashi sai ya ajiye min jotter ta ya juya ya fita daga class din, na tashi na tafi gurin Hafsat ina taba ta ta ture ni, nan naga hannunta duk ya farfashe yana jini
Episode fifteen: blood is Thicker than Water.