Sashe 107
Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Da yamma na fita balcony, nan ne gurin zama na yanzu indai ina son in jini ni kadai ko in ina son muyi waya da sultan. Na dafa railer na dauko wayata ina kokarin kiran sultan kawai ina daga ido na na hango shi, duk da cewa da akwai distance a tsakanin mu kuma gari ya fara duhu amma na gane shi, yayi packing dan nesa da gidan mu kadan yana tsaye ya jingina da jikin mota ya rungume hannayensa a kirjinsa. Wata irin muguwar faduwa gaba na yayi, Allah kenan, babu yadda baya juya lamarin sa, da akwai lokacin da kullum nake tsayawa a balcony din nan ina kallon waje hoping zan ganshi amma yau gashi ina kallonsa amma maimakon inji dadi sai faduwar gaba da ji. Allah ne kadai yasan dadewarsa a gurin, Allah ne kuma kadai yasan dawa yayi magana. Nasan Sultan dai bai dawo gida ba, baya zuwa yanzu sai dare yayi sosai saboda mutane. Kamar ance ya dago ido sai ga idonsa a cikin nawa, da sauri yayi kamar me shirin tahowa ni kuma nayi sauri naja da baya yanda zai daina ganina. Saboda faduwar gaba har daci nake ji a bakina, na shiga uku, na leka a hankali naga har yanzu balcony din yake kallo. Na koma daki da sauri na shiga toilet, sai da nayi calming down sannan na kira sultan. Yace "Hello love" nace "hey kana ina ne?" Yace "naje karbo mana sauran dinkunan mune. What's up?" Nace "babu komai. Kawai da ina so inji ya kake ne" yayi dariya yace "thanks love, ko in taho ne?" Nace "I would appreciate that amma kasan gidan yanda yake yanzu, ballantana yanzu da yamma" yace "right, nima daga nan zanje wajan Daniel ne yazo gari, so sai dare zan shigo gidan, hope ba za kiyi bacci ba kafin inzo" nace "yeah, bazan yi ba sai kazo, bye" muna gama wayar na koma na leka balcony naga har yanzu Ibrahim yana tsaye. Da sauri na sauka kasa dakin Hafsat na same tana shirya kayan khairat, tace "lafiya? Waye ya koro ki?" Nace "Hafsat Ibrahim ne yazo yana waje" tace "and? Kina nufin fita zakiyi gurin sa?" Nace "no, ke nake so kije" ta yatsina fuska tace "ni? Allah ya tsari gatari da saran shuka" nace "Dan Allah Hafsat kije kiyi masa magana, make him understand abinda yake so ba zai yiwu ba" tace "in baki shawara? Ki kira David ki hada shi da shi, nayi miki alkawarin ba zaki kara ganin sa ba" na girgiza kai da sauri, Hafsat ba zata fahimci abinda nake nufi ba, babu wanda zai fahimci situation dina sai wanda ya taba shiga irinsa. Ma zauna a bakin gadon ta nace "I don't want to hurt him, I don't want to hurt Sultan. Please help me" ta dan jima tana kallona sai kuma ta dauki hijab ta saka tace "amma kin san dama can ni ba shiri muke yi da shi ba, dan haka ba lallai ne yanzu ma mu fahimci juna ba" tana fita na koma sama da sauri na kuma shiga balcony, ya baro jikin motar ya dawo dai dai opposite din gidan mu, ina kallon Hafsat ta bude gate ta fita. Yana ganin ta yayi saurin karaso wa wajanta, bana hango su sosai yanzu, sun jima suna magana sannan daga baya naga ya juya ya tafi wajan motarsa, kafin ya bude motar ya sake juyowa ya kallo balcony din sannan ya shiga ya tafi. Na dawo daki na zauna ina sauke ajjiyar Zuciya, ina jin kuma babu dadi a cikin raina, but haka Allah ya tsara mana ni da shi, we are not destined to be together. Ina nan zaune har Hafsat ta shigo, ta jefo min wani complimentary card tace "gashi nan yace a baki, he is so hot headed sai da na kusa loosing temper dina, he believes hada ku aure akayi da Sultan, yace yaji labarin dan sarkin garin nan ne, shi a ganin sa kin yarda da auren ne saboda babu shi. Yayi yayi in bashi number dinki na hana shi shine ya bani card dinsa yace in baki ki kira shi, yace in baki kira shi ba zai sake dawowa gobe" ta zauna a kusa dani tace "Moon, ki kira Sultan ki gaya masa halinda kike ciki, he will know what to do" na girgiza kaina nace "Sultan will definitely hurt Ibrahim in na gaya masa" tace "to ki fada wa David ya hana shi zuwa gidan nan" nan ma na girgiza kai "securities will treat him badly and I don't want that" ta mike a fusace tace "to hada kayan ki ki kirashi yazo ya dauke ki ku gudu tare a fasa auren" ta fice a fusace ta bugu min kofa. Kwalla ce ta taru a idona ina jin zafi a raina. Na sunkuya na dauki card din nasa, kallo daya nayi wa number din na haddace ta na jefa card din a waste bin. Ina bukatar inyi addu'ar sosai in nemi Allah's guidance. Ranar kam da daddare haka na tashi nayi ta jero adduoi akan Allah ya fitar dani daga matsalar da nake ciki, Allah ya saka wa Ibrahim dangana ya fahimci cewa ni ba matar sa bace ba.
Seven days....
Seven days....