Sashe 159
Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
ya kashe min ido, na makale kafada ina dariya. Nace "ni kuma ga tawa shawarar; idan kun gama settling wannan maganar, ina ganin ka mayar da Abbas makaranta, yadda zai samu future mai kyau nan gaba, ya koma makaranta ko first degree ya samu ya kammala, in ma ba zai yi aiki ba ya ajiye takardun. Kuma komawarsa makaranta zata saka ya dauke hankalinsa daga kan sarauta yasan cewa yana da opportunities a rayuwa beyond his imagination" sultan ya daga kafada yace "OK, I can see what I can do. Amma in yace baya so kinsan bazan dauke shi aka in kaishi ba" Washegari suka zauna akan maganar. Abbas did not take maganar lightly kuma ni na fahimce shi, maganar da ciwo. Da kyar Sultan ya shawo kansa dan cewa yayi sai yaga bayan Hajiya, Hajiya kam tayi kuka da idonta, ranar Abbas a gidan mu ya kwana part din baki maza. Bayan sultan ya dawo daga gurinsa ya same ni zaune da hijab ga key din mota a hannuna, ya tsaya rike da labule yana kallona, na langwabar da kai gefe, yace "yau kuma me babyn take so?" Nace "Namiji ne fa ba mace ba. Vanilla flavoured ice cream yake so. Sannan da sponge cake ya sha cream da yawa. Sai kuma tsire mai kuli kuli" dariya yayi sosai ya karaso ya karbi key din ya miko min hannunsa yace "you got it". Muna tafiya a mota muna shan ice cream din mu wayar sultan tayi kara, ya dauka, daga gaisuwar da yake nasan Takawa ne, yaje ya tarar bama nan, budar bakin sultan sai cewa yayi "mun tafi shan ice cream, baby ne yake rigima yace shi ice cream zai sha" na bude baki ina kallonsa, duk inda kake tunanin rashin kunyar sultan ta wuce nan, yace "what? He deserves to know da wuri saboda ya fara siyan pampers". A cikin satin Takawa yaje maiduguri nemarwa Amir auren Aishan sa, ai kuwa iyayenta jiki na karkarwa suka ce sun bayar. Tare da sultan suka tafi. A bauchi suka sauka sannan suka hau motoci zuwa maidugurin, suka kuma dawowa bauchi igan sarki suka yi taro sannan suka dawo Abuja. Tun a hanya sultan yayi min waya wai ya gaji, shi ya dade rabon dayayi irin wannn gajiyar. Yana dawowa kuwa da kyar na samu yaci abinci duk kuwa da soyayyar sultan da abinci. Dakinsa ya wuce yana tafiya yana hada hanya saboda bacci. Ina kallonsa ina dariya a raina. Allah ya nuna min ranar da zan rama abinda sultan yake yi min a gidan nan, yau zai gane shayi ma ruwa ne, zai ji yadda nake ji idan ya hanani bacci. Dakina na tafi nima naje na tsalala wanka, na shafe jikina da turaruka da mayuka irin duk wanda sultan yake so, na dauko wata rigar bacci na da tun da nazo gidan ban taba saka taba saboda kallonta ma kadai in nayi kunya nake ji, na saka, na dauko jan jambaki da nasan yana ruda sultan na shafa a lips dina, na zura hijab a raina ina cewa sultan yau ka kade har ganyenka. Ina shiga dakin na ganshi ya bararraje akan gado daga shi sai three quarter wando, ya kure ACn dakin kamar ka shiga freezer, na taba jikin sa naji sanyi kalau, naje na rage ACn na dawo ina kallonsa, a hankali na hau kan gadon na fara shafa fuskarsa, "sultan? Sultan?" Amma sultan shiru kamar gawa, nayi masa chakulkuli a kafa irin yadda yake min amma bai san ina yi ba, a raina nace aikuwa sai ka tashi yau. Na shiga toilet na dauko cotton bud, nazo na fara sosa masa kunne a hankali, yayi juyi ya janyo pillow ya dora akan sa. Haushi kamar ya kashe ni amma naki hakura, na fara shafashi duk inda nasan yana so amma maimakon ya farka sai jikin sane yake farkawar. Naji tsoro na daina. Na koma kiran sunan sa da dan karfi, sai a lokacin yayi juyi ya dauke pillow daga kansa, na kara volume din kirana, ya dan bude idonsa da suka yi ja sosai saboda bacci ya kalleni kamar zaiyi kuka, nace "pay back time" ya kwabe fuska ya gane me nake nufi yace "dan Allah Moon ba yau ba. Ki bari wata rana kya ramar, you have no idea irin baccin da nakeji yau" nace "nima lokacin da kake tashina you had no idea irin baccin da nake ji" bai ce min komai ba ya juya baya ya ja bargo, na tsallaka ta samansa na yaye bargon ina dariya, hankali na ya kwanta, ko a haka na barshi nima na rama. Ya dago yana kallona ina dariya, a hankali naga baccin idonsa yana washewa lust yana replacing baccin, idonsa akan rigar dake jikina, nayi sauri na daina dariyar nace "shikenan ma babu wani abu na hakura kwanta kayi baccinka" ya dago yana kallon fuskata yanayinsa yana chanzawa, yana min rikitaccen kallo yace "no thank you, na fasa baccin kuma, I got something sweeter than bacci" da sauri na ja da baya, yau na kunto wa kaina ruwa kuma bani da lema, ai kam kafin in sauka ya kamo ni yana kare min kallo, na fara bashi hakuri "kaga ka gaji da yawa, dan Allah ka kwanta kayi baccinka kawai, kaga gobe zakaje office kar kazo ka makara" yayi dariya yace "a da kenan, yanxu na chanza shawara" ya kawo bakinsa dai dai kunnena yace "tunda har kika tambayeni bashin da kike bina, dole ki karba". Nasha kama Sultan yana kallon picture din Ummee a waya ta, sai nazo kuma sai ya basar yayi kamar wani abin yake yi daban, shi a dole wai bai damu da ita ba. Ni kuma da naga haka sai ba saka hoton nata a screen saver dina, yana dauka ya gani ya juyo yana kallona da alamar tambaya, na daga masa kafada nace "for easy viewing" ya ajiye wayar yayi tafiyar sa irin baya son maganar nan. A bangaren Hafsat kuwa har suka gama zaman su a Riyadh Ummee bata fada mata wata maganar da zata dangantata da Nigeria ba ko kuma da Sultan. Rannan kawai sai ga Hafsat ta kirani tace zasu koma Riyadh Abban Zayed baya jin dadi zasu je su duba shi. Kuma tayi min alkawarin insha Allah wannan karon zata samo labari ko da kuwa a gurin Ummeen zayed ne. Kwana uku bayan nan muna zaune da Asmau tana yi min kitso sai ga wayar Hafsat na dauka ina addu'ar Allah yasa labari mai dadi ne, tace "Moon she talked to me" nace "how managed? Ya kika yi mata?" Tace "zama nayi ina ta bata labarin Nigeria da Abuja, na kuma bata labarin Mommyn mu da yadda take son mu bata son rabuwa damu ko kadan. Irin heart to heart talk din nan. Daganan kawai sai tace min ai itama tana da da, kuma tana sonsa fiye da komai a duniya, tana nan kuma tana jiran ranar da zai zo gurinta. All these years zaman jiran yazo gurinta take yi, all these dukiyar da take tarawa, shi take ajiyewa dan tasan komai daran dadewa zai zo gurinta" nayi shiru inajin hawaye yana taruwa a idona, tace "yanzu kina ganin in gaya mata nasan shi ko kuma me kike so in ce mata" na danyi tunani kadan sannan na tsarawa Hafsat duk abinda nake so ta gayawa Ummee. A ranar da daddare muna zaune a palon Sultan, ina kwance akan kujera ina game a wayarsa shi kuma kan study table dinsa yana zane, sai ga kiran Hafsat a waya ta, sai da na jera adduoi sannan na dauka, na daga murya yadda zan calling attention din sultan nayi mata sallama, tace min da fulatanci "na gaya mata duk yadda kika ce" ina jin haka na saka waya ta a hands free, Hafsat ta koma turanci "Maimunatu this is zayed aunt, she wants to talk to you about her son" ina kallon sultan ya ajiye pencil din hannunsa, nima sai da na hadiye yawu saboda bakina naji ya bushe, ina jin Hafsat tana bata wayar tana mata bayanin ga sister din tata, naji muryarta ta larabawa tace "As Salaam-o-Alaikum" na amsa mata murya ta na rawa, idona akan na sultan wanda ya juyo yana kallona, ta fara magana da turancin ta mai accent din larabawa "Am sorry to disturb you. What is your name?" Nace "Maimunatu" tace "Nice name you get, I always wanted to name my daughter that, but I didn't get a daughter I got a son. I talked to your sister about him she said she didn't know him, but she said you might. His name is Sultan, he is a Prince in Abuja. Very handsome and very strong. I only want to know how he is doing" sai da na tattaro dukkan jarumtata sannan na iya magana, still idanuna a cikin na sultan wadanda suka chanja kala, nace "I don't only know him, he is my husband, Ummee"