Sashe 188
Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Episode Hundred : Not The End. One Year Later Daddy yayi retire daga ambassadorship, yace lokaci yayi kuma da ya kamata ya dawo Nigeria ya zauna cikin 'yan'uwa da abokan arzikin sa, tunda dai yasan ya tara da yawa, ya kafa kansa ya kafa 'ya'yansa, ko da ace bai tara dukiya ba 'ya'yansa kadai sun isa su rike shi zuwa karshen rayuwarsa. Yaya Walid yana aiki a kamfanin hakar man fetur na SHELL a matsayin engineer, sosai yake samun kudi kuma da yake shi mai nutsuwa ne sosai da tattali, nan da nan ya fara shiga layin wadanda za'a kira da masu kudi. Yaya Habeeb yana aikin banki, duk da cewa shi mai yawan kashe kudi ne amma dai dai gwargwado yana samun cigaba shima. Ni kam da ni da Hafsat medical doctors ne, duk da dai har yanzu babu wanda ya fara aiki a cikin mu amma mazajen mu sun ishe mu duk bukatun mu. Faruk ya gama service dinsa ya koma masters, tun kafin ya tafi yace a nema masa auren Huda amma Daddy yace sai ya gama karatu ya samu aikin yi sannan za'a yi masa aure, an dai shigar da maganar manya sun sani. Daddy yana dawowa Nigeria ya aika 'yalleman aka daukk inna da Hajja ya dawo dasu Abuja su zauna tare dashi, tunda 'yalleman din kusan babu kowa sai uncle rufa'i, shi kuma ba mazauni bane sosai. Tunda labarin retirement din Daddy ya bazu a Nigeria, nan da nan aka fara aiko masa da offer din aiki, government, ministries, companies amma duk yaki karba yace hutawa yake so yayi. Amma bai dade a gida ba kuma sai yaji zaman gidan ya ishe shi, tunda babu kowa a gidan sai su inna da 'yan aiki, Mommy har yanzu tana aikin ta, dan haka rana daya Daddy yace ya karbi offer din da university of Abuja ta aiko masa akan ya zama next VC idan tenure din wanda yake kai ta kare. Dama shi Daddy harkar siyasa ce baya so, amma yana ganin as a VC zai taimakawa kasarsa without getting involved in politics. Bikin su Ya walid yana da wata goma Zainab da Fadila, wadanda yanzu sun zama kawaye sosai, suka haihu kusan a tare, Zainab ce ta fara haihuwar baby girl aka saka mata Mommy, ranar sunan ta Fadila ta haifi Daddy, dan haka yaran suka tashi kamar tagwaye, small Mommy da small Daddy. Hafsat ta juye ta sake dauka. Lol. Ta haifi danta namiji watanni biyu bayan haihuwar Al'ameen. Mukaje England muka sha suna, yaro yaci sunan baban Zayed. AbdulMalik, muna kiransa da Ayaan. Watannin Ayaan biyar a duniya Hafsat ta kira ni tace min wani cikin ne da ita, nace "kai Hafsat, wannan ke ai har kinfi Mommy ma" tace "ai dama haka ake yi, idan ka koyi abu a gurin mutum sai kazo ka fishi iyawa kuma" mukayi dariya, tunda dai duk ita da yaranta lafiya lau suke to babu wata matsala. Anyi bikin Amira da Mahdi, mun je kano munsha hidima. Duk da dai Sultan ya hana ni kwana yace Al'ameen yayi kankanta da shiga biki, ni kuwa nasan bata Al'ameen yake ba, ta kansa yake, dan Sultan yana nan yadda kuka san shi babu abinda ya ragu sai ma ince karuwa yayi. Mahdi ya samu aiki a asibitin malam Aminu kano. Last wayar da mukayi da Amira itama ta gayamin ta kamu. Suna zamansu lafiya lau from all indications. Ibrahim da Jewel dinsa Amina kam soyayya sai abinda ya kara gaba. Dan ko ziyara mutum yaje gidan su sai ya fahimci suna kaunar junan su. Maman Ibrahim ma ta dauki son duniya ta dora akan Amina dan tana ganin itace sanadiyyar dai daituwar dan ta. Ita kuma Amina ta rike little Moon tamkar ita ta haife ta, in baka sani bama ba zaka ce ba ita ta haife ta din ba. Kullum kaga Ibrahim zaka ganshi cikin farin ciki, alamar cewa hankalinsa a kwance yake. Sosai suke zumunci shi da sultan, dan wani lokacin ma har yazo gidan mu ya tafi bana sani, sai daga baya sannan sultan ya gaya min. Sai dai kuma har yau, duk ranar da muka hadu da Ibrahim muka gaisa sai naga kishi a idon sultan, sai dai baya nuna wa har wasu su gane. I guess some things will never change. An samu karuwa a gidan Amir shima. An samu namiji wanda a take Amir ya saka masa sunan Sultan. Abubakar Sadiq Abdallah. Kuma ake kiransa da Sultan. Sultan yaji dadi sosai amma sai ya bata fuska yace "ko kara ma babu, sultan zaku ce masa kamar wani sa'an ku? Ina lefin ma ku ringa ce masa Yaya?" A raina nace 'ho, sultan akwai son girma'. Har yanzu amir bai samu iyayensa ba, kuma dama bawai tayar da hankalinsa yayi yana neman su ba, yace "if it is meant to be, then it will be" gwara ya zauna ya gina rayuwarsa tare da mutanen da yake dasu, wadanda ya tabbatar suna kaunarsa akan yaje ya bata lokacin sa gurin neman wadanda ba lallai ne suna son sa ba. Munir tun rasuwar Baffa ba karamin girgiza shi mutuwar tayi ba, kasancewar tunda akayi masa takunkumi a 'yalleman suke tare da Baffa suna kara shakuwa, mutuwar Baffa sai ta nunawa Munir cewa itafa duniya ba matabbata bace ba, kana cikin shagalinka za'a iya zuwa a zare ranka ba tare da ka tuba ba. Wannan ya saka shi ya kara nutsuwa, ya rungumi matarsa ya kuma rungimi aikinsa. Kowa a dangi yaji dadin chanjin munir, wannan ya saka Hajja tace to tunda dama neme-nemen mata ne ya lalata shi, to gwara a kara masa wata matar dan ya kara nutsuwa. Ai kuwa a take uncle rufa'i ya bashi Rufaida kanwar Amina. Munir baki har kunne saboda murna dan dama ya taba cewa yana sonta ta wulakanta shi saboda halinsa, amma tunda yanzu ya shiryu itama ba'a wani sha wahalar shawo kanta ba tace ta yarda. Ummee da Takawa ana nan ana bude sabon page na rayuwa, dan idan ina gurin Ummee Takawa ya shigo tashi nake yi in fita, saboda kunya yake sakani ina ji shi kuma babu ruwansa, daga dukkan alamu rashin kunyar sultan ta gado ce. Sultan da Takawa are very much alike, saboda idan suna wani abin tamkar mutum daya ne da kamanni biyu. Ummee ta sayar da business dinta kaf na Riyadh, dukkan kudin ta zubasu a account din sultan. A take Takawa ya sake bata wani jarin ta fara sabon business a Nigeria, nan da nan aka hada mata connection da 'yan kasuwa take shigo musu da kaya daga kasashen waje. Sultan yace "amma Ummee wannan karon ba sunana kika saka ba ko?" Tace "sunan little love na saka" yace "Ummee I don't need money kin sani, in dai ta nine kiyi hutawarki" ta harare shi tace "dama kaine little love din?" Sultan ya tsaya saroro yana kallonta yace "OK. Kun fi kusa ke da shi". Hajiya tun tana saka ran Takawa zai mayar da ita har ta fara kosawa. Shi kam har manta wa ma yake yi da ita a duniya, dan in dai ba zuwa tayi gaishe shi ba baya ma tunawa da ita, duk sanda tazo gaishe shi kuwa sai ya hade rai sosai sannan yake amsa mata, dan baya son ma taga fuska ballantana ta kawomasa wata magana. Da Hajiya taga babu fuska sai ta fara bin manyan su tane rokon a roka mata shi ya mayar da ita. Yaya ta kira su gaba daya suka zauna a gabanta, tana yiwa Takawa maganar ce mata yayi shi ba zai iya mayar da Hajiya ba, tace "saboda me? Saboda kai baka yafiya? Baka son kaima Allah ya yafe maka?" Yace "ai na yafe mata, da ban yafe mata ba da tuni na koreta daga gidana ita da shegen danta. Ba zan mayar da ita ba saboda ina gudun sabawa Allah. Allah yace duk wanda yake da hali to ya auri mata biyu zuwa hudu in har yasan zai iyayin adalci a tsakanin su. Ni nasan bazan iya adalci a tsakanin khairat da wata mace ba, ba Zuwaira kadai ba, dan haka bazan iya mayar da ita ba. Zaman da muka yi da ita a da ma da ace ina da iko dana goge shi daga kwakwalwata na taina tunawa" jin haka yasa Hajiya tace ita kam ba zata iya zama babu miji ba, dan haka tunda ba zai mayar da ita ba to zata fita ta sami wani mijin tayi aurenta, Takawa yace Allah ya raka taki gona, amma kar ta saka ran tafiya da ko daya daga cikin 'ya'yansa, sai dai in nata dan zata dauka to bismillah. Haka kuwa akayi, Hajiya ta sayi gida da kudinta a wajen palace ta koma can da zama, amma kuma mijin aure yaki samuwa, matsalar shine da wahala sarki ya saki mace wani kuma ya aura. Ummee ta sami Takawa da lallami tace tunda shi yace ba zai mayar da Hajiya ba to dan Allah ya samo mata mijin aure da kansa, saboda gudun kar azo a kuma yin wani abin kunyar, tunda har ta fada da bakinta cewa ba zaya iya zama babu miji ba, albarkacin 'ya'yanta, tunda komai tayi dole za'a ce uwar 'ya'yansa ce tayi. Babu jimawa Takawa ya samo mata miji, wani tsohon abokinsa da suka yi secondary school tare, mazaunin garin kauran namoda ta jihar zamfara. Hajiya akayi sabon aure aka tare da ango. Su saratu suka fara nuna rashin jin dadin su akan sabon auren da mahaifiyarsu tayi, Takawa yana ganin haka yace suma duk su fito da mazaje yayi musu aure, dama kowacce ashe da nata saurayin suna tsoron fada ne kar ace sunyi laifi, dan haka babu jimawa muka sha shagalin bikinsu muka kaisu dakunan su. Daya Kaduna daya kuma anan Abuja. Abbas kam ko daga kai bai yi ba akan sabon auren Hajiya, karatun sa kawai ya saka a gaba yana gina sabuwar rayuwarsa. Kamar yadda mukayi shawara da sultan a Riyadh haka akayi. Sultan ya gina sabuwar obrphanage, amma wannan karon a Kano ya gina ta, yace next time kuma a Lagos zaiyi tunda sune manyan buranen Nigeria. Ya kashe kudi sosai wajen ginin da furnishings. Sannan yazo ya dauki