← Book details Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 168 OF 190

Sashe 168

Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Episode Ninety One : His Mother's Son 2 Tace "to ni yanzu moon ta ina zan same shi?" Nace "How will I know ni da bana kasar ma" tace "Moon tsoronsa nakeji, tunda ya gane gaskiya bamu hadu ba, bansan wacce irin karba zai yi min ba" na danyi tunani a raina, tabbas Ibrahim yana jin haushin Amira sosai, dan haka ba lallai ne yasaurare ta ba in taje wajansa, Allah ma yasa karya faffalla mata mari. Sai kuma wata shawara ta fado min arai na, nace "abinda za'ayi Amira, kije gidan mu gurin Amina, ni zan kira ta in yi mata bayanin abinda nake so tayi, zata hada ki da Ibrahim kuyi magana, duk abinda ake ciki kuma sai muyi waya" ina gama yawa da amira na sake kiran Amina, ta dauka tace "what again?" Nace "ke dalla can ba maganar shi zanyi miki ba" sai nayi mata bayanin duk yadda mukayi da Amira, nace "yanzu taimako nake nema a gurinki, so nake ki hada su ta roke shi gafara, kema dan Allah sai ki tayata rokonshi" tace "kuma kika ce min ba maganarsa zakiyi min ba" nayi dariya nace "amma ai ba maganarsa dake nayi miki ba, maganar abinda ya faru tsakaninsa da amira nayi miki" ta danyi tsaki tace "ba lallai ne fa ya yafe matan ba, tunda har yanzu bai manta ki ba ba lallai ya yafewa wadda ta raba ku ba" nace "in kika hada su ne zaki tabbatar cewa ya manta dani yanzu, nayi miki alkawarin zaki sha mamaki, bazan miki alkawarin zai manta dani completely ba tunda nima ban manta dashi completely ba amma babu zancan soyayya, an wuce gurin, sai mutunta juna. Duk kanin mu, ni da ke, Ibrahim da Amira, duk mutane ne mu, muna making wrong decisions a rayuwar mu, muna sabawa Allah ma kansa ballantana mutum, amma in muka nemi gafarar Allah sai ya yafe mana, ya sake bamu chance saboda yana son mu chanza mu zama mutanen kirki, ti me yasa mu mutane ba zamu ke yafe wa junan mu ba? Me yasa zamu ke riko a ranmu bayan munsan cewa muma muna so in mun yiwa wani laifi ya yafe mana. Please Amina kiyi kokari kiga Ibrahim ya yafe wa Amira kema sai ki yafe masa ki sake bashi chance" ina kallon sultan ya shigo dakin da takardu a hannunsa ya tsaya yana kallona, Amina tace "shikenan, zanyi magana da Amirar in gani, I will see what I can do" muka ajiyar wayar. Sultan har yanzu yana tsaye yana kallona, am sure yaji ambaton sunan Ibrahim da nayi a waya, na tsaya ina jiran inga reaction dinsa, ya karaso inda nake yace "miss problem solver, kina nan amma kina solving problems din wadanda suke thousands miles away" naji dadi da ya fahimce ni, ya zauna a gefe na ya miko min takardun hannunsa yace "Ummee tayi miki maganar nan?" Na karbi takardun ina dubawa, da sauri na mike zaune sosai ina kara dubawa, na girgiza masa kai nace "bata yi min maganar ba, ta dai ce saboda kai ta fara kasuwancin ta, amma bata gaya min cewa sunan ka ne akan komai ba" dukkan takardun abinda Ummee ta mallaka ne, hatta takardun wannan gidan, da bank account dinta, da takardun dukkan contracts din data karba na shigo da kaya, duk sunan sultan ne a jiki. Na ajiye takardun ina kallonsa, yace "how do I tell her ni bana son kudinta?" Na girgiza kaina nace "mahaifiyar kace sultan, duk abinda ta baka ba faduwa tayi ba kuma kaima in ka karba ba faduwa kayi ba, karbar da zaka yi a ganina shine nuna godiyar ka gareta, inka mayar mata ka nuna mata baka so ba zata ji dadi ba, ka karba amma sai kace mata ka barta a matsayin care taker ta dukiyar taka, ta cigaba da kula da ita kamar yadda takeyi da" yace "to wannan uban cash din kuma da yake banki ya zanyi dashi?" Nace "kudi ne fa, you can do anything with it" ya jawo ni kan cinyarsa yace "ke a shawarar ki me kike ganin ya dace inyi dasu?" Na gyara kwanciyata a kan cinyarsa na danyi tunani kadan sannan nace "why not ka sake gina wata orphanage din, kuma ka bunkasa wacce kake da ita already, kace kana son gina musu makaranta da daukan malamai. Kaga idan kayi haka daga kai har ummee zaku samu lada har karshen rayuwar ku", yana murmushi yace "har ke da kika kawo shawarar" na mayar masa da murmushin nace "yes, har ni dana kawo shawarar". Washegari Ummee ta kaini gidan su zayed na wuni a can Umm zayed me kirki sosai gata wayayyiya, da sister dinsa zahra, na sake sosai dasu muna ta hira da zahra ina vata labarin England, wai tana son zuwa tayi karatu amma an hana ta a gida, muma cikin hira tace "amma kinfi sister dinki kirki, ita bata yiwa mutane magana" nayi dariya nace "ba haka bane ba, Hafsat tana da kirki sosai, kawai dai banbancin halayya ne a tsakanin mu, ni ina da surutu da saurin sabo da mutane ita kuma bata kula mutane sosai, amma in kika saba da ita zaki fahimci tana da kirki sosai. Abinda zakiyi ki lallaba a barki ki je England gurinsu ki dan kwana biyu, zakiyi mamakin kirkin Hafsat" sai magrib sultan yazo ya dauke ni muka koma gida. A hanya yake ce min "yaushe zamu koma Nigeria ne, Takawa yana ta waya wai ya kamata in taho haka nan" nima nayi missing gida sosai, amma nace masa "akwai rigima da ummee kenan" yace "sosai kuwa, dan yadda take ta plans dinta tunani take yi munzo garin nan kenan, ta manta ina aiki a can, besides Takawa ba zai taba barina in dawo nan da zama ba" a raina nace wasa kenan, dan nashi namiji guda daya kamar rai, his only heir, sultan yace "abinda za'ayi yanzu in munje gida, naga kunfi shiri da ita, ki tayar mata da maganar komawar mu Nigeria mu gani abinda zata ce, sai muyi mata bayanin ai ana ta nemana a office din mu sannan kema asibitin da kikayi booking zaki yi antenatal suna nemanki, mu ce mata amma zamu ke zuwa from time to time" na yarda da shawarar sultan dan haka muna dinner na fara maganar, dama sai da na gama jero adduoi sannan na fara magana, tunda na fara ta ajiye spoon din hannunta tana kallona, na duburburce na kasa karasawa, na kalli sultan amma sam yaki dago kansa ya kalleni, tace "yaushe kuka hada wannan plan din? A hanya ko kuma dazu a daki? You are not going anywhere. Me zakayi da aikin a can din? In aikin yi kake so sai ka nema anan ai. Ke kuma wanne antenatal zaki yi wanda ba zaki iya yi anan ba? You are a doctor, kinsan duk abinda kike ji kinsan kuma drugs din da zaki sha, ki rubuta masa sai ya siyo miki, sai menene kuma ake yi a antenatal din? Akwai kanin zayed shima doctor ne anan, ki shirya gobe sai muje ayi miki scanning" na kalli sultan na ga har yanzu baya kallona, nace a raina, wato zura ni kayi dama ka barni ni kadai ko? Ai kuwa muna komawa part din mu na fara sauke masa kwandon bala'i, "shine dazu kaki yin magana ko" yace "dama nasan ba zata yarda ba, I just want to confirm" nace "shine kayi using dina kayi confirmation din ko? I tot we are suppose to be a team" yace "we are a team. Yanzu ni bansan me zance wa Takawa ba idan ya sake kira, dazu daya kira cewa yayi da yasan zamu dade da kema ba zai barki ki taho ba ballantana har in biyo ki. Yanzu me zance masa?" Nace "oho, ni dai ba zaka sake yin using dina ba ehe, kawai dan ace ni ce marar kunya" ya jani muka zauna yana langwabar da kai, "hava love, ba using dinki nayi ba, kin san ina jin kunyar ummee ba zan iya yi mata musu ba shi yasa nayi shiru. Ina son komawa Nigeria amma kuma bana son inyi hurting ummee" na danyi tunani sai kuma nayi murmushi nace "then tell Takawa the truth, ka gaya masa ummee tace ba zamu dawo ba anan zamu cigaba da rayuwa har illa masha Allah" ya dan yi shiru sai kuma ya fara dariya, yace "that means war" nace "then let them have the war, mu sai mu zama 'yan kallo" ya manna min kiss yace "that's why I love you more every day". Washe gari muka je scanning. Dani da Sultan da Ummee. Private clinic ne na Ahmad kanin zayed, kusan sa'an sultan ne dan haka muna zuwa suka kama hira, yana da fara'ar sosai da wasa kamar zayed. Tare muka shiga dakin scanning din gaba daya, ya fara min tambayoyi ina amsawa yana tsokana ta, ummee tayi masa bayanin cewa nima doctor ce, yace "shi kenan ma kinga abin yazo da sauki, duk bayanan da zan miki kin sani, sai dai kawai mu duba muga lafiyar babyn shikenan" nace "doctor we don't want to know the sex of the baby" da sauri sultan yace "when did we decide on that?" na harare shi, ummee tayi dariya, nace "kullum yana cewa mace ce ni kuma ina cewa namiji ne, so I tot mu barshi kawai in an haihu magani" sultan yace "no, ban yarda ba, dan kinsan ke zaki yi loosing shi yasa kika ce haka" Ahmad yace "ai ya danganta da kwanciyar babyn, idan babyn ya kwanta yadda zamuga sex din shi kenan in kuma ba haka ba sai mu bari daga baya mu sake dubawa" ni dai na bata rai, dan nasan in aka ga macece sultan in ya saka ni a gaba da tsokana har sai nayi kuka. Ummee taga na bata rai tace "abinda za'a yi, in kaga sex din kar ka fada musu, ni zaka fada wa, ni zanyi deciding me za'ayi dashi" sultan ya fara kunkunin ummee tafi sona a kansa. Doctor Ahmad har da juya screen din dan kar in gani, sam bai daga min riga ta ba, ta cikin rigar ya saka handle din ya kama jujjuya shi
Chapter 168 · 0% Book details