← Book details Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 166 OF 190

Sashe 166

Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Episode Ninety : His Mother's Son Bedroom din Ummee na shiga na turo kofa, na zauna a bakin gado ina ta murmushi ni kadai like an idiot, reaction din sultan ya bani mamaki kuma ya kara tabbatar min da cewa there is no one like mother. Na san dama zai sauko amma banyi tsammanin saukowar shi da sauri haka ba. Wai kunyar ta yake ji, sultan ne wai da kunya, abin ma abin dariya. Na gaji da zama na jawo pillow na kashingida ina jin farin ciki sosai a raina, burina ya kusa cika, nayi wa kaina alkawarin I will totally change sultan's life around kuma so far babu abinda zance sai Alhamdulillah. Wannan duk ba yi na bane yin Allah ne. Ina nan kwance har akayi sallar azahar na tashi na naje nayi sallah, ina idarwa na koma nayi kwanciya ta, na dauki waya na kira Hafsat tace min sun fita da zayed da khairat, ina nan a kwance sai ga Ummee ta shigo, ta tsaya a bakin kofa tana kallona sannan tace "waye zaiyi serving mijinki abinci da kika zo kika kwanta?" Na dan tashi ina dariya, ta daga gira tace "he has been asking for you, yaki cin abincin ma, wai shi kunya ta yake ji" na tashi na gyara veil dina muka fita tare. A dining na same shi ya tisa abinci a gaba ya zuba uban tagumi, na dan yi gyaran murya, ya juyo da sauri, ina kallonsa har da ajjiyar zuciya ya taso ya taho, na fara waige waigen ummee amma naga bata gurin, na karasa nima gurinsa na shige cikin kirjinsa ya rufe ni da hannayensa, a tare muka sauke ajjiyar zuciya, sosai nayi missing mijina, na lumshe idona ina shakar kamshinsa da yake kwantar min da hankali a koda yaushe, nace "I missed you, mijina" ya danyi dariya yace "ba zan yi magana ba ni, a aikace zaki ga kalmar missing din" na dan ture shi nace "nan dai gidan ummee ne ba gidan mu ba, dan haka mind your steps" na fara tafiya dining ya biyo ni, yace "ai itama tasan ba zata hanani matata ba, in kuwa ta gwada to akwai rigima" na jawo masa kujera ya zauna, na sunkuya dai dai fuskarsa nace "albishirinka?" Yace "goro" nace "a dakin ummee nake kwana a kan gadonta tare da ita" ya yamutsa fuska yace "da kenan, likacin bana nan, yanzu nazo dole a bani matata" nace "to idan tazo sai ka gaya mata" yace "kunyarta nake ji. Shine dazu kika gudu kika barni tare da ita ko?" Na fara bude masa dishes din gurin nace ya zabi wanne zanyi serving dinsa first, amma ga mamaki na sai naga sam bai wani rude akan abincin ba kamar yadda nayi tunani, ni kawai yake kallo, nace "food always come first, hausawa suna cewa ci shi yake gaba da sallah ma" ya daha gira yace "not to me" sallamar ummee mukaji, ina kallon sultan ya wani sunkuyar da kansa kasa, kamar zanyi dariya na maze na fara zuba masa abinci, ummee ta karaso ta zauna tana kallonsa yadda yake juya cokali a cikin abincin, ta kalleni tace "in bashi yake so ba ki zuba masa wani mana" ya dago kai yana kallona yace 'it is OK, am just tired ne, shi yasa" tace "try to eat something then, sai kaje kayi wanka ka kwanta ka huta" yana kallona nayi sauri na dauke kaina na tafi na fara serving ummee, nima na zuba abinci na na fara ci, ummee gaba daya hankalinta a kansa yake, nima ina kallonsa ta gefen idona, a hankali ya fara cin abincin kuma, sai kuma ya fara ci da dan sauri, muka hada ido da ummee mukayi murmushi, yace "this food is really good" nace "ummee ce ta yi shi, for you, ita ta girka all this food, for you" yana shafa kai ya dan kalleta yace "thank you" tace "bani kadai nayi ba ai, tare da maimunatu mukayi" ai kuwa sultan ya zage yaci abincin sosai, kusan komai sai da na zuba masa yaci, yana ci kuma yana santi, ummee sai tsokanar sa take yi yana zuba mata zance, kunyar ta fara tafiya. Muna gamawa ummee tace "an kai maka kayanka dakinka, maimunatu sai ki raka shi yayi wanka ya huta ko?" Na dan bata rai irin ni bana so din nan, ya mike ya fara tafiya, har yakai bakin kofa ya juyo yana kallona yace, "ban san gurin ba fa, sai anzo an nuna min" ummee ta harare ni tayi min alamar go da hannunta, ni dai duk kunya ta ishe ni, na bishi a baya. Muna fita nayi gaba, nasan gurin dama ummee ta nuna min sanda ta zagaya dani gidan, katon palo ne da three bedrooms, komai na gurin red and cream ne, hatta electronics din gurin. Muna shiga ya rufo kofa yana kallona, nace "welcome to gidan ka da baka san dashi ba" kallo daya yayi wa dakin yace "wato da ba zaki zo ba ko?" Na saka hannu ina shafa sajen sa, ya lumshe ido yana kara kwantar da fuskarsa a hannuna, nace "Ummee tana gurin kuma sai kawai in yi saurin tahowa? Kai ma kanka kake cewa kana jin kunyarta ballantana ni?" Ya dora hannunsa akan cikina, sai kuma ya danyi murmushi yace "ya naji kamar ya kara girma ne wai? How is she?" Nace "He is fine, yayi missing Daddy dinsa". Bedroom daya na kai shi na hada masa ruwan wanka, shi lallai wai sai dai muyi tare ni kuma bana son in bata kalliyata ummee ta gane. Amma ina sam bai fahimci wannan yaren ba, da nayi masa taurin kai ma dauka na yayi har ni har kayan jikina ya saka a tub, ba kwalliya ba har kaya na ma na bata kenan. Ba zan iya lissafa tsahon lokacin da muka bata a bandakin ba, dan anan aka nuna min duk missing din da ake ta fada min kuma na fahimci lallai anyi missing din nawa. Sai daya karar min da duk energy na dan kasa fitowa nayi daga toilet din sai shi ya fito dani ya dora akan gado, ya kunna room heater ya saka jallabiyya ya fita, naji dadin dumin da dakin yayi na fara bacci, cikin baccin naji dawowarsa, na dan bude ido na ganshi da tray a hannunsa, ya ajiye yana cewa " kinsan dai babu kyau baccin la'asar kuma kike yi ko?" Na dan tashi ina kara jan bargo jikina, ya kama bargon zai cire na saka kara yayi dariya yace "as if U don't know what is there" nace "oho dai, ba zan bude ba" to amma dai zaki sha madarar nan ko? Tunda kince na karar miki da karfin ki to gashi nan na biya ki" ya zubo madarar ya miko min, shima ya zuba ya zauna a bakin gado yana sha. Anan yake bani labarin da kyar Takawa ya barshi ya taho, yana so yazo din kuma baya son rabuwa dashi. Muka zauna kowa yana bawa dan uwansa labarin abinda ya faru bayan rabuwa, amma sam ban bashi labarin da ummee ta bani ba, a ganina wannan ba hurumi na bane ba, nafi son ta bashi labarin da kanta yadda hakan zai kara karfafa alakar su. Sai da mukayi sallar magrib sannan muka fara shirin fita, ga kayana har underwears a jike a toilet, na rasa inda zan saka kaina, sultan ya saka kaya yabani jallabiyar sa yace in saka, na saka na dauki mayafin doguwar riga ta na saka, muna fita dakin da aka sauki Hafsat na tafi da sauri dan bana son Ummee ta ganni, Allah ya taimake ni dakin a bude yake na shiga na samu kayan ta na saka sannan na tafi palon ummee, sultan na gani a bakin kofa wai kunya yake ji ya shiga shi kadai, ni kuma nace kunya nake ji mu shiga tare, muna ta muhawara sai gata ta bude kofar tana kallon mu, duk muka sunkuyar da kai kamar wasu munafukai, tace min "shine kika gudu kika barni da girki ni kadai ko?" Na dan sosa kaina nace "I tot abincin dazu zai isa har dare" tace "sai kije kiyi arranging table din" ta matsa ta bamu guri muka shigo, tana kallon sultan tace "welcome little love" da alamar tsokana a muryarta, ai kuwa sultan harda rufe fuska, ni kam dariya nake masa, ni banga abin kunya a uwa ba, tana shiga daki ya biyo ni dining room "wai baki lura cewa she looks too young ba?" Nace "eh na gani mana, amma ai dama jikinsu da namu ba daya bane ba, plus bata hayaiyafa ba, haihuwa kuma tana daga cikin abubuwan da suke saka mata tsufa" yace "ni kunyar ta nake ji wallahi" nace "wai menene abin kunyar a ciki?" Yace "yanzu fa kinsan tayi min tsarki ina baby, nayi mata a mai a jiki" nace "amai kadai? Kayi mata kashi kayi mata fitsari duk a jikinta" da sauri yace "no, banyi ba" nace "in tazo a tambaye ta?" Yace "a'a a bar maganar kawai" nace "she gave birth to you sultan, she nurse you, she fed you, and she loves you more than anything in this world". Kafin mu fara dinner na kira Hafsat tace min ba zasu dawo yau ba, a gidan su zayed zasu kwana saboda suna shirye shiryen komawa England. Muna gama dinner nace da ummee bara in je daki, ina shiga daki nayi kwanciyata sabida dama sultan ya tara min gajiya. Sai wajan ten na tashi nayi sallar isha, na dan bude kofa na leka falo, still sunanan, sultan na gani durkushe a gaban ummee ya dora kansa akan cinyarta, bana ganin fuskarta amma ina jin muryarta tana masa magana da alamar tayi kuka, na mayar da kofar na rufe na koma na cigaba da baccina. Cikin baccin naji tana tashi na, na farka da kyar ina kallonta, tace "tashi ki tafi dakin mijinki, da safe kya dauki kayanki" zance nata a'a tace "I insist" dole na tashi na dan dauki abubuwan da zan bukata, itace ma mai tuna min da wani abin, ni dai duk kunya ta ishe ni, na dau kayana na fita. Ina shiga part din sultan na tarar har ya kwanta, motsina ne ya
Chapter 166 · 0% Book details