Sashe 145
Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
da Ibrahim bayan bansan yana gurin ba" yace "am so sorry" nace "don't be. Rayuwa ta da taka ba iri daya bace ba. Ka tafi, ni bazan iya zama da mutumin da yake ganin cewa it is OK yayi kisan kai ba, bazan iya haifar 'ya'ya da kai ba, wannan ma da yake cikina in naga baka chanza ba I will make sure cewa bai san kaine babansa ba" da gaske magana ta ta shige shi dan fuskarsa koma wa tayi kamar an chire masa spirit din jikinsa, na mike tsaye nace "now get out of my room" ko motsi bai yi ba, na kunna fitilar dakin, yanayin da naga fuskarsa yasa nayi saurin dauke idona daga kansa tun kafin zuciyata ta karaya, na sake cewa "ka fita ko in kira security su fitar min da kai" a hankali yace "you won't" ban kuma ce masa komai ba naje na danna security button, ba'a jima ba sai ga David da wasu guda biyu sun shigo dakin, David da bindiga a hannunsa. Na nuna Sultan nace "ku fitar mun dashi daga nan" David yace "with pleasure ma'am" dama har yanzu David yana da grudges for sultan saboda dukan daya yi masa rannan ya kunyata shi a gaban yaransa. Ga mamakina ko motsi sultan baiyi ba ballantana yace zai yi fada dasu, suka kama shi suka fita dashi ta gabana, na dauke kaina ban kalle suba, amma suna fita na bi bayansu na tsaya a kofar dakina ina kallon yadda suke jansa akan stairs, ji nake tamkar zuciyata suka fito da ita waje suke ja a kasa, ina kallon su har suka bude kofar palo suka fita dashi waje. Na hango Daddy a kofar dakinsa shima yana kallon su. Na koma dakina da sauri na bude kofar balcony na shiga na cigaba da kallonsu suna jansa a kasa kamar babu rai a jikinsa, har suka bude gate suka fita dashi waje, a gaban gida na biyu bayan namu na hango motar sa, nan suka nufa dashi suka jefar dashi a gaban motar suka juyo, na tsaya ina kallon duhun inda yake a kwance a kasa, a raina ina cewa 'get up sultan' amma shiru bai tashi ba, bayan kamar 20 minutes na koma dakina na dauko waya na dawo balcony din, na kira wayar Amir, yana dauka nace "Kazo gidan mu yanzu, your friend needs you" na kashe wayar, ban bar gurin ba har sai da naga shigowar Amir unguwar mu, har ya wuce inda Sultan yake sai kuma yayi reverse, ya fita da sauri yana taba sultan, sannan ya daga shi, naji wani dadi a rauna ganin sultan din yana kokarin tafiya da kansa, a bayan mota Amir ya saka shi sannan ya koma ya rurrufe motar sultan din sannan suka tafi. Na rufe fuskata da hannayena ina kuka, I really hope cewa abinda nayi is the right thing to do. Waya tace ta fara kara, duk a tunani na Amir ne amma sai naga sunan Hafsat. Nace a raina 'har ta samu labari kenan' na dauka nayi mata sallama cikin sarkakkiyar murya, excitedly ta fara magana "Moon am sorry na kira ki yanzu nasan dare yayi sosai a Nigeria, what ever you are doing ki ajiye ki hau WhatsApp na turo miki hoton wata auntyn zayed, she looks exactly like Sultan, her name is Khairat, Moon I think she is his mother". *when everything seems lost, have hope and trust in Allah, He will always find a way out for you. Remember, there is always darkness before dawn.*