← Book details Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 190

Sashe 33

Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kitchen na shiga na tarar da cook tana ta aikin dinner, na dauki vegetables na fara yankawa sai ga mommy ta shigo ta tsaya tana kallona saboda ni bamai son girki bace, sam bana shiga kitchen in ba dole ba. Kit na yanke hannuna da wuka, da sauri mommy tazo zata rike hannuna na ja da baya na fice daga kitchen din, ina jin ta tana kirana na bude kofar main palo na fita hannuna yana jini. Har na dau hanyar gate sai na tuna kayan jikina yadda suke sai na dawo na koma cikin palo, ina jin Amina tana yimin magana itama na rabu da ita. Sam bana so ayi min magana. Extra dakin da yake part din mu na shiga, na shiga toilet na wanke ciwon hannuna, na daure shi da handkerchief. Har dare ina dakin ban fito ba kuma har lokacin hawaye bai zubo a idona ba. Nayi sallar magrib da isha, Hafsat ta kawo min abinci tace ta gayawa mommy bana jin dadi, nace mata na gode. Na kwanta amma bacci ya gagari idona sai juyi kawai nake yi. Cikin dare naga ba bacci babu labarinsa, na tashi nayi alwala nazo na fara sallah. Ni kaina bansan raka'a nawa nayi a ranar ba, kuma duk sujjada sai na roki Allah ya chire min Ibrahim daga raina. Har aka yi sallar asuba, nayi sallah na zauna ina azkar anan bacci ya dauke ni. Mommy ta shigo ta dubani taji jikina yayi zafi, nan ta kama fadan me yasa na kwanta ni kadai? Nan da nan aka kirawo Victoria, tana gwada jini na kuwa tace ya hau. Dama nasan haka zata kasance saboda yadda nake jin wani azababben ciwon kai. Mommy ta saka ni a gaba akan lallai sai na gaya mata menene matsala ta amma nayi shiru, fada take kamar zata ari baki. Ni dai na samu akayi min allurar bacci nayi kwanciyata. Ranar wuni nayi a gida ban je school ba. Washe gari Saturday tun safe nace da daddy ina son zuwa bakin ruwa (beach), ya barni saboda yana ganin fresh air zata taimaka min, amma yace mu tafi tare da Hafsat da Amina. Ban so haka ba saboda so nake in zauna inyi tunani. Muna zuwa bance musu qala ba na dau handbag dina nayi gaba, sai da na samu gurin da babu kowa sannan na zauna a kasa ina kallon ruwan.

When was the last time I had a serious conversation with myself? Me ya faru da ni ne? Ina wannan yarinyar 'yar makaranta who is loved by all? Na tuna da medal din da school din mu ta bani, to the most talented student the school has ever had. Ina dreams dina na zama likita in bude private hospital a Nigeria in ringa taimakawa marasa karfi wadanda ba zasu iya zuwa kasar waje ba? My life was so peaceful before kuma ina so ta koma kamar da. Indai har ina so in koma kamar da i have to let go of Ibrahim. Tabbas ya samu guri a zuciyata yadda bazan taba iya goge shi ba, amma zan iya tura shi baya yadda bazan ke tuno shi ba. Tabbas wani barin na zuciyata is 100% sure cewa Ibrahim yana so na amma mai yasa yayi aure? Nasan maganar Hafsat zata iya zama gaskiya cewa takura masa akayi amma still ya kamata ace ya neme ni ya gayamin abinda ya faru, na bar masa sako a gida kuma nasan da yaje da baba Habu ya kira ni ya gaya min. Tunda har bai neme ni ba yana nufin yayi accepting auren kenan, he looks happy in the wedding picture. Duk da ya taba gayamin cewa baya son Efi amma tana da chance din da zata juyo hankalinsa kanta a matsayinta na matarsa. Duk da bani da shekaru da yawa amma nasan maza suna da one weakness, Sex, cikina naji ya hargitsa wani amai ya taso min, sex, kusan wata guda kenan da auren, they might have already done it by now. Da sauri na tashi na fara kwarara amai, Allah ya soni babu kowa a gurin, sai da na gama amai na sannan hawaye ya zo idona, na zauna na saka kaina a tsakanin cinyoyi na nayi kukana mai isata sannan na tashi, naje bakin ruwa na wanke fuskata da bakina. Na dauko handbag dina na bude na fito da hotunan da takardun da aka kawo wa Hafsat, daya bayan daya na ringa jefasu cikin ruwan suna tafiya, ina kallansu suna tafiya a saman ruwa sannan suka fara nutsewa kasan ruwa. Na dauko waya ta na goge numbersa da na ke ta faman ajjiya, na shiga messages duk na goge messages dinsa da na kasa gogewa da, na saka hannu a handbag din na sake sauko letter dinsa, first letter din da ya fara rubutomin, na bude na sake karantawa sannan itama na jefa ta ruwa, abu na karshe shine CD din daya aiko min, na dauko ina kallon rubutunsa da yayi da permanent marker a jikin CD din, I LOVE YOU, a hankali nace I love you too Ibrahim but I must let you go, na jefa cd din shi ma cikin ruwan

Episode Thirty One: Let it go

Ina kallon cdn ya jima yana floating sannan ya nutse. Na dauke kaina na koma hanyar inda na baro su Hafsat. Tun daga nesa na hango alamar abinci suke ci, sun shimfida blanket suna zaune akansa. Na karasa da sauri nace "ina fatan dai baku cinye sandwich din nan ba" Amina ta kalleni da mamaki tace "au da jira kike yi mu rage miki? Kinga na hannuna shi ne na karshe, sai dai kisha fruits" ban yi wata wata ba na kwace na hannunnata na tura gabaki daya a baki na, ai kuwa ta taso kaina lallai sai ta kwace, suka hadu ita da hafsat suka danne ni, Hafsat ta kama yi min chakulkuli ina dariya Amina ta kwakule sandwich din daga bakina, sai kuma ta jefar dashi a kasa tace "ew, duk ta saka yawu a ciki" Hafsat ta daga ni tana karkade jikinta saboda dan squeezing da kayanta suka yi, na faki idonta na damko kasa cikin hannuna na watsa mata ta cikin wuyan rigarta. Tsayawa kawai tayi tana kallona cike da takaici, Hafsat da shegiyar tsafta, kuma na tabbatar kasar ta shiga har cikin brazier ta. Ta ma rasa me zata ce min duk masifar ta. Sai kawai ta juya baya tana karkade rigarta ni kuma na cigaba da kyalkyala mata dariyar mugunta, banyi aune ba kawai sai jin kasa nayi a fuskata, har cikin baki na dana bude ina dariya. Nan take wani fadan ya kuma rinchabewa kowa yana watsawa kowa kasa. Kasa har cikin gashin mu ranar sai da ta shiga. Sai late evening ranar muka bar beach din gabaki dayan mu munyi kacha kacha. Muna shiga palo mommy ta mike "what in God's name happened" Hafsat ta nuna ni tace "ita ce ta fara" mommy ta juyo da dubanta kaina, kafin tayi magana na yi sauri nace "aga wanda zai fara zuwa toilet" nan muka dau gudu muka yi dakin mu muka bar mommy da sakakken baki.

Tun daga ranar na mayar da hankali na wajan gyara rayuwata, daga naji Ibrahim ya fado min araina sai in fara wani abin da zai dauke hankali na. Addu'ah kuwa kullum sai na yita. Lecturers din mu sunyi marking report din da na rubuta sun turo wa daddy, ya kira ni naje na same shi a zaune shida mommy ya miko min takardar hannun sa yace "karanta a fili inji" na bude hannuna yana rawa na fara karantawa, As da Bs ne duk, ko C babu, na ajiye takardar na rufe bakina ina dariya, daddy shima dariyar yake yi yace "ashe zaki iya, da wato ganin dama ne bakiyi ba ko?" Mommy tace "Moon ai tamkar mai aljanu take, yau fari gobe baki, ni kaina ban san inda ta sa gabanta ba" daddy yace "at least she is doing good yanzu" ya juyo ya kalleni yace "Moon, ina so in cigaba da ganin irin wannan result din, bana son wannan mood swings din naki. Kina da kokari, kiyi amfani da brain din ki yanzu da kike da chance" nace "nagode daddy, insha Allah abinda ya faru a baya ba zai kuma faruwa ba".

Yanzu a makaranta bama tare da Hafsat, dan haka kowa harkar gabansa yake. Amma hakan bai yi affecting dina ba kamar yadda nayi tsammani, na mayar da hankali na sosai akan karatu na, nan da nan na fara sabawa da mutane, lecturers duk sun sanni saboda ni ina da saurin shiga ran mutane. Turawa, blacks da sauran kabilu duk kowa nawa ne, maza da mata. I am very serious akan karatu but I am not boring, I am very friendly.
Chapter 33 · 0% Book details