← Book details Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 190

Sashe 114

Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

kamar masu yi min farewell, anan mukayi dinner tare suna ta tsokana ta, sai da suka ga na fara musu kuka sannan suka rabu dani. Daddy da Mommy suka tashi suka tafi suka bar mu. Muna ta hira har sallar isha, su yaya walid suka fita mosque suka dawo, can nace musu "wai ku ba za kuje bachelor's night din bane" yaya Habeeb yace "Allah ya kiyaye. Wannan night din ai yafi karfin mu" ban gane me yake nufi ba nace "saboda me?" Ya walid yace "kin san menene bachelor's night ma kuwa?" Nace "I thought kawai it is just a funny guys' thing. Just to have fun" yace "exactly" nace "to menene laifi? Don't you want to have fun?" Yace "ya danganta da irin fun din da za ai having" nayi shiru ina kallonsa yace "look parrot, wadanda suka shirya wa Sultan bachelor's night dinsa are not my kind of people, dan haka yana yi min magana nace ba zamu je ba" Ban sake cewa komai ba nayi shiru ina tunani, su waye suka shirya masa? Take na samu amsata, the gang bang. Lokaci daya naji hankali na ya tashi. Tun da na dawo daga Niger ban kuma ganin sultan a buge ba, kuma bana jin ko a bayan idona yana sha duk da bamu taba maganar ba. Har karfe goma ina zaune a palon amma sam hankali na baya tare dani. Only God knows a ina sultan yake kuma me yake yi. Na tashi nayi musu sallama na tafi daki, na kira wayar sultan tana ta ringing babu answer. Ko da ace Sultan ya daina shan giya amma temptation fa? Musamman idan ya ga ana sha, ballantana nasan zasu iya bashi su ce sai yasha. A automatic redial na saka wayar na kuma saka ta a speaker na kwanta, kiran yana ta shiga har wajan 30minutes bai dauka ba, ina cikin haka Amina ta shigo, ta kalleni tace "ba dai Sultan kike kira ba? Ke ma kinsan kina bata lokacin ki da battery din wayarki ne a banza amma ba dauka zai yi ba" ina kallonta ta gama shirin kwanciya ta hawo kan gado ta kwanta, nace "Amina, what do you think maza sunayi a bachelor's night?" Tace "hmm, a England an taba bikin wani dan ajin mu, mazan suka shirya masa bachelor's night, washegari very few ne suka zo makaranta, saboda sauran all got drunk the other night ba zasu iya zuwa ba. Na tambayi wani a cikin su,why?, sai yace ai suna celebrating last day of freedom din su ne, in suka yi aure kamar they are bond to their wives babu sauran sakewa suyi abinda suke so. So duk abinda namiji yafi enjoying shi zai yi a daren, in mashayi ne in manemin mata ne sai yayi kayan sa one last time" tayi sauri tace "amma fa ba ina cewa abinda sultan yake yi kenan yanzu ba, it depends on mutun. Ke kinsan Sultan kinsan me zaiyi kinsan kuma menene ba zai yi ba" bance mata komai ba amma zuciyata in ban da zafi babu abinda take yi, har yanzu kira nake kuma har yanzu bai dauka ba. Ba'a jima ba Amina tayi baccinta ta barni, har na fitar da ran zai dauka kawai naji ya dauka, gurin da yake hayaniya ne kawai da kida yake tashi a gurin, yace "Hello, love, bakiyi bacci ba" nace "sultan where are you?" Yace "muna gidan Solomon, wani abu ne?" A hankali nace "Sultan I want you to come back home" yace "why? The party hasn't even started yet" ina jin wani a gurin yana cewa "chafdi, Sultan wannan amaryar taka in aka gama bikin nan ko kofar gida ba zata ke barin ka kana fitowa ba" duk suka kwashe da dariya, Sultan ya dan matsa daga gurin su yace "why?" Nace "ni kawai bana sonka da mutanen nan wallahi" yace "Moon, this is my party, saboda ni suka shirya shi. I can't just leave" naji wani abu ya tsaya min a makogwaro na. Kafin in san me zance masa wani a cikin su ya karbe wayar yace "look amarya, we are going to get your ango drunk today, he is even lucky he don't do women, amma shima in kika sake kiransa we will make him do it even if we have to tied him to the bed" Sultan ya warce yawar yana ce masa "fuck you" da sauri yace min "Moon" ban jira abinda zai kuma cewa ba na kashe wayata. Kafin in ajiye ta ya kira, ban dauka ba, ya sake kira na kuma share shi. Zafi nake ji sosai a raina. Sai da yayi five missed calls sannan ua hakura. Na runtse idona ina addu'ar Allah yasa in iya bacci amma sam babu bacci a idona. Ina tsakiyar tunani na naji wayata ta cigaba da kara, nayi niyyar in sake rabuwa dashi amma na daure na dauka, bance komai ba yace "kinyi fushi ko?" Naji inda yake babu hayaniya, amma duk da haka bance masa komai ba, ya sake cewa "gani a balcony dinki, ki bude min kofa" I hope duk wacce take karanta littafin nan zata so saurayinta/mijinta kamar yadda Moon take son Sultan, duk wanda yake karantawa kuma shima zaiso budurwarsa/matarsa kamar yadda Sultan yake son Moon. Remember, Love is the strongest magic of all. Stay loved.
Chapter 114 · 0% Book details