Sashe 101
Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin tsananin mamaki nace "what? Waye ya gaya maka haka" gani nayi yana kallon office din kamar me neman wani abu, nima na taya shi dubawa, sai a lokacin na tuna cewa tare da Amira muka shigo office din, babu ita babi alamar ta. A zuciye naga yayi hanyar kofa yana cewa "I will murder that bitch" jiri naji yana kokarin dibana, nayi sauri na zauna a kujera, nasan da za'a gwada jini na a lokacin za'a tarar ya hau, Amira, why? Me yasa zata yi min haka? I trusted her. Babu abinda banyi mata ba kuma babu abinda ba zan iya yi mata ba. Ina zaune rike da kaina Ibrahim ya dawo cikin office din idonsa kamar garwashin wuta, ya fara zagaye office din da alama jinin yarabawan ne ya motsa. "She told me lokacin da Daddy ya san alakar mu ya hada ki aure da wani cousin dinki a 'yalleman, she even showed me the wedding invitation, after a year ta turomin message tace kin haihu" sosai kaina yake juyawa dan sama sama nake jin maganar sa, lokaci daya kuma naji wani realisations yayi hitting dina, Hafsat, oh dear God no, not Hafsat, i can take betrayal from Amira but not from Hafsat, na juyo na kalleshi nace "kaima ance min kayi aure, ka auri Efi" ya tsaya a zagayen da yake yi, yazo ya tsugunna a gaba na, expression din fuskarsa na kalla naji wani dadi a raina, at least Hafsat gaskiya ta fada. Yace "yes, na auri efi shekara daya bayan rabuwar mu, amma ban karbi auren ta ba sai bayan da na samu labarin kinyi aure tukunna..." Na katse shi nace "and kawai daga Amira ta gaya maka nayi aure you just believe her, ba zaka bincika ba, ask around, ba zaka kira ni ba kayi confirming daga baki na ba" na danyi shiru ina controlling temper dina, sannan na cigaba "you switched off your phone, you didn't even call me, you just left without a second look" Ya mike tsaye ya koma ya zauna akan kujerar da take kallon tawa, har yanzu bai ce komai ba, na dago kai na kalleshi muka hada ido na mayar da ido na kasa, a hankali naji yace "kin chanza sosai, you look more beautiful, more beautiful than I kept imagining you would be" a hankali nima nace "it doesn't matter, abinda nake so kawai in sani shine 'why?' Dama tun farko bada gaske kake sona ba ko kuma bayan ka tafi ne ka chanza ra'ayi?" Ya kara jawo kujerar sa kusa da tawa yace "Maimunatu kema kinsan amsarki, I love You, more than life itself. Ki tsaya ki saurari labarin abinda ya faru bayan tafiya ta, ina tabbatar miki da cewa zaki yadda cewa it hurt me more than it hurts you. I was fooled by your friend, totally fooled" na sake dago ido ina kallon rinannun idanunsa da suke kaina. Nace "OK. Ina jinka, tell me, what happened" "Bayan na bar gidan ku a ranar nan, na koma makaranta, ina zuwa na kashe wayata na ajiye saboda nasan zaki kira ni, ni kuma a lokacin gani nake yi as long as ina jin muryar ki I cannot stay away from you. I thought i was strong, na dauka zan iya zama babu ke har sai na samu abinda nake nema, har sai nasan na isa in zo in nemi auren ki. I had your number in my memory, dan haka plan dina shine duk sanda naga cewa it's OK to return sai in kira ki. Ranar sam banyi bacci ba, washegari na tashi da rashin lafiyar da har sai da aka kwantar dani a clinic din school. Sati da daya ina jinya sannan na dan samu sauki nace su sallame ni, suna sallamata na shiga office din PC na bata takarda ta ta barin aiki, bana son duk sanda na tashi dawowa neman aurenki ya zamanyo ina jingine da babanki ne. Kayan da suke gidana duk na hada na sayar na dau jakar kayana na fita daga makarantar, gidanku na fara zuwa na bada sakon CD a gurin mai gadi sannan na wuce tasha, .nadabazan iya misalta miki yadda nake jin raina ba a lokacin maimunatu, ina jin haushinki a lokacin sabida kin gaya min gaskiya da kika yi kuma ina jin wani irin sanki a raina, sannan ga alhinin rabuwa dake kuma, ji nake kamar na chire wani bari na jikina na ajiye. I was tempted to call you then, na dauko waya ta na saka sim na kunna, sai kuma na sake kashewa na cire sim din na jefa shi ta window din motar. Kafin muje ibadan zazzabi ya sake rufe ni, da muka je sai mai motar ne ya karbi number din baba a wajena ya kira ya gaya musu halin da nake ciki, nan suka zo suka dauke ni sai asibiti, na jima shima ina rashin lafiya a can, hatta mama bata san abinda yake damuna ba ballantana su Hadiza, na gaya musu na ajiye aikina na Abuja, kawai dai sun fahimci cewa it has something to do with you. Bayan na samu lafiya an sallamoni sai na yanke shawarar tafiya Lagos, da akwai wani uncle dina a can wanda kudin inheritance din mu yake hannunsa yana business dashi, mama taso ace na zauna a ibadan na nemi wani aikin amma naki, gani nake aikin government babu abinda zai kawo min. Ina zuwa lagos uncle dina ya fara koyamin harkar business, cikin 'yan watanni na koya sosai, ya dauki kudaden mu gaba daya ya bani na fara nawa daban. Duk abinda nake yi kowacce rana, kowanne hour, kowanne minute kowanne second kina cikin raina maimunatu. A lokacin na fara trying kiran number dinki da sabuwar number ta, at least duk da cewa ina ganin lokacin dawowata bai yi ba amma ina so in san ya kike, amma ga mamakina your phone was switched off, kullum na kira a kashe, bani da number din kowa kuma a gidan ku sai taki. Tun a sannan na fara zama very frustrated. A haka har shekara ta kusa ta zagayo. Ban wani tara kudin kirki ba amma bazan iya jure zama babu ke ba, a dole na fara shirin tahowa Abuja in neme ki. Kamar hadin baki, ina zuwa ibadan baba ya shigar min da maganar auren Efi, a take nace masa a'a, wannan ba karamin bata ran mama yayi ba, saboda bata taba zaton zan iya cewa da baba a'a ba, tunda ban taba ce masa a'a ba. Ta fara fada baba yace a tambaye ni uzuri na, nan na gaya masa maganar ki, na nuna masa sosai irin yadda nake sonki, shi kuma ya goya min baya yace inzo abuja muyi magana da daddy in ya amince sai inzo in fada su kuma sai suje ayi maganar manya. Washegarin da muka yi maganar dashi na taho Abuja, har a lokacin wayarki bata shiga. Nazo unguwarku naga gidan ku babu alamar movement kamar wancan zuwam nawa, bana son wulakancin securities din ku dan haka na tsallaka gidan opposite dinku na tambayi me gadin kuna nan kuwa? Sai yace min ai kun tashi daga kasar ma gaba daya, sosai hankali na ya tashi, sai a lokacin na fahimci dalilin da yasa wayarku bata shiga. Bansan a gurin wa zan samu labarinki ba ballantana contact dinki. Na tuna da kawarki Amira itama a abuja take da zama kuma nasan tabbas zan samu labarinki a gurinta. Na tafi tsohuwar makarantar ku gurin principal na roke ta ta nemo min file din Amira, a ciki na samu address din gidan su, ina zuwa gidan su na aika a kirata aka cemin ta tafi makaranta, anan na zauna nayi ta jiranta har magrib sannan ta dawo. Sosai tayi mamakin ganina a kofar gidan su, kuma tayi murna sosai. Sai yanzu na fahimci dalilin murnar ta, ta dauka gurinta naje, ni na manta ma da cewa tana da wani feelings for me, na dauka tunda na gaya mata baki da baki cewa bana sonta shikenan magana zata wuce. Bayan mun gaisa ta kawo min ruwa nasha sai na gabatar mata da abinda ya kawo ni gurinta, cewa ina neman hanyar da zan same ki ne ko kuma number dinki. Abinda tace min shine 'au baka sani ba? Na dauka ta gaya maka ai' nace mata 'me fa?' Tace 'zancen auren ta mana, ai ranar da kaje gidan su Daddy n ta ya ganka, kana tafiya ya tambayeta waye kai ta gaya masa yace babu ita babu kai, shi ba zai bawa bayarabe 'yarsa ba, data takura ta daina cin abinci ta daina yiwa kowa magana sai ya dauke ta ya kaita 'yalleman, bata fi two weeks acan ba aka hada auren ta da wani cousin dinta a can' ji nayi tamkar ta zuba min fetur a jiki na ta kyatta a shana. She is your best friend, how can I not trust her words? Besides, nasan dama ba kowanne bafulatani ne zai yadda ya bawa bayarabe auren 'yarsa ba. Ganin irin yadda hankali na ya tashi ne yasa ta fara lallashina, tace in ban yarda ba zata kawo min sample din IV daurin aurenki kafin in bar gari. Ta gaya min cewa duk 'yan gidan ku suna England yanxu ke kuma kina 'yalleman. Anan ta karbi number ta da niyyar zata kawo min IV din. Daga gidan su Amira da kyar na samu taxi ta kaini hotel na kwana, ranar nayi kukan da ban taba yin irinsa ba a rayuwata, na tausaya miki na tausayawa kaina saboda ina ganin soyayyata ce ta jawo miki aka miki auren dole aka kaiki kauye aka katse miki karatun ki, alhalin ga 'yaruwarki can a England tana karatun ta. Washegari da ciwo na tashi dan ko fitowa ban iya yi ba har Amira tazo da yamma ta kawo min IV din, naga sunan ki da sunan wani Abdulaziz a matsayin mijin. Ganin ina kokarin in mutar mata a hannu yasa ta kira mai taxi suka kaini asibiti, a take aka kwantar dani dan sosai nake neman rasa numfashina. Kwana na uka a kwance Amira tana ta dawainiya dani, ranar dana warke nayi mata godiya nace zan tafi, amma dan Allah she should at least call