← Book details Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 189 OF 190

Sashe 189

Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ma'aikata. Sai da komai ya kammala sannan ya damka ta a hannun abokin sa Mahmud, nan take aka bada cigiyar yara wadanda aka yar a titi da kuma marayu da suke basu da galihu, daga 'yan kwana daya zuwa shekaru goma sha biyar, babu jimawa orphanage din ta cika taf, sultan yace shi baya son publicity, ba ya son ma asan cewa shi ya gina, dan haka ya bar ta a hannun Mahmud sai dai duk wata zasu yo masa bill din abinda suke bukata sai ya tura musu. Lokaci zuwa lokaci kuma muna zuwa mu gano halin da yaran suke ciki, kuma sosai muna jin dadin abinda muke gani dan mahmud ya rike amana sosai. Ranar da muka fara zuwa sai da nayi kukan tausayin yaran nan, wadansu jarirai wadansu 'yan kananan yara kuma wai duk marayu ne, amma kuma Alhamdulillah, gaskiya suna samun kulawa sosai dan sultan yana sakar musu kudi, abincin da suke ci ko wadansu yaran da suke zaune a gaban iyayensu ba zasu samu kamarsa ba. Sai dai soyayyar iyaye ce dole sunyi missing din ta. A duk wata sultan yana gama ware mana abinda zamu bukata na watan to next shine orphans dinsa, sai ya ware musu sannan komai ya biyo baya. Kullum kuwa arzikin sultan karuwa yake yi, kowanne wata abinda yake samu yafi na watan daya gabata. Al'ameen yana da shekara daya a duniya muka nemi admission ni da Hafsat muka koma karatu, an sha rigima kafin su Ummee su yarda in tafi, twin house din na su Hafsat muka karba rent muka zauna a can. Kafin muje Zayed ya gama yi mana duk harkar registrations, dan haka ina zuwa karatu kawai muka fara. Bamu dade da fara karatu ba Hafsat ta haifi third child dinta, a girl, Aaysha. Daga nan kuma sai ta tsaya tace tayi uku sai ta huta kuma. Muna can Amina ta haihu itama, mun sami baby boy wanda yaci sunan marikin Ibrahim, Abdulshakur. Zaman mu tare dasu Hafsat ya kara dankon zumunci sosai tsakanin zayed da sultan, dan zayed zama yayi tamkar brother din sultan tunda dama sultan bashi da brother. Ni kuma da Hafsat zumuncin mu ya kara karuwa muka koma tamkar twins. Duk da cewa gidajen mu daban ne amma komai a tare muke yi, Al'ameen ya saba dasu khairat sosai. Bamu dade da komawa England ba Ummee ta matsa mana lallai sai da na yaye Al'ameen aka mayar dashi Nigeria gurinta. Nan fa Sultan shima ya damu da rashin Al'ameen saboda ba karamar shakuwa suka yi ba, shima Al'ameen a can kullum sai rigimar neman Dad dinsa da Mom dinsa, amma Ummee taki dawo mana dashi a haka har ya saba da ita sai dai muyi waya dashi ko kuma idan munje gaishe su. Shekarun mu biyu muna karatu muka kammala, kuma Alhamdulillah mun samu sakamako mai kyau. Ranar passing out dinmu family din mu sunzo sosai, dan har Takawa sai da yazo taya ni murna. A lokacin da cikina wata bakwai, wanda aka tabbatar min twins ne a ciki. Wannan ya saka sultan yace ba zamu koma Nigeria ba sai na haihu, lokacin haihuwata yana gabatowa ummee ta dauko al'ameen suka taho gurin mu, a haka har na haihu, wannan lokacin kuma Alhamdulillah da kaina na haihu ba'ayi min aiki ba, amma fa nasha wahala ba karama ba, na haifi mace da namiji wadanda a take sultan yayi musu huduba da sunan ummee da na Takawa. Muna kiransu da Bassam da Basma. Gaba dayansu babu wanda yayi min kara, dan kamar Ummee da sultan suka dauko sak. Sultan harda yi min gwalo yana tsokana ta. Bayan haihuwar twins muka tattaro muka dawo Nigeria. Tunda muka dawo naga sultan yana ta kumbiya kumbiya, nasan akwai abinda yake boye min amma na kasa gane menene. Wani lokacin idan yana waya ina shigowa zai katse, da yawan fita da yake yi yanzu har weekends in ya fita tun safe wani lokacin sai magrib zai dawo kuma ya dawo min a gajiye, in na tambayeshi ina yaje kuma sai yace min yana gurin Takawa ko kuma yace gurin Daddy yaje, ni kuwa nasan daga Takawa har Daddy babu wanda zai gajiyar da shi. Tun ina dannewa har na fara damuwa, rannan yana shigowa ya kwanta yana ta juyi nazo na zauna na saka masa kuka, tashi yayi ya zauna yayi tagumi yana kallona ina ta rera kuka na, yace "wannan shagwabar ta mecece kuma?" Nace "ba kai bane kake fita kullum kuma kaki ka gaya min inda kake zuwa" ya matso kusa dani ya jawo ni jikinsa yace "My Love, na gaya miki ba wani gurin nake zuwa ba fa, most of the times ina gurin Takawa" nace "ni dai ban yarda ba, yanzu haka ma zance kake zuwa" dariya yayi sosai yace "zance kuma Moon? Where on earth do you get this Idea?" Nace "to bayan kullum in kana waya ma in ka ganni sai ka kashe?" Ya sake dariya yace "Love how many times zan gaya miki babu wata a gaba na bayan ke?" Nace "you are acting otherwise. Tun da muka dawo Nigeria kake boye min wani abu, kuma nayi nayi da kai ka samo min aiki kaki yarda, ya za'ayi ace ban samu aiki ba, ina ka taba ganin doctor ya rasa aiki, na gaji da zaman gida, I want to do something, it has always been in my dream in ga na zama doctor ina taimakawa mutane" ya saka hannu yana share min hawayena yace "wannan shi yasa kike zubar min da precious hawayen ki? To tashi ki saka hijab dinki ki bar su Bassam a gurin nanny din su ki zo muje in kaiki inda nake zuwa kullum, in ma budurwarce zaki gani" na tashi da sauri ina jin excitement na saka hijab dina muka fita. Hanyar office dinsa naga mun dauka, a raina nace 'so yake ya wayance ya nuna min office yake zuwa kullum har weekends'. Amma kuma sai naga mun wuce office din kadan sai muka tsaya a next building after it. Ya fito ya zagayo ya bude min kofa nima na fito, muka jingina a jikin mota muna facing wani sabon gini wanda ko fenti ba'a yi masa ba, hawa biyu ne sama da kasa, kuma babba ne sosai. Sultan ya dora hannunsa a kafada ta yace "nan gurin nake zuwa kullum, bam sani ba ko anan budurwar tawa take?" Na dan ture shi nace "to amma ai kai ai architecture ne, menene hadin ka da field work kuma?" Yace "wannan ba aikin office bane ba, this is personal". Ya juyo dani ina facing dinsa yace " da banyi niyyar gaya miki ba har sai aikin ya kammala, amma tunda kin fara tunanin zance nake zuwa, gwara in gaya miki yanzu" ya cigaba "I am building a hospital for you. Shine wannan, tunda muka dawo nake aikinsa kuma almost na kusa gama wa. Takawa ya bayar da order za'a sayo miki duk machines din da ake bukata a asibiti. You will be the MD, sai ki dauki sauran ma'aikatan ki da kanki" na dan jima ina kallonsa kafin in fahimci da gaske yake bada wasa ba. Ai kuwa wani tsallen murna nayi na dafe jikinsa, shi kuma ya biye min ya ringa juyi dani a gurin in circles muna dariya, mutane har daga mota lekowa sukeyi suna kallon mu,, daga baya ya ajiye ni muka shige cikin building din da gudu kamar wasu yara. Da gudu muka rinka zagayawa room by room, sai na fahimci ma kamar gurin yafi girma daga ciki akan ta waje. I can't believe all this is mine. Muna gamawa na rungume sultan a jikina ina hawayen murna nace "bansan da wanne bakin zan gode maka ba. Na gode Allah ya kara maka budi, Allah ya raya mana zuri'ar mu" yace "Ameen my love, you deserve this and much more" daga nan ya saka babban dan yatsansa yana zagaya lips dina, ba sai na gaya muku abinda ya biyo baya ba. Lol. Daddy na fara kira na gaya masa, yace min ai already ya sani, sultan ya gaya masa tun kafin ya fara aikin. Na kira Mahdi na gaya masa abinda ya faru, nace "I will appreciate it if you will help me in running the hospital" yace "it will be my pleasure" sannan yayi min murna sosai tare da fatan alkhairi. Ranar har dare ina ta waya ina gaya wa mutane, kowa sai murna yake min da fatan alkhairi. Washegari da safe na shiga cikin gida nayi wa Takawa da Ummee godiya, Takawa yana ta yi min dariya wai sai washe baki nake yi, yace "haka zaki ke yiwa patients din naki?" Na sake washe bakin ina dariya. Ummee tace "yanzu menene plan dinki akan asibitin?" Nace "burina shine in rage kudin komai a asibitin, yadda mutane talakawa suma zasu ke samun best medical care a cikin kudi kalilan" Takawa ya gyada kai yace "Zakiyi mamakin kuwa yadda Allah zai saka miki albarka a cikin sa. In mutum ya fara business, ko wanne iri ne, idan ka saukaka kudin shine Allah yake saka maka albarka, idan kuma ka zafafa sai Allah ya barka da dabarar ka, wacce babu inda zata kaika. Sai kiga an fara business amma ko shekara ba za'ayi ba ra rushe saboda babu albarka a ciki" Allah yasa mu gane. Watanni uku bayan nan aka gama komai, duk kayan da akayi order sun zo an sassaka, na shiga na duba komai sannan na sake rubuta wani list din na sauran kayan da nake bukata, Daddy ne ya karba yace shima yana son a saka shi a ladan, babu jimawa aka kawo kayan gaba daya. Yaya Walid ne ya shirya min opening party a cikin harabar asibitin, kusan duk 'yan'uwa sunzo, har Hafsat da Zayed sai da sula zo da 'ya'yansu guda uku kyawawa gasu kusan kansu daya, nan ma sultan ya saka ta a gaba da tsokanar wai duk saurin ta gashinan mun kamo ta, uku take dashi kuma muma uku muke dasu, ta harare shi tace "neman in kulaka kake yi muyi, ni kuma bani da lokacin ka, besides ni bana kula kannena". Itama yanzu ta samu aiki a hospital din da zayed yake aiki. Sai wajan sha
Chapter 189 · 0% Book details