← Book details Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 161 OF 190

Sashe 161

Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yana maganar yana zagaye dakin, nace "bata yi wadansu yayan ba, in fact vata kuma yin wani auren ba tun barinta Nigeria" ya tsaya da zagayen da yake yi ya kalle ni yace "then why didn't she come for me?" Na mika masa wayata nace "call her and ask her, ni bansani ba" ya karbi wayar ya ajiye a gefe, at least wannan karon ba'a fasa min waya ba. Na mike tsaye na karasa gabansa, na saka hannu biyu na riko fuskarsa nace "Sultan she has been crying tun ranar da muka yi waya da ita, ta gane abinda ya faru, ta gane kai ka kashe wayar saboda ba kason magana da ita, ta gane cewa fushi kakeyi da ita. Sultan mahaifiyar kace fa, kar ka bari ubangiji yayi fushi da kai akanta Sultan, ko ma menene tayi ya kamata ka saurare ta" bai ce min komai ba ya sauke idonsa kasa, amma nasan I got his attention, na jayo hannunsa muka dawo muka zauna akan kujera, yace "ni yanzu inna kira ta to me zance mata? I miss you zance mata ko me?" Nace "I miss you din ma is in order" yace "no, it's not, ban san taba ballantana inyi missing dinta" nace "then let's go to her. In baka san me zaka ce mata a waya ba in muka je ka ganta ido da ido am sure zaka san me zaka ce mata" ya girgiza kansa stubbornly, ba tare da warning ba na hade bakin mu na fara kissing dinsa da zafi zafi, nan da nan kuwa ya dauki zafi, dama abinda yake ta nema ne ido rufe naki in bashi, yau sai gashi har gida, nan na fara sarrafa shi son raina, duk abinda nasan yana so shi nayi masa double, na ruda shi sosai na rikita masa tunanin sa, duk wani stubbornness dinsa sai da na cire masa shi ya dawo a tafin hannuna, a nan kan kujerar muka sauke hajar mu. Ana gamawa Sultan yace shi kari yake so, na bata rai na juya masa baya, ya jawo ni ya kwantar a kirjinsa yayi ajjiyar zuciya yace "why do you care about her? Baki santa ba, baki san halinta ba, for all we know maybe tana zuwa gidan nan ke ce mutum ta farko da zata ce bata so" nace "maybe, maybe not. Maybe tana zuwa gidan nan son da zata yi min sai yafi wanda zata yi maka, we will never find out idan bamu je ba" ya bata fuska kamar zai yi kuka yace "please Love I really don't want to go" nace "then let me go. In kai ba zaka iya zuwa ba ni ka barni inje, Hafsat da zayed suna can, at least in naje muka yi magana da ita zan samo maka duk amsar tambayoyin ka, daga nan sai ka yanke shawarar me zakayi next" yayi shiru yana tunani, ba dan hannunsa da yake shafa cikina ba zan iya cewa bacci yake yi saboda dadewar da yayi a haka. Can yayi magana "zaki je next week, zakiyi three days a can, a gurin su Hafsat zaki sauka saboda bana son a wulakanta min ke, in na fita gobe zan fara processing tafiyar taki" da sauri na mike zaune ina rawar murna, na manta ma babu kaya a jikina sai daga baya na tuna na koma na dunkule a jikinsa, yana dariya ya dago ni yace "amma da sharadi, daga yau duk abinda nake so shi za'a ke yimin, ko yaushe ne kuma ko a ina ne, in ba haka ba an fasa tafiyar" nace "yes sir, an gama" ya mike tsaye ya mikar dani yace "yanzu sai muje daki mu cigaba daga inda muka tsaya". Washegari duk da farin ciki muka tashi, ni ina murnar na shawo kan sultan shi kuma yana murnar mun dawo rayuwar mu dai dai, dan haka ranar da kyar ya fita office. Bayan mun kammala duk abubuwan al'ada na gyaran gida muka shiga kitchen muna kokarin dora abincin yana, sai ga yarinya tazo tace min wai nayi bakuwa, na leka palon naga Amira na rike kugu nace " au dama ke ce bakuwar zaki wani zauna a palo? Ki tashi ki cire wannan mayafin ki taho kitchen" tana dariya ta ajiye mayafin ta ta taho, a kitchen din muka gaisa sosai sannan ta gaisa da Asma'u da sauran yarana, na lura tayi sanyi sosai kuma naji ina tausayinta har cikin raina. Sai da muka kusa kammala aikin sannan muka bar su Asma'u muka dawo palo muka zauna, muka fara hira, mostly hirar da yadda kawancen mu yake, da yadda tayi ta bani shawara akan sultan ni kuma na rufe idona naki dauka, wani gurin muyi dariya wani kuma muyi jimami, ina sane na sako mata zancen Ibrahim da labarin yanzu Amina yake nema, ina maganar ina kallon fuskarta inga yadda zata dauki maganar amma sai naga babu wani chanji a fuskarta sai ma alamar tana taya Amina murna. Muna nan zaune muka ji sallama, Amira tayi saurin daukan mayafinta ta yafa, a raina nace 'har yanzu ustazancin yana nan kenan' Abbas ne ya shigo cin abinci, da yake shima yanzu anan yake cin abinci tunda har yanzu bai huce da Hajiya ba. Ina sane nace Amira tayi serving dinsa, ta harare ni na langwabar da kai na nuna mata cikina, ta tashi ta bishi dining tana serving dinsa, ina jiyo maganganun su, dan Abbas akwai surutu kamar fa'iza, saratu ce mai shiru shiru dinsu. Bayan ta gama ta dawo gurina muka cigaba da hirar mu, sam ban bata labarin komai da yake wakana a rayuwar mu da sultan ba saboda ance once biting twice shy, bayan Abbas ya tafi muma muka je muka ci abinci tare sannan ta tafi gida. Bata jima da tafiya ba sai ga Abbas ya dawo, ina ganinsa nace a raina tarko na yayi kamu kenan, yazo ya zauna yana shafa kai yace "babbar yaya wacece dazu tazo gidan nan?" Na hade rai amma cikin wasa nace "ina ruwanka da ita?" Yace "please ki dan shigar dani mana" na wara hannuna nace "a nawa? Kasan ni bana aikin banza" yace "zanyi ta yi miki addu'ah kullum idan nayi sallah. Please" nace "ni ba zan shigar da kai ba, zan dai baka number dinta ka je ka shigar da kanka" yayi godiya ya karbi number din ya fita. Asma'u tana daga kitchen ta leko tace "dama nasan za'a rina, wai an saci zanin mahaukaciya" muka yi dariya tare. Na kira Hafsat na gaya mata an bar ni zuwa, nace ta gaya wa Ummee cewa zanzo amma ni kadai, anan take gaya min cewa khairat ta hana ta komawa gidan su zayed tun da tasan dangantakata da ita, anan gidan yanzu take sai dai zayed yazo gurinta, tace min itama tana murnar zuwan nawa nan da sati daya. Satin da sauri yazo, tun kwana uku tafiya ta na fara hada kaya, sultan kam sai kumbura yake yi, kullum sai ya tsara min yadda tafiyar zata kasance, yace gurin Hafsat zan sauka, sau daya zanje gurin Ummee, in naga babu fuska kar in sake zuwa, ni dai to kawai nake ce masa amma ni na gama plan dina, ana gobe tafiyata naje gida na wuni gurin Mommy, Daddy dama baya nan lokacin, na gaya wa Mommy komai yadda ake ciki da kuma plan din da nayi, farko ta fahimta kuma ta yarda, sai kuma daga baya ta zama alarmed, "kin ga neman takawa dama suke yi suyi masa hukuncin sace musu 'yarsu da yayi, kar kije kuma su kama ki ke" nayi dariya nace "Mommy ba abinda zasu yi min, shekara talatin fa da yin abin, besides, gurin Hafsat zanje". Sai dare sultan yazo daukana, tun a mota yake cewa shi ya akayi ya bar ni wannan tafiyar ne, a ranar yadda muka ga dare haka muka ga rana, sultan yayi nadamar bari na yafi cikin charbi, sai kara jaddada min yake yi "three days kawai, babu kari, make sure wayarki a kunne take all the time, in kinga zasu daga miki kai ko su Hafsan ne ma ki rabu dasu kije ki kama hotel ki kwana da safe kiyi tahowar ki" ni dai sai to kawai nakr ce masa. Da safe saura kadan ya saka inyi missing plight kuma nasan yana sane, so yake in fasa tafiyar amma naki. Muna zuwa airport yace "ko dai ince na fasa barinki tafiyar nan ne?" Nace "nasan ma ba zaka fadi haka ba" yace "saboda me kika ce haka?" Nace "because you are a man of your words" ya girgiza kai kawai ya fito min da akwatina, har sai da aka fara cewa za'a rufe kofar jirgi sannan sultan ya sake ni na tafi. Ina shiga jirgin ina zama naji na fara missing dinsa, na dauko waya na kira shi nace "already missing you Darling" yace "then come down ki fasa tafiyar nan please" nace "no, na riga nayi niyyar, just pray for me" ya kashe wayar bai ce min komai ba. Wajan asr jirgin mu ya sauka a birnin Riyadh. Ina fita reception na hango Hafsat da Zayed suna jirana, na karasa da sauri na rungume Hafsat da naga ta kara kiba da kyau, jin dadi sosai ya bayyana a tare da ita, Zayed ya karbi akwatina yana cewa "welcome to my home town sister In-law, kin zama in-law dina ta two sides" muka yi dariya a tare. Muna shiga mota yace "gidan khaloo (Aunty) zamu je ko?" Nace masa "eh" ni dai duk ina feeling nervous, ban san ya zata karbe ni ba, what if sultan is right? What if ta wulakanta ni?" A hanya Hafsat take ce min wai khairat har fenti ta saka aka sakewa gidan ta na tara ta, wai yau tun safe take kitchen tana girki, ta rasa me zata dafa min, jiya kuma sam bata yi bacci ba saboda anticipation. Wannan maganar ce ta dan kwantar min da hankali. Tun daga gate din gidan nasan an ajiye dukiya a gidan nan. Ya hadu karshen haduwa, dan bazan iya tsayawa fassara haduwar sa ba. Ni dai kawai bin su Hafsat nake a baya da sakakken baki ina kallo, mun wuce palo sunfi uku sannan muka zo inda suka ce
Chapter 161 · 0% Book details