← Book details Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 190

Sashe 77

Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

ganin shine dai dai a gareni, amma ni abinda ban fahimta ba shine dalilin ta na kin gayawa daddy bayan kuma nasan komai tayi sai ta gaya masa. Ina nan kwance abin duniya ya ishe ni gwoggo Sa'a ta shigo tace in tashi inyi sallah inci abinci, bayan na gama ne ta tambayeni "Maimoon wai me ke faruwa ne tsakanin mommyn ki da daddyn ki?" A raina nace wannan tsegumi take so kenan, na daga mata kafada alamar bansani ba, daga nan bata sake cewa komai ba. Mommy suka shigo tare da daada, ko kallon inda nake bata yi ba ta shige toilet tayo alwala tazo ta tayar da sallah, daada tana ta 'yan mitocinta "ba shikenan ba, sai kije ai ya aura miki ko ma waye yaga dama, duk abinda ya fari kuma daga baya kar ki zo gurin mu, ki je can ku karata ke da baban naki" ni duk maganganun da take yi ban fahimci me take nufi ba dan haka kawai kallonta nake yi, mommy ta idar da sallah ta mike ta tsaya a bakin window tana kallon waje, muna haka sai ga dan aike daga waje "wai Maimoon tazo su tafi" na mike ina saka hijab dina nace "mommy ance mu fito" ta juyo ta kalleni tace "ance ki fito dai, ko kinji an ambaci sunana?" Na yar da hijab din hannuna na karasa kusa da ita nace cikin rawar murya "mommy ba tare zamu tafi ba?" Ta juya min baya tace "no, am going to stay here for a while, go with your father " na durkushe a gurin duk farin cikin komawa gida ya gushe daga zuciya ta, na rike kafarta nace "mommy ni bazan koma gida ba tare da ke ba, mommy dan Allah kiyi hakuri ki zo mu tafi, mommy in dai akan maganar Sultan ne zaku samu matsala da daddy wallahi ni na hakura da shi. Kun fiye min dubun sultan wallahi. Dan Allah mommy kiyi hakuri kice kin yafe min" kuka nake sosai. Ta dago ni ta rungume ni tace "ni na yafe miki tun tini Moon. I just wanted to clear the mess you created" nayi sauri nace "to in kin hakura kizo mu tafi gida tare" tace "that's not up to me, daddyn kine yayi fishi bani ba" na chika ta da sauri nasaka hijab dina na fita, a compound naga daddy tare dasi kawu, ina fitowa yace "taho da sauri mu tafi dare yana yi" ina zuwa na durkusa akan gwuiyoyina ina hawaye nace "daddy dan Allah kayi hakuri, wallahi ni na hakura da koma menene yasa kuka samu matsala da mommy, it's all my fault. Dan Allah kuyi hakuri mu koma gida gaba daya, ni ba zan iya rayuwa babu mommy ba kuma bazan iya babu kai ba" ya dago ni yace "it is not your fault Moon, kowa akwai destiny dinsa a rayuwa. Ita kuma mommyn ki ita tace tana son ta zauna anan for sometime, bani nace ta zauna ba, if you can get her to go with us then I will be more than happy" na koma ciki da sauri nace "mommy daddy yace ki zo mu tafi tare" tana kallona tace "shi ya gaya miki hakan?" Nace "eh" kafin ta sake magana kawu sharu ya shigo ya kama bambami "ya zaku ke wani abu ne kamar yara Fatima? Kece me laifi kuma kece mai fushi? Shi kenan kuma kinyi laifi sai kice ba za'a yi miki fada ba? Dan kin samu miji mai hakuri ko?" Ya juya kan daada A cigaba "duk kece kike daure mata gindi ai, kin barta sai abinda taga dama take yi, ai ba gata kike mata ba" sai da ya wanke su tass sannan yace mommy ta fito mu tafi. Fuu ta wuce ni tayi gaba, da sauri2 na bita a baya.
Chapter 77 · 0% Book details