← Book details Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 190

Sashe 52

Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Nayi nisa sosai a harkar project dina dan kadan ya rage min in kammala, haka zalika project dina na psychology ma, wanda kachokam akan Sultan nake rubuta shi, ina ware light side dinsa wato behaviors dinsa da mutane suka sani da kuma shadow side dinsa wato behavior dinsa da yake buyewa, wadanda sune hakayensa masu kyau, anan na fahimci cewa halayen Sultan masu kyau sun ninka marasa kyau dan kusan rabin halayensa marasa kyau shaci fadi ne, rabin abubuwan da ake cewa yayi bai yi ba, wadansu abubuwan ma shi yake kirkira ya ce yayi saboda ya kara wa kansa tabo, gashi yanzu tabon shi zai iya jawowa a hana shi aure na. Dama hausawa sunce rana goma ta barawo rana daya ta mai kaya, rannan muna tafiya a makaranta ni da sultan wani bature dan ajinmu ya tsayar dani muna magana, Sultan duk ya gama kulewa sai faman taje kansa yake da hannunsa. Can dai ya gaji yazo ya taba Jack ta baya, ya juyo sultan yace masa "ita wannan da ka sakata a gaba kana kallonta kana mata surutu tayi kama da uwarka ne?" Jack ya bishi da kallo bai san me yace ba, Sultan ya sake cewa "Uwarka nace, shege da fuska kamar danyen kosai" ni dai ina ta kunshe dariyar da take neman kwacemin, kawai kamar daga sama sai ganin yaya Habeeb nayi a gurin yana kallona da mamaki, nan take dariyar ta tafi zuciya ta ta fara lugude a kirjina. Na gaishe shi sannan Sultan shima ya lura dashi ya bashi hannu suka gaisa, bai kuma cemin komai ba ya wuce warsa ya tafi. Tun daga lokacin ban kuma samun walwala ba har na koma gida, nasan yaya Habeeb ya taba kora min warning akan sultan kuma a lokacin nace masa babu komai a tsakanin mu to yanzu gashi ya kuma ganin mu tare kuma a England bama a Nigeria ba. Har dare ina ta sake saken amsar da zan bashi in ya tambayeni. Ina shirin kwanciya kuwa sai ga kiransa a waya, na dauka yace "ki same ni a palo" daga nan ya kashe. Na riga na gama shirya abinda zan gaya masa dan haka da confidence dina na fita gurinsa. Wani mugun kallo yake bina dashi har na zauna yace "me yake yi a garin nan kuma a Oxford kuma a tare dake?" Nayi gyaran murya nace "yaya Habibi" ya katseni "don't yaya Habibi me, ki gaya min gaskiya in ba haka ba straight daga nan sai gurin mommy zan kai ki" nace "yaya Habeeb kasan ina yin psychology, to an bani project topic" kaf na bashi labarin project dina da yadda na lura characters din sultan sun dace da project din nawa nace "to abinda yasa nake tare dashi kenan, idan ban jawoshi a jikina ba bazan iya studying dinsa yadda ya kamata ba. Amma da zarar na kammala aiki na a kansa zan yi masa kafa" naga kamar bayani na bai gamshe shiba na tashi na dauko laptop dina ba bude masa aikin da nake yi akan sultan ya karanta, sai a lokacin naga yayi ajjiyar zuciya yace "OK, but you have to be very careful, guy din is very dangerous" daga nan ya tafi ya barni ina tunani. Anya kuwa abinda nayi dai dai ne? Shi kanshi project din da nake rubutawa har yanzu ban gaya wa Sultan ina rubuta shi ba, gashi kuma nayi wa yayana karya akansa, Sultan ya sha gayamin cewa baya son secret. Amma in banyi haka ba menene a binyi. Kullum ina cikin feeling guilty saboda karyar da nake tayi ina boye boye. Dole in nemi mafita.

Na yanke shawarar zan daina ganin sultan har sai na samu solution, time is running out. Bani da abinyi a school wannan week din dan haka nayi zamana gida naki fita, wayar duniyar nan sultan yayi min amma naki fitowa nace masa bana jin dadi, wani lokacin sai yayi kamar yayi fushi amma ana jimawa zai kara kirana. Ranar Friday sati guda kenan bamu hadu ba, muna palon mu ni da Amina muna kallo har after 12, daga nan na fara jin bacci nayi mata sallama zanjr in kwanta tunda yanzu mun raba daki ita tana spare dakin part din mu. Ina bude kofar dakina naji kamshin Sultan, nayi sauri na mayar da kofar na rufe ina wara ido, aikuwa ga mamakina shi dinne a tsaye a bakin window. Da sauri na na saka lock a jikin kofar na juyo na rasa ma me zance masa "Sultan how do you get in here" ya nuna min taga, nace "amma duk security din gidan nan ta ya akayi ka wuce get na farko dana biyu, ka zagayo baya, taya akayi ma kasan waccece window na" devilish smile yayi kafin yace "baki san waye Sultan ba har yanzu" lallai sultan ya wuce duk inda nake tunani, tsalle yayo daga inda yake ya fada kan gado na kamar wani karamin yaro, sai da katakon gadon ya amsa, ni maimunatu yau na shiga uku katon gardi akan gadona, yanzu idan mommy ta shigo gurina fa? Ko Amina? Ta yaya zan fara yi musu bayani? Na tabbatar in aka zo aka kama Sultan a dakina to babu wani bayani da zanyi wa daddy ya aura min shi kuma. Nace "Sultan dan Allah ka tafi, this is very dangerous wallahi, idan wani ya ganka fa?" Bai bani amsa ba sai jawo bargo na yayi yana shanshanawa yana wani lumshe ido "hmmmmm I so much miss kamshin ki wallahi" ikon Allah sai kallo, anya sultan kansa daya kuwa. Sai a lokacin na kalli kayan jikina, riga da wando ne na bacci, Allah ya soni dogaye ne sai dai linon ne masu bin jiki. Nayi sauri na dauki hijab din sallata dogo har kasa na saka na bata rai nace "Sultan ka fitar min a daki" ya mike shima ya hade rai ya zo sai tin fuskata yace "if not?" Na kara bata fuska nace "zan danna button din alarm mintu biyu yayi yawa security zasu cika dakin nan har daddy da mommy na" ya kawo fuskarsa dai dai tawa yace "then go ahead and do it" mamaki ne ya cika ni na saki baki ina kallonsa shi kuma ya tsare ni da ido, can yace "nasan ba zaki iya ba because you love me too" murmushin mugunta ya sake yi min sannan ya koma ya yi adungure akan gadona. Ya gyara kwaciya tare da bubbuga gadon yace "zo ki kwanta" na watsa masa harara, yayi dariya yace "I will not touch in abinda kike gudu kenan, ni kaina kishin kaina nake yi akan ki, I can't bring myself to touch you. Zuwa nayi in ganki kuma muyi hira. Me yasa kika ce min baki da lafiya bayan kuma lafiyar ki kalau" na tabe baki nace "in kana son muyi magana ka fitar min daga daki gobe sai mu hadu muyi magana" shima tabe bakin yayi yace "OK then, sai da safe" daga haka ya gyara kwanciya yaja bargo ya lulluba, da sauri na karasa bakin gadon "sultan ka tashi ka fita don Allah" rokonsa nake tayi amma kamar ba dashi nake ba dan ko motsi bai yi ba, idansa a rufe amma nasan bai yi bacci ba. Na tsaya kawai ina kallonsa. Ina bin kowanne feature na fuskarsa da kallo, ban taba kare masa kallo irin haka ba, naga yadda akayi trimming sajensa yayi kyau sosai da yadda sajen ya kwalta akan fatar sa daga dukkan alama zai yi laushi, ji nayi a raina kamar in kai hannu in taba, nayi sauri na mike tsaye na bar gurin na koma bakin kofa ina tunanin abinyi, inna ce zan koma palo in kwanta that means kofar dakin zata zama a bude kenan and I can't take that risk, wani zai iya shigowa yaga sultan, and I can't take the risk of sleeping with sultan saboda I don't trust him and I definitely don't trust myself akansa. Muryarsa naji yace "in kin gama lissafin ki kashe fitila saboda bana iya bacci da haske" wato idonsa biyu ma ashe. Kofar ban daki na bude na shiga ina lissafin ko anan zan kwana ne? Kai gaskiya bazan iya kwana a toilet ba, nayo alwala na fito, ina fitowa na tarar har ya kashe fitilar ya koma yayi kwanciyarsa. Na dauki pillow na koma can bakin kofa na ajiye. Windows din dakin na rufe nayi locking ta ciki sannan na karo karfin AC. Na dauko wani bargon naje inda pillow na yake na shimfida rabi sannan na kwanta na kudunduna ba hijab din jikina sannan na sake lulluba da sauran rabin bargon. Oh ni Maimunatu naga ta kaina, yau zan kwana da gardi a dakina.

*wannan dai kam har da arias nayi muku, I love you guys so much. Stay blessed

Episode Forty Three: America
Chapter 52 · 0% Book details