Sashe 149
Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yi suna jin su on top of the world, babu mai saka su babu mai hana su, babu abinda suke sai soyayya kamar su chinye junan su, sun zama Americans sosai. Sadiq ya nemi aiki da takardunsa kuma bai sha wahala ba ya samu, suka nemi gidan haya suka kama, khairat taso neman aiki itama amma sadiq ya hana yace albashinsa ya ishe su, su biyu kadai basu ajiye kowa ba. Wata daya da auren su khairat ta samu ciki, nan fa murna a gurinsu kamar me, Sadiq yana kallon cikin a matsayin hanyar komawarsa gida, idan babansa yaga cewa ya haihu da khairat ai dole ya hakura ya karbe ta da duk wani challenges din da auren nata zai taho dashi. Su biyu suka yi renon cikin su cike da soyayya da kulawa, da watan haihuwar khairat ya kama kuwa sadiq a jiye aikin sa yayi ya dawo gida gurinta yana kula da ita, hana ta yin komai yayi, komai shi yake yi mata, ko ya kuwa yaga ta dan bata fuska sai hankalinsa ya tashi. A haka labor ya zo mata, hankalin sadiq ya tashi sosai gani yake kamar mutuwa zatayi ballan tana da ta fara bashi wasiyyar ya kula da babyn su, ya kaishi gurin 'yan uwanta ya basu hakuri. Kusan akan chinyarsa ta haihu dan zama yayi dirshan akan gadon ya rungume ta yana yi mata alkawarin daha wannan haihuwar ba zai sake bari ta samu ciki ba saboda ba zai sake bari ta sha wannan wahalar ba. Ana haihuwar Sultan sadiq ya karbe shi ya rungume a kirjinsa, ko goge shi ba'a yi ba, dariya kawai yake yi saboda murna, shi a rayuwarsa bai taba ganin kyakykyawan yaro irin wannan ba, ya sunkuyo gurin khairat da ake gyarawa yace "look at our Little Love, He looks just like you". Nan fa suka ninka soyayyar da suke yiwa junan su suka dora akan Little Love dinsu wanda yaci sunan babansa, Abubakar, sukan zauna kawai su saka shi a gaba suna kallo, watan Sultan biyu a duniya Sadiq yaga cewa ya kamata su gwada zuwa gida suga yadda zata kasance, suka shirya amma basu kwashe kayansu ba saboda basu da tabbas din za'a karbe su a gidan. Sadiq ya shiga gida hannunsa na dama dauke da two months old Sultan, hannunsa na hagu kuma rike da Khairat. Da fushi sarki Abdullahi ya taho, yana zuwa Sadiq ya mika masa Sultan wanda a lokacin kwuiya ce dashi amma kawai sai akaga ya tafi gurin sarki yana bangala masa dariya yana ta ba masa fuska, Sarku Abdallah ji yayi ya kasa fadan kuma, niyyarsa yana zuwa ya kora su su koma inda suka fito amma sai ya kasa, wata soyayyar yaron yaji tana ratsa zuciyarsa. Kowa a gurin sai ya koma kallon su, sultan tamkar ya saba da kakan nasa, Khairat da Sadiq sai dariya suke yi suna mamaki. Dole Sarki Abdallah ya karbi surukarsa da jikansa. Aka ware musu dakunan su suka tare, suka tattaro kayansu gaba daya suka dawo gida. Nan take Khairat tayi farinjini a gurin mutane saboda kirkin ta, ba ta iya hausa ba amma koya take har a gurin bayin gidan, bata damu cewa wai ta fita daban a cikin su ba harkokinta kawai take yi tana kula da mijinta da Little Love dinta. Sarki Abdallah ya karbi surukarsa amma a cikin ransa ya san cewa this is not the end of the story. Dole wata rana sai iyayen khairat sun gano inda take, ko kuma ita khairat din da kanta ta nemi zuwa gurin iyayenta. Takanas ya tura kaninsa zuwa Riyadh dan ya bincika masa yaji me iyayen khairat suke ciki, labarin da aka kawo masa sam baiyi masa dadi ba, iyayen khairat sun dauki maganar very serious dan haka ruwa a jallo ake neman sadiq. Charges dinsa suna da yawa, akwai trespassing tunda ya shigar musu gida ba tare da izinin su ba, ga kidnapping tunda basu yarda cewa ita ta bishi ba sun barshi a cewa sace ta yayi, sauran changes din kuma sai an ganta an ga a halin da take ciki, kuma sarki Abdallah ya tabbatar suna ganinta da baby zasu kara da raping da forced marriage, a takaice indai suka kama Sadiq to sai ya biya da ransa. Sarki Abdallah kuwa is not ready to give up his son, tunda dai aikin gama ya riga ya gama. Ya kira Sadiq yayi masa bayanin duk abinda ake ciki, Sadiq ya daga kafada yace "they can't catch me now" sarki Abdallah ya girgiza kansa a ransa yana cewa 'ta yaro mai take bata karko, kuma komai nisan jifa kasa zai fado'. A bangaren khairat kuwa kullum tana tuna iyayenta amma sai tayi sauri ta kawar da tunanin daga ranta, saboda tasan haduwa dasu yana nufin rabuwa da Sadiq da kuma Little Love dinta, wanda bata jin zata iya hakan. Sarki Abdallah yasan tabbas iyayen khairat zasu gano inda take wata rana za kuma su zo neman ta, dan haka kullum yana cikin tararradin zuwan nasu. Iyayen Khairat basu samu nasarar gano inda take ba sai da Sultan ya shekara biyu a duniya, lokacin shekarar ta kusan uku rabonta da gida. Da daddare suka iso, babanta mahaifi da kanin babanta, a fusace suke gaba dayan su, tun daga bakin gate da suka ce mai martaba sarki suke nema, aka gaya mudu ya kwanta bacci suka ce basu damu ba. Ganin cewa ba kananan mutane bane ya saka daga bakin gate aka yo waya cikin gida aka fada, sarki Abdallah yana ji yasan ko su waye. Da sauri ya fita, yana ganin idan aka bi abin a sannu za'a iya samun maslaha. Amma yana zuwa ya fahimci babu maslaha, dan sun dauki zafi sosai, saboda abin ya bata musu rai da yawa, domin khairat tana daga cikin yara masu tarbiyya a zuri'ar su, wannan nema dalilin da yasa aka barta ta tafi karatu England, suna ganin duk yaron da har ya iya ya hure wa khairat kunne har ta juya wa iyayenta baya to lallai yafi shaidan shaidanci, cewa sukayi sadiq is a devil kuma ya kamata ayi eliminating dinsa a society, bai kamata ace wai shine crown Prince din da zai jagoranci al'umma ba. Sun dau alwashin cewa sai sunyi hanging dinsa sun nuna wa duniya yadda mulki yake a Nigeria, in dai ire iren su ne shugabannin Nigeria to ya kamata a dau mataki a kai. Wannan maganar ta bala'in bata ran sarki Abdallah, dan shi yana ganin cewa dansa ba mutumin banza bane ba, dan duk a cikin 'ya'yansa yafi na'am dashi, his only fault is falling in love with a wrong girl, amma kuma mutane ba zasu duba cewa the girl lead him on ba, in irin wannan case din ya faru koda yaushe laifin namiji ake gani ba'a duba macen, da bata bashi fuska ba da ba zaiyi hakan ba. Da aka taso abdallah da khairat basu san me yake faruwa ba sai da suka shigo gurin tukunna, Khairat da gudu ta juya zata koma uncle dinta ya damketa, kuka take yi kamar ranta zai fita tana kiran sultan da sadiq. Da kyar aka samu masu rike Sadiq saboda neman zauce musu yayi. A lokacin Yaya ta shigo da Sultan ya hannunta wanda bacci yake yi hayaniya ce ta tashe shi, ita Yaya ta shigo da Sultan ne wai tana ganin kamar in suka ga dan zasu hakura su bar masa uwarsa amma sabanin haka, suna ganin sultan suka gane dan Khairat ne dan haka baban khairat yace shima Sultan din tafiya zasuyi dashi, ai Islamically da na uwa ne har sai ya girma sannan zai zaba, wannan kam sarki yace ba'a isa ba, da kansa ya karbi Sultan wanda ya fara kuka ganin ummeen sa tana kuka, Sarki yace babu wanda ya isa ya karbi Sultan, dole suka hakura saboda an fi karfin su. Aka uncle din Khairat ya dauke ta ya fita da ita tana ihu tana kiran Sultan wanda shima kukan yake yana kiran Ummee na, duk da baisan me yake faruwa ba, da sauri sadiq ya kwace daga rikon da akayi masa ya bisu har wajan mota yace "Khairat, I will come for you, no matter what, no matter how long" a take babanta ya juyo ya dawo gaban sadiq yace "then I will hang you, If you ever step on Saudi land, I will hang you" daga haka suka ja mota suka tafi. Tashin hankali ba'a saka masa rana, inda Allah ya rufa asiri ma da daddare ne duk gidan kowa bacci yake yi. Da kyar aka mayar da Sadiq daki sarki ya saka akayi masa allurar bacci, amma har yayi baccin yana rantsuwa sai yaje ya karbo matarsa. Sultan kuwa bai koma bacci ba dan gaba daya ya rikice shi ummeen sa da daddyn sa. A ranar sarki Abdallah bai koma bacci ba shima, yana lissafin abinda ya kamata yayi. Duk da yasan cewa gaba da gabanta amma kuma ya tabbatar ba zasu iya taba Sadiq a Nigeria ba, amma yana shiga saudiyya ya zama nama. Sannan kuma ya tabbatar cewa sadiq sai yaje. Tunda assuba ya aika a kirawo masa babban malamin sa da yake saka yayi masa addu'oi idan wani abin ya shige masa duhu a harkar sarautar sa ko kuma a harkar cikin gidansa. Malamin yana zuwa sarki Abdallah ya yi masa bayanin duk halin da ake ciki bai boye masa komai ba. Malamin yayi shiru yana tunani sannan yace "to yanzu Allah ya taimaki sarki mai kake so ayi?" Sarki yace "so nake idan da wani sirri da kake dashi wanda zaka cire masa ita daga zuciyarsa kwata kwata ya manta da ita" malamin yace "akwai Allah ya taimake ka, za'a iya yin hakan. Amma kuma ran sarki ya dade akwai da a tsakanin su, idan an mantar dashi uwar shi kuma dan fa? Duk sanda ya kalli dan dole ya tuna da uwarsa, musamman ma da yake dan da uwar suna kama" sarki ya danyi tunani kadan sannan yace "to ya kake ganin za'ayi? Malamin yace " za'a iya raba su din kamar yadda ka bukata amma kuma ina tsoron abin zai shafi yaron. In akayi aikin, adadin soyayyar da uban yake yiwa dan zai juye