Sashe 133
Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bara mu dan yi magana akan rashin iya girkin Moon. Na saka cewa Moon ba ta iya girki ba ne saboda ina son in nuna wa mazan da suke karanta littafin nan dama matan cewa 'nobody is perfect' babu, kar ka saka ran zaka auri mace kyakykyawa mai ilimi mai addini mai tsafta mai son mutane mai ladabi da biyayya mai iya kula da miji, mai iya kula da miji a other room kuma mai iya girki, NO, ba zai yiwu ba, kamar yadda shima namijin ba za'a samu wanda yake 100% complete ba. Tabbas akwai matan da basa son girki, kamar yadda akwai matan da basa son shara da wanke wanke, kamar yadda akwai mazan da basa son kallon ball. Girki is a hobby, sometimes yana zama necessity, to idan ya zama both shine ake samun matar da ta iya girki sosai. Idan kuma aka samu matar da bata da interest akan girki amma kuma ya zame mata dole to sai azo a samu matsala, saboda hakkin kula da abincin miji da 'ya'ya yana hannun mu mu mata. Idan kinsan bakya son girki to kiyi kokari ki fara son shi, saboda ba zaki koya ba har sai kina son ki koya din, make it a hobby, make it a challenge, ki fara da kadan kadan a hankali zaki ga kin fara son sa. Nan gaba zaku kara fahimtar abinda nake nufi. Har mota muka raka Amira da Amir, suna tafiya nayi gaba na bar Sultan dan har yanzu ba hucewa nayi ba. Daki na na tafi nayi kwanciya ta, ko minti biyu banyi ba kuwa ya shigo, na juya bayana na rufe ido. Ya zagayo ta gabana ya zauna akan gadon "wai kar dai ki ce min maganar abincin nan ce baki manta ba?", na turo baki, ya mintsini bakin nayi kara na sake juya masa baya. Ya hau kan gadon sosai yace " to wai bana baki hakuri bane ba. I never meant anything by it. I don't want a good cook, I want you. Idan abinci ne I can get it anywhere amma ke guda daya ne, there is no one like you" ya juyo dani yace "please kiyi murmushi mana in gani" ina so inyi murmushin amma na kara bata rai nace "just promise me ba zaka kara cin abincin ta ba" yace "abincin wa?" Nace "ita dai" yace "ni bansan wa kike magana akai ba, I don't know anyone bayan ke" ya dora goshinsa akan nawa "now smile" nayi murmushi tare da zagayo hannayena a wuyansa, yace "that's what am talking about" na saka fuskata a wuyansa irin yadda yake min nace "I will learn how to cook, for you" yace "NO, I don't want you stressing yourself out akan abinci, I will get a cook for us, ko ba a kasar nan bane ba" nace "na riga na kira Mommy ai, tace zata bani aron ma'u for sometime" ya jawo fuskata ya rike a hannunsa yace "dakin bar musu asma'un su mu ba sai mu samu tamu ba?". A haka dai muka kare har magrib sannan ya tashi ya tafi masjid. Washegari tunda safe ya ce min zamu je mu gaishe da Yaya da Nani. Nace masa Hajiya fa? Yace sai Takawa ya dawo, baya kasar, in ya dawo sai muje mu gaishe su gaba daya. Muna gama breakfast na shirya cikin doguwar rigar lace, budaddiya, na gyara fuskata amma babu kwalliya sosai, na dauko jeweleries na zuba, na daura dankwali sannan na yafa babban mayafi, na kalli kai na a madubi, ni kaina sai da nayi mamakin chanzawar da nayi in few days, lallai aure daban ne, that little girl is gone, am a woman now, matar aure. Sultan ya shigo ya same ni a tsaye gaban madubi, yazo ya tsaya a bayana muna kallon kan mu ta cikin mirror din. Ya sunkuyo a hankali yayi kissing kuncina yace "you look beautiful, Darling" na daga hannuna na shafa fuskarsa ina kallonsa ta cikin madubin nace "you look handsome too, Darling" a tare muka yi dariya, ya dauko wayarsa yayi mana selfie ta cikin mirror sannan muka tafi. A bayan palace din sabon gurin yake, an kawata gurin sosai dan zaka dauka wani palace din ne daban, ko da yake gidan mahaifiyar sarki ai dole a kawata mata shi. Tun daga bakin gate ake ta gaishe mu, ni har kunya nake ji in naga manyan mutane suna durkusawa har kasa suna gaishe mu, na kalli fuskar sultan naga ya wani hade rai kamar bai taba dariya ba, ni kuwa sai washe baki nake ina amsawa. Direct part din Yaya muka shiga, da kanta ta fito har kofar palo ta tare mu, ta kama hannuna ta jani jikinta ta rungume, sai naji kunyar ta sosai, naja mayafina na rufe fuskata, tana ta dariya tace "ni fa kakar kice ba surukarki ba, ki bude fuskarki ki kalle ni sosai, in kika tsaya wasa sai in kwace mijin, dama ara miki nayi" ina jin Sultan yana cewa "nan gani nan bari Yaya, ai wutsiyar rakumi tayi bala'in nesa da kasa" suna ta wasan su na kaka da jika muka shiga ciki, har cikin bedroom dinta ta zarce damu. Sultan ya samu kan gado ya haye harda harde kafa. Ni kuwa na zauna a kasa kan carpet, Yaya ta zauna kusa dani, na rissina ba gaishe ta ta amsa da fara'arta, tace "ya bakunta? Ina fatan dai bakiyi kewar gida da yawa ba?" Nayi murmushi kawai bance komai ba. Tana ta tsokana ta wai kauyanci nake yi irin na fulani, Sultan dan rashin kunya shine yake ramamin, ta saka aka cika mana gaban mu da kayan ciye ciye. Ni dai na kasa cin komai, sultan kam aka sauko aka fara aikin da aka saba, ci. Da kyar na danci fruits kadan naci dambun nama. Yaya tace "kaga karamin sarki, ka tashi ka tafi ka bar mana ita. Da daddare sai ka dawo ka dauke ta" da sauri sultan yace "what? Amma dai wasa kike yi ko? Ai ba haka muka yi ba, cewa kika yi in kawo ta ku gaisa ba wai in kawo ta ta wuni ba" ta rike baki tace "au yanzu kana nufin ba zaka bar mana ita ta wuni din ba?" Ya girgiza kai yace "gaskiya ba yau ba, sai dai wata rana kuma" na dauko wayata nayi masa text, 'Sultan ka barni in wunin mana, kaga haka ba dadi fa' yana ta zance bai gani ba nayi masa flashing yana dauko wayar na katse, ya duba yayo min reply 'yanzu kina nufin ni kadai zan koma gida?' Na amsa 'it will be for just few hours ne fa, in kuma ba ka son zama kai kadai sai ka zauna anan din kaima, ko kuma ka tafi wani gurin" ya dan kalle ni nayi masa alamar please, ya dauke kai. Yace "OK, Yaya, kinci nasara, zan bar miki ita, saura kuma in na dawo daukanta ace kwana kuma ake so tayi" ya mike yana kallona nace "adawo lafiya" yayi kwafa bai ce komai ba ya tafi, Yaya tace "Allah ya raka taki gona, daga zuwanka har ka saka ni ciwon baki saboda magana". Sai daya dan jima da tafiya sannan Yaya tace "kin ki cin komai maimunatu, kina ganin dai shi yadda yake ta zuba min rashin kunya amma ke abinci na ma kin kasa ci" nace mata "na koshi ne ai" tace "wai menene sirrin ne?" Na kalketa da alamar rashin fahimta tace "ya akayi kika kwace min miji ne wai?" Na sake jin kunya na sunkuyar da kai, tace "gaskiya ni kam babu abinda zan ce miki sai godiya, ko a mafarki ban taba tunanin zan ga karamin sarki yadda na ganshi yau ba. Ban taba ganinsa cikin fara'a, kwanciyar hankali da nutsuwa irin yau ba. Allah ya saka miki da mafificin alkhairi duniya da lahira, yadda kika kawo farin ciki rayuwarsa Allah ya tabbatar miki da farin ciki a cikin taki rayuwar" nace "Ameen" ta cigaba da magana "kullum babu dare babu rana addu'ah ta akan yaron nan take, bam taba gajiyawa ba kuma ban taba fitar da rai ba, gashi Allah ya amshi adduah ta ta hanyar ki maimunatu. Ni kam babu abinda zan saka miki dashi illa in yi miki alkawarin zan yi iya bakin kokarina inga cewa dake dashi kun cigaba da zama cikin farin ciki har abada. Dan haka duk wani abu da kike so, na kudi ko akasin haka, ki gaya min. Duk wani abu da kika ga anyi muku ba dai dai ba shima ki gaya min, kar kice zaki boye har ku zo ku cutu dake dashi. Karamin sarki yasa wahala a rayuwarsa, yanzu farin ciki yazo masa, akwai mutanen da ba zasu so suga wannan farincikin ya dore ba, dan Allah maimunatu kar ki basu dama. Karki yadda wani ya gaya miki wani abu akan mijinki ki yarda, duk abinda aka gayamiki kiyi bincike sosai akansa. Nasan tun kafin ki auri karamin sarki kin san yana shan giya, amma baya neman mata, ban taba samun wannan complain din akansa ba. Duk wadannan mugayen abokan nasa na tabbatar zaki iya raba shi dasu, dan in baki raba shi dasu ba zaki ke yin tubka ne suna warware miki" da tanyi shiru sannan ta cigaba "Maimunatu ke kadai ce hope din mu akan karamin sarki. Ke ce amsar adduar mu" jin ta sake yin shiru ya sa na dago kaina nace "Insha Allahu Yaya komai ya kusa zuwa karshe, insha Allah yanda ki kai kuka akansa kin kusa kiyi dariya" dariya ta fara yi tun yanzu tace "dariya kam ai na fara yin ta maimunatu, ganinsa da nayi yau kadai ya wanke min zuciya ta" wata 'yar karamar budurwa ce ta leko da sallama tana kallon mu daya bayan daya. Yaya ta ce "sai ki shigo ai, dodon naki ya tafi" ta karaso amma kamar bata yarda ba, sai da ta tabbatar innan ta zauna tana dariya ta gaishe ni, na amsa da fara'a tace "ashe ya tafi, ina ta lekowa tun dazu ina son inzo in gaishe ki bana son mu hadu dashi, ni tsoro yake bani wallahi" Yaya tace "Allah ya shirye ki, dan uwan naki kike tsoro" tace "Yaya baki ga yadda