← Book details Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 116 OF 190

Sashe 116

Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na jima a tsaye a gurin ina kallon hanyar da yabi sannan na juya na shiga daki. Direct toilet na shiga nayo alwala nazo na fara sallali ina rokon Allah alkhairan da suke cikin auren nan da kuma tsari daga sharrukan da suke cikinsa, ban jima ba aka fara assalatu, na tashi na kawo raka'atainil fajri sannan na dora da subh. Ina idar wa Mommy ta shigo tace min "kizo inji Daddy n ku" na mike na bita a baya har part din Daddy, ina shiga na tarar dashi a zaune yana shan coffee, ya shirya tsaf daga dukkan alamu daga nan sai gurin daurin aure. Ba zauna a kasa na gaishe shi ya amsa mun fuskar sa a sake. Sai da ya gama shan coffee dinsa sannan ya fara min magana "maimunatu yau Allah yayi insha Allah nan da 'yan awanni zamu daura miki aure da Sultan wanda ke kika zabe shi da kanki mu kuma muka goya miki baya har Allah ya tabbatar mana da abin. To so far dai babu abinda zance sai Alhamdulillah. Na amince zan aura miki Sultan ne saboda abu biyu, na farko ina kwadayin ladan da zamu samu daga ni har ke in har burin mu ya cika na gyara rayuwarsa, abu na biyu kuma saboda tsananin sonki da naga yana yi, nasan wannan soyayyar zata iya saka shi yayi komai, wanda nake saka ran soyayyar ki zata iya saka shi ya chanza rayuwarsa. Auren Sultan da zakiyi tamkar jahadi ne. Duk abinda nayi a rayuwar sultan tamkar sharar fage ne akan wanda ke zaki cigaba dayi bayan auren ku. Sai kin dage sosai maimunatu. Nasan ke yarinya ce mai ibada amma ina so ki kara akan wacce kike yi da, ki dage da adduoi na neman tsari sannan ki tsarkake zuciyar ki daga dukkan sharri. In sha Allahu Allah yana tare da ke kuma bazai barki ki tabe ba. Ina son ki sani cewa dani da Mommy n ki muna tare dake 100% amma hakan ba yana nufin muna so mu san duk wani sabani daya shiga tsakanin ki da mijinki bane, duk abinda ya faru tsakanin ku mun fi son ya kasance ya tsaya a tsakanin ku, sai dai in har kinga yafi karfin ku sannan sai ki kawo mana shi mu kuma zamu yi iyakacin kokarin mu muga an samu maslaha a lamarin. Allah yayi miki albarka Allah, Allah ya baku zaman lafiya dake da mijinki" Mommy tace "Ameen" ya tashi yace "nina tafi" sai da suka fita shida Mommy sannan na lura cewa kuka nake yi ashe, ba goge hawayen idona ina jin alamar jikina yana daukan zafi kamar mai shirin fara zazzabi. Ina nan zaune har Mommy ta dawo daga rakiyar Daddy ta zauna kusa dani ta kamo hannayena tace "kuka kuma maimoon? Wa yace miki yanzu 'yammata suna kukan aure?" Nayi mamakin yadda Mommy take min magana a hankali cikin rarrashi babu fada, nan ta shiga yimin tata nasihar da kuma bani shawarwari akan harkar auratayya, na koma na kwanta akan cinyarta ina sauraronta kuma ina daukan duk abinda take gaya min. Muna a haka Hafsat ta shigo da khairat a hannunta suka hadu ita da Mommy suke ta kwantar min da hankali, Hafsat tana tsokanata da cewa "ke da zaki zauna ma a kusa da gida? Ko ihu kikayi da karfi Mommy zata jiyo ki" na dan yi murmushi kadan. Wayar Mommy tayi kara aka sanar mata mai gyaran jikina tazo, muka sauka kasa mukayi breakfast first sannan aka fara yimin kitso, dama na gaya mata ina son tayi min kitso shi yasa ma tazo da wuri. Kanana kitso ne irin na bare bari akayi min da kitson gaba da matar tayi masa wata tubka wacce ta rufe rabin ido na na hagu. Kowa yaga kitson nan sai sambarka. Bamu gama ba sai wajan sha daya da rabi. Ni dai duk hankali na baya kan wanda suke tare dani kallon agogo kawai nake yi gaba na yana faduwa, har daci nake ji a bakina. Ana gama yi mun kitson na sulale na gudu na tafi dakin daada, duk babu kowa a ciki dan duk suna part din mu, na shige cikin bedroom dinta na kwanta ina jin temperature dina tana kara hawa. 12:00 nayi na runtse ido na ina karanto duk adduoin da aka koya min a islamiyya. Around 12:30 na jiyo guda cikin gidan mu, gaba daya an dauki hayaniya. Nan take hawaye ya balle min. Kuka nake yi sosai amma ni kaina bansan dalilin kukan nawa ba. Shin na murnar na zama matar Sultan ne ko kuma na menene oho. Nasan ana can ana nemana a cikin gida dan ko waya ta ban taho da ita ba dan kar a kira ni. Suwaiba, wata 'yar uwar mu daga Niger ce ta shigo dakin ta ganni around 1:00 da sauri ta fita ina jinta tana bada sanarwar ai gani can a dakin daada. Kan kace kwabo dakin ya cika, tsofaffi da 'yammata sai tsokana ta suke wai azo aga amaryar zamani amma tana kuka, ni kam kamar kara zugani suke yi dan kuka na kawai nake yi bana sauraren su. Umma ce, babar Amina tazo ta fito dani tace su daina tsokana ta, ta shiga dani har dakina itama ta sakani a gaba da nasiha, Amina har da yimin video wai sai ta nuna wa Sultan dan yasan cewa ashe duk I love you din na karya ne bai kai zuci ba. Ina daukan waya ta naga 13 missed calls daga sultan, a raina nace "wasa ma kenan, kai da kaji muryata kuma ai sai dai acan" .

Sallah kadai na samu nayi dan abinci ma kasa saka shi nayi a bakina, aunty zaliha ce ta saka ni a gaba da kyar na iya cin loma biyar nace na koshi. Mommy ta shigo ta kawo min magani na tace in sha, na karba ba musu na shanye. Idon Mommy kawai na kalla nasan itama kukan ta gama. Ina jin Hafsat tana kiran mutane su zo su ga hoton ango a waya, suna ta yaba kyan da yayi amma ni kam na kasa kalla. Daga baya naji suna waya da Hafsat tana gaya masa wai gani nan ina ta kuka, ta miko min naki karba sai ta saka shi a hands free "kiyi hakuri amaryata ki daina kuka, gani nan akan hanya, ina shigowa abuja zan zo in rarrasheki da kaina. Kuma duk wanda ya tsokane ki ki rubuta min sunan sa ni kadai nasan abinda zanyi masa" daga jin yadda yake maganar kasan shima dariyar yake yi, na karbe wayar na kashe, ni banga abin dariya ba dan ina kuka anyi min aure. Mai gyaran jiki na ta hada min ruwa tace inje in shiga, na shiga na kwanta ina lissafin shikenan fa, yau na taka wani stage na daban a rayuwaya, yau wani nauyi babba ya hau kaina, shi kenan na zama matar aure. Bayan an gama yi min wankan na shafe jikina da wannan man da ta bani na musamman, ta hada min turaren da nake tsugunnawa akai shima nayi. Muma gama wa da mai gyaran jiki mai kyalliya tazo muka fara, na gaya mata yau bana son heavy make up light zatayi min dan haka ba mu dade ba ta gama min. Yau shadda na saka fara tas da bakin aiki a jiki, komai da na saka fari ne. Irin shigar da Sultan yayi kenan ta daurin aure. Da dankwalin shaddar aka yi min gwaggwaro. Mommy ta shigo da wani dan karamin box a hannunta ta fito da complete set din sarkar gold, da kanta ta saka min, nan na kara fitowa tar dani. Ina yin sallar la'asar aka saka farin mayafina aka rufe ni ruf har fuska aka saukar dani kasa zuwa dakin Hafsat, karfe biyar 'yan daukan amarya suka zo, ai ina jin zuwansu na kankame Mommy na fara sabon kuka, itama biye min tayi muka yi ta rusa kukan mu, sai da wata kanwar daada tazo sannan ta kama yi wa Mommy fada. Yaya ce da kanta tazo dauka na, inna ce ta bayar dani ta danka hannuna a hannun yaya, ni dai idona a rufe, ji nayi an lullube ni da wani abu mai kauri yana wani kamshi na musamman, ashe alkyabba ce. Babu abinda nake ji sai guda ta ko ina. Haka ina ji ina gani aka fita dani daga gidan mu aka sakani a mota, da jiniya da komai aka tafi dani palace. Yaya da inna su suka saka ni a tsakiya. Tun da nake ban taba shiga palace ba sai yau. Kuma yau din ma fuska ta a rufe take dan haka babu abinda na gani.

Cikin gida aka fara shiga dani direct part din Hajiya. Ina jin muryoyin su Fa'iza suna tsokana ta amma ban kula su ba. Da fara'a da komai Hajiya ta tarye mu. Duk da cewa fuska ta a rufe take amma na fahimci shima gidan a cike yake da mutane. A nan Umma kuma ta bawa Hajiya amana ta ita kuma tace ta karba. Sai da akayi sallar magrib sannan aka tafi dani gidana. Tafiyar kusan unguwa guda ce kafin gidan. Tun daga waje mutane suke kiran masha Allah, inna ta sakani nayi bismillah sannan na shiga da kafar dama. Direct cikin bedroom dina aka wuce dani, gidan gaba daya kamshi yake yi saboda tun safe Mommy ta aiko aka kara gyarashi aka saka fresheners a ko ina. Ko ina an bude a gidan saboda mutane su gani, part din Sultan ne kawai a rufe. A hankali mutane suka fara watsewa, iyayena duk suka zo sukayi min sallama suka tafi, daga karshe ya rage daga ni dai kawayena wadanda zasu zauna saboda partyn da za'ayi in an jima wanda kuma zai yi serving a matsayin siyan baki.
Chapter 116 · 0% Book details