Sashe 105
Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Waya ta ta cigaba da ringing, na dauka ina kallon sunan sultan har ta katse, a cikin dictionary din sultan babu wata kalma wai ita giving up, he never gave up, yanzu kiran nan da ya ke yi min zai yi ta yi ne har sai na dauka ko kuma sai charging wayar ya kare. Na duba missed calls naga 23, amma 5 daga Mommy ne, sauran kuma nashi. Na fara tunanin abinda zance musu tunda duk cikin su babu wanda zan iya gayawa gaskiyar abinda ya faru yau. Mommy na fara kira, bugu daya ta dauka tace "ina kika shiga? Sai da nace muku fa kar ku kai magrib gashi har after seven baki dawo gida ba?" A nutse nace "Mommy mun dan samu matsala ne shagon, Amira ce suka dan samu sabani da wata cashier shine abin yayi delaying din mu, kuma nabar wayata a mota shi yasa ban san kuna ta kira na haka ba" ta dan rage fadan da take yi tace "to amma ai da ko wayar ita Amiran sai ki karba ki kira ki fada mana halin da kuke ciki, ni ba sai inzo da kaina ko in turo wani yaji matsalar da aka samu ba? Na kira wancan yaron ma yace shima yana ta kiranki baki dauka ba, duk kin tayar mana da hankali wallahi" na danyi murmushi a raina nace 'I love you too Mommy' nace "gani nan zuwa yanzu, zan kai Amira gida ne kawai in taho" da sauri tace "NO, duhu yayi kuma unguwar su Amira akwai nisa. Ku tsaya a inda kuke ki kira shi sai ya kai ki ya dawo dake gida" nace "yes mother" na kashe. Ina kashewa kiran Sultan yana shigowa, sai da nayi bismillah sannan na dauka, ina dauka yace "damn it, where have you been?" Cikin sanyin murya nace "am sorry Sultan, na manta waya ta ne a cikin mota, muna cikin wani supermarket ne kuma muka samu wata 'yar matsala, duk everything is Ok yanzu na kai Amira gida zan taho gida nima" kamar sun hada baki da Mommy yace "no, ki zauna bara inzo in dauko ki, dare yayi kuma hannunki bai yi kwari ba" nace "yes sir" ya sauke ajjiyar zuciyar da har sai da naji ta ta cikin wayar yace "you almost gave me a heart attack. Gaba na yana ta faduwa, kuma ina ta kiran wayarki tana ta ringing baki dauka ba. Please don't ever do this again in ba so kike zuciya ta ta buga in mutu ba" kalmar mutun da ya fada ce ta saka ni nayi murmushi nace "kar ka zama ragon maza mana, ko three hours fa ba muyi da waya ba" yace "anything can happen ai a cikin three hours din, kin san babu abinda ban aiyana a raina ba? Har sai da na hango ki a kasan tirela" nayi dariya, yanzu shikenan date din na mu ya wargaje? Har nayi musu waya nace suyi mana reserving table " nace "am sorry, in sha Allahu I will make it up to you. Yanzu Mommy tana can tana jirana in muka tafi fada zata yi. Insha Allahu zan lallabata ta sake bari na fita sai muje" ya shagwabe murya yace "baki ga kwalliyar da nayi miki ba fa" nayi murmushi nace "really?, show me, I want to see" yace "how?" Nace "kayi snapping picture ka turo min yanzu" yayi dariya yace "no, it is kind of special, in kina so ki gani sai dai kisan yadda zaki samar mana fita da wuri. Yanzu cirewa zanyi ma in boye" mukayi sallama yace gashi nan tahowa. Na tayar da mota, I have one stop to make, gidan su Amira. A hankali nake tuki sabida hasken fitulu da yake kashe min ido, addu'ah ta Allah ya kaini lafiya kuma Allah yasa kada Sultan ya riga ni zuwa. Cikin sa'a naje na tarar bai zo ba. Na debi kayan ta data siya ta bari a motar na shiga. Mama ce kadai a palo tana cin abinci, na gaishe ta ta amsa cikin kulawa tace "ya akayi kika zo da daddaren nan bayan dazu ta dawo daga gurinki itama?" Nace "wani sako na manta bance ta taho min dashi ba, kuma gobe zan yi amfani dashi" tace "da fatan dai ba ke kadai kika taho ba" nace "a'a kawo ni akayi" tace "kin ga yanzu tsayawarki ta shiga daki amma tunda ta dawo tana kwance a palon nan, tace bata jin dadine, ki shiga tana ciki" na mike na shiga dakin. Ina bude kofa ita kuma tana shigewa toilet. Na rufe kofar na karasa bakin toilet din na zauna a kasa. A hankali na fara magana "why? Me yasa kika yi min haka? Me tasa kika kasance me son kanki da yawa? Me nayi miki da nayi deserving wannan cin amanar daga gareki?" Shiru babu amsa. Na cigaba "ban taba koda jin labarin mutum marar imani marar tausayi irin ki ba. Nayi miki soyayya ta hakika amma ke ashe duk duniya babu wanda kika tsana irina. Amira babu abinda baki sani ba na wahalar da nasha akan soyayyar Ibrahim amma ashe ko sau daya baki taba tausaya min ba, maybe ma dariya kike min a bayan idona, Amira kina kallona a kan gadon asibiti amma ashe kina da maganin ciwo na kika boye kika hanani. To ki sani, ni babu abinda zan yi miki, na barki da Allah, kuma na tabbata Allah sai ya sakamin cin amana ta da kika yi. Kuma ki sani, kanki kika yiwa. Shi wanda kike claiming kina so shi yafi kowa wahala a cikin duk abinda ya faru, shine kuma still har yanzu a cikin wahalar bani ba. Kuma ki sani, duk da Allah ya kaddaro babu aure a tsakanina da Ibrahim to kema ba zaki same shi ba, saboda Ibrahim baya sonki kuma bai taba sonki ba, kuma ba zai taba sonki ba, especially yanzu daya gano gaskiyar makircin ki, he hates you and I hate you also. Kuma ina gargadinki da kiyi hankali da dosar inda yake saboda yace in dai ya ganki sai na lahira ya fiki jin dadi. Ina fatan zaki halarci bikina nan da kwana goma, ina so kizo saboda ki gani da idonki irin farin cikin da zan kasance a ciki, ina so ki gani da idonki irin sakayyar da Allah yayi min tun a duniya kafin muje can. Ga kayanki nan da kika bari a motar mijina" na mike tsaye, ina jiyo sheshshekar kukanta a cikin toilet na fice, nayi sallama da maman su na fita. Ina fita ana sauke Sultan a taxi. Da sauri ya fito yana bani hakurin ya dade, ya karbi key muka tafi. Muna daukan hanya, ga mamaki na sai naji yace "what's wrong?" Nace masa "me ka gani?" Yace "you look and sound different, kamar akwai wani abu a ranki" na tattaro dukkan charms dina nace "Hey, I am suppose to be the psychologist ba kai ba" yayi murmushi yace "kin san ance zama da madaukin kanwa" nace "to babu abinda yake damuna, kawai dai na gaji ne, kwana biyu bana fita kuma yau mun dan yi yawo, gashi ni nake driving" yace "sorry, kuma gaki dama da son jiki ko? Wannan duk sanda aka fara bikin nan bansan ya zaki ke yi ba" nayi dariya nace "ai wadansu events din skipping zan ringa yi, na gaya muku bana son big wedding kun dage sai anyi" yace "karki damu after the wedding zaki huta sosai, I will be there to help you rest" na harareshi duk da babi haske, dariyar mugunta yake min ban ce masa komai ba, yace "ya kika yi shiru?" Nace "oho maka, kai ka sani" Muna zuwa gida yace wai shi lallai sai dai mu zauna a mota muyi ta hira ba zan shiga gida ba, ni kuwa nasan dan dai gidan da akwai baki ne yasa har yanzu Mommy bata kuma kirana ba amma tana sane da cewa ban dawo ba. Da kyar na samu da lallabashi na gudu. Ina shiga bayan na gaishe da Mommy na tafi dakin Hafsat, kawai so nake in samu in gaya wa wani abin da yake raina ko na dan ji sanyi.