Sashe 48
Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Tunda muka shiga gida Amira take min bala'i. Ni dai kawai dariya nake mata. "Yanzu kinsan kuwa duk wanda ya ganki a motar sultan irin kallon da zaiyi miki? Kin san ma kuwa waye Sultan? Mutumin nan ko magana bai kamata ace ta hada ku dashi ba ballantana har ki shiga motar sa. Yanzu ma tukunna, ina kukaje da kuka dade haka baku karaso ba?" Na harare ta nace "gidan sa ya kaini. Ina ruwanki da inda muka je?" Muka shiga dakin mamanta muka gaisheta sannan muka koma dakin ta. Nan fa ta saka ni a gaba da nasiha, ita lallai gani take shiga motar Sultan din da nayi tamkar wani katon zunubi na aikata. Tace "Yanzu Allah ne kadai yasan irin maganganun da ya gaya miki, duk sai yaje ya hure miki kunne anzo an kasa gane kanki. Ki rufa mana asiri Moon ki rabu da Sultan dinnan" Nace "Saboda me?" Tace "saboda me? Yanzu har tambaya kike yi saboda me? Just look at him zaki gane saboda me. He is a criminal for God's sake. He is spoilt rotten. A gangster. A rogue. A drunk. Duk wadannan dalilan basu ishe ki ba?" Murmushi kawai nake yi ina kallon yadda ta dage tana ta bayani. Nace "yanzu in tambayeki, ya akayi kika san Sultan is a drunk?" Tace "duk garinnan waye bai san dan shaye2 bane? sau nawa ana ganinsa yana yawo a gari a buge" nace "yanzu ke kin taba ganinsa yana shan giya?" Tace "ni ban taba ganin sa ba amma.. " na daga mata hannu nace "amma me? Annabi da kansa ya hana yada jita jita, abinda baka tabbatar ba kar ka fada musamman akan alfasha" Amira ta saki baki tana kallona kamar zata yi kuka tace "are you truly depending him?" Nace "ba wai goyon bayan Sultan nake yi ba, ina goyon bayan gaskiya ne" ta sake matsowa kusa dani desperately tace "yanzu ki duba kiga irin abokansa, ki kalli wannan shegen Amir din ki gani. Kin san kuwa sunan gang dinsu? Gang Bang they call themselves. Gang din 'ya'yan manya ne wadanda suka fi karfin karfin iyayensu. Abuja, kano, kaduna, legos da duk sauran manyan states na Nigeria an sansu, Sultan da Amir sune 'yan Abuja. Moon duk wanda yake cikin gang dinnan is a known criminal kawai dai dan babu yadda za'ayi dasu ne shi yasa. Kinsan kuwa kwanan baya suka yi gang raping wata yarinya a Nassarawa state?" Ji nayi tamkar ta chaka min mashi a kirjina, amma na daure nace "ke a ina kikaji wannan labarin?" Ta daga kafada tace "a radio, a television, a social media, a newspaper ko ina zancen akeyi" nace "ita yarinyarce tace su su kayi raping dinta" tace "eh mana, anyi hira da ita har a gidan radio" na sake cewa "ita yarinyar ce tace da wane da wane da Sultan suka yi raping dinta?" Tace "just because his name wasn't mentioned doesn't mean he didn't do it" na girgiza kai na kawai ina kallonta, tace "Moon kar ki bari son da kike masa ya rufe miki ido ki kasa ganin gaskiya. Dududu yaushe kika sanshi da har zaki tunanin kinsan shi fiye da sauran jama'a? Duk abinda nake gaya miki kamar yana shiga ta wannan kunnen ne yana fita ta wancan. Already har ya riga ya hure miki kunne" ta mike a fusace ta dauko laptop dinta ta ajiye min agaba na tace "in baki yarda dani ba check for yourself, ki duba internet zaki fahimci waye Sultan" daga nan ta fice ta barni a dakin. Na jima ina kallon laptop din ina jimamin abinda bincike na zai gano min. Can na dauka na kunna direct na shiga goggle, nayi typing sultan sai naga amsoshi da yawa wadanda ba sa dangantaka da abinda nake nema. Na goge nayi typing sultan Abuja prince. Nan da nan kuwa naga an watso min hotunan Sultan, wadansu a kasarnan wasu a kasar waje. Duk hotunan babu ko guda daya da yake da manyan kaya a jikin sa, babu kuma ko guda daya da yake tare da babansa. Nayi typing criminal record dinsa, nan ma naga rubutu da hotuna da yawa, can ya daki wancan, nan yayi trashing wancan shagon, yayi causing traffic jam, duk dai labarin daya ne. Nayi shiru ina karanta labaran daya bayan daya, sai wani tunani yazo min, duk cikin labaran banji ance yayi sata ba, banji fashi da makami ba, banji kisan kai ba kuma banji labarin yarinyar ta Amira ta fada ba, asali ma duk hotu an nasa babu inda na ganshi da mace, duk tare da maza ne masu shiga irin tasa. Wani hotonsa ne ya dauki hankali na nayi zooming, Sultan ne fuskarsa dauke da murmushi, rike a hannunsa kwalbar giya ce a daga ta alamar cheers. Na runtse idona ina jin zafi a kirjina. So it's true, yana shan giya. Hawaye naji yana kokarin zubo min na yi sauri na mayar dashi. Nayi typing emir of Abuja, nan ma hotuna na gani ba adadi na mai martaba sarki kuma kusan duk hoton yana tare da second son dinsa Abbas, cikin kima da daraja da kwarjini irin na sarauta, mostly a gurin saukar karatu ko bude masallaci ko musabakar alqurani. Nayi zooming wani hoton mai martaba, kana ganinsa kasan shi ya haifi sultan, idonsu, girarsu da shape din fuskarsu iri daya. Na koma nayi searching prince Abbas, nayi ta bincike amma na kasa ganin single fault nasa, he is like a perfect son, komai tare suke yi da mai martaba, duk inda mai martaba zaije tare suke zuwa. Can naga wank hotonsu shida sultan a america gurin graduation din sultan na masters. Nayi shiru ina tunani, mutane criminals irin sultan basa karatu, most of them da wahala suke gama sec sch, amma sultan masters ne dashi kuma a babban field like architecture. What is happening? What am I missing? What are u sultan? A gurin manyan mutane da masu kudi shi criminal ne, a gurin talakawa da sauran marasa karfi shi hero ne. Wanne dalili ne zai saka mutumin kirki ya mayar da kansa mutumin banza a idon mutane. Har zan rufe laptop din sai na fasa nayi typing the gang bang. Ai kuwa naga rubutu sosai a kansu, Amira tayi gaskiya dan daga 'ya'yan tsofaffin shugabannin kasa sai 'ya'yan gwamnoni da manyan masu kudi, a cikin list din naga an rubuta "the drunk prince of abuja" duk da basu fada ba nasan sultan suke nufi. Na rufe laptop din na kwanta ina tunani. Why will Sultan want people to think he is a bad guy while in reality he is good, very good. Yau kusan 3 hours nayi a motar sa daga ni sai shi amma ko da wasa bai kai hannunsa jikina ba kuma baiyi min wata magana da zata nuna cewa dan iska bane. Dear God, what do I do now. Inanan a kwance Amira tazo ta kawo mana abinci har yanzu fushi take yi dani ita wai lallai naki jin maganar ta. Da kyar na samu na bata hakuri nace tayi min addu'a insha Allah komai zai warware. Muna nan muna ta hira har magrib sai Sultan ya kira ni yace min gashi nan zuwa, tun daga nan Amira ta cigaba da bata fuska, naje zanyi sallama da mama tace min "Maimunatu wai me yake damun kawarki ne?" Nace "mama me ya faru? " tace "sam taki kula samari ballantana har ayi maganar fitar da miji, ta gama degree dinta, tayi service, me kuma yayi saura? Ni na gaji da surutun da iyayenta suke yi min wallahi, ni babu miji ita babu miji amma ita sam bata damu ba, shi wanda naga tana nacewa da ya fara zuwa kamar gaske kuma yanzu shiru, ni ko waya ma yanzu banji suna ji ba, idan ba aurenta zai yi ba sai ta rabu dashi ta samu wani" na kalli Amira da alamarr tambaya saboda ban gane maganar da mama take yi ba, Amira ta daga kafada irin oho din nan, nan dai na bawa mama hakuri nace zamuyi maganar da Amira. Muna fita na tambayeta "wanene mama take magana akansa" ta dauke kai tace "nima bansani bafa, ita dai kawai ta damu sai nayi aure ne kuma ai shi aure lokaci ne, idan mijin baizo ba ni zan auri kaina ne?" Jikina ya bani da akwai abinda Amira take boyewa amma sai na rabu da ita, na san in tana son in sani zata gayamin ne da kanta.