Sashe 162
Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
min shine palon ta, zayed ya bude kofar da sallama sai kuma yaja baya ya bani guri yayi min alama da in shiga, na hadiye yawu da kyar sannan na daga labule na shiga da sallama. Tana zaune akan kujerar da take facing din kofa, bakar abaya ce a jikinta da rolling irin na larabawa, gashin kanta ya fito ta kasan mayafinta ya sauka har gadon bayanta, ta saka hannayenta a tsakanin cinyoyinta, ta bude idanuwanta tana kallona, she looks more like sultan in reality than in the picture. Kallo daya nayi mata naga extreme of innocence a fuskarta. Ta mike tsaye tana jujjuya hannunta, idonta ya sauka akan dan karamin cikina, naga kwalla ta fara taruwa a idonta, ta kasa cewa komai, na karasa shiga palon a hankali, kafin inyi magana wayata tayi kara, ina dubawa naga sultan, na dauka da sallama, bai amsa ba yace "kin fasa yin kwana ukun, na duba naga gobe da akwai jirgin safe daga nan Riyadh zai dawo Nigeria, ki biyo shi ki dawo" nace masa "an gama" na katse kiran, na kashe wayar gaba daya na saka ta a jaka ta. A hankali tace "Sultan ne" Nace "eh shine" Tace "he is already regretting letting you come ko?" Nace "yes" take naga fuskarta ta chanja kalar tashin hankali, tace "fushi yake yi dani and I don't blame him, sai dai bansan me zanyi masa ya hakura ba. Cewa yayi ki koma Nigeria ko?" Nace "yes. But if he wants me, he will have to come and get me?" A hankali naga damuwar fuskarta tana washewa, farin ciki yana replacing, ta karaso gurina da sauri ta rungume ni tace "thank you my daughter". Afuwan jiya kun jini shiru, abubuwa ne suka dan sha kaina amma lafiya lau nake Alhamdulillah, nagode da kulawarku sosai. I feel loved.