← Book details Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 190

Sashe 90

Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da Sultan muka yi ta pictures sannan muka tafi mkrt, muna zuwa suma 'yan gida suka zo nan guri ya hargitse muka tafi hall din taro, muna shiga muka tarar anyi displaying innovations na graduands, zanen Sultan na gani anyi enlarging dinsa a saka a wall din da take kallon mu, duk kan mu tsayawa mukayi muna kallon zanen, kowa yana cewa "kunga zanen sultan" "yayi kyau" "moon ke kika zana?" Ni dai duk ba wanda na bawa amsa, na juya na kalli sultan a gefe na naga ya saki baki yana kallon zanen, na kasa karanta expression dinsa, can ya juyo ya kalle ni yace "ke kika yi zanen nan?" Na kalle shi cikin ido nace "yes" ya kuma kallon zanen sannan ya sake juyowa yace "dama haka shape din kaina yake kamar mangaro?" Duk gurin kowa sai da yayi dariya nace "you are welcome, dan nasan thank you kake so ka ce" An gama taro lafiya duk muka karbi certificate din mu, I am now officially a neurologist and also a psychologist, Faruk da Amina ma duk sun karbi nasu, daga gurin taron gidan Hafsat muka zarce gaba daya inda Zayed da Hafsat suka shirya mana Walima. Washegari zamu koma Nigeria dan haka Hafsat already ta riga ta gama hada kayanta, Zayed sai bacin rai yake yi, ina jinsa yana gayawa sultan wai shi fa ba'a son ransa ba, kai Sultan maimakon ka bada hakuri sai cewa yayi "chafdi, ai kayi kokari ma, ni kam babu mai rabani da matata dan zata haihu" Hafsat tace "wato kar mu saka rai kenan ko?" Yace "gaskiya kam, kar ma ku saka rai ballantana in na hana kuji haushi" Washegari muka dawo Nigeria. Motar mu tana shigowa gate na hango mutane cirko2 a tsatstsaye. Da sauri muma muka karasa gurin muka fito. Wata arniyar picanto fara tas an nada mata ribbon alamar gift ce, a jikin plate dinta an rubuta 'Her Royal Highness' ina gani nasan aikin waye wannan, nayi ta nemansa ko sama ko kasa bayanan, a saman motar an ajiye card, na dauka na karanta 'it will be my pleasure if you will let me teach you how to drive' lallai sultan rigima yake so ya debo min a gidan nan. Daddy yana ganin motar shima ya gane aikin waye yace da walid "ina sultan?" Ya Walid yace "a hanya ya sauka bai karaso gida ba" Daddy yace "call him" yana zuwa Daddy ya mika mishi key din motar yace "not now. In zaka koya mata mota akwai motoci a gidan nan ku dauki duk wacce kuke so" Sultan ya dan bata fuska Daddy yace in serious voice "I said NO" dole sultan ya karbi key dinsa. Inaji ina kallo aka saka motar a garage aka rufe. A kasa aka gyara wa Hafsat daki saboda tace ba zata iya zirga2r hawa sama ba, nayi mamaki sosai yadda naga suna mu'amala da sultan, ta sake dashi sosai, Mommy ma naga yanzu tana dan kulashi kadan, har wani lokacin takan tambaye shi ya office ko kuma ta dan saka shi wani aiki. Shi kuma na lura yana jin nauyin ta sosai, dan in dai tana guri wata nutsuwa ta musamman yake yi. Kwanan mu biyar da dawowa rannan da safe bayan mun gama breakfast duk 'yan mazan sun tafi aiki sai ga Amira da mamanta sunzo, daga ganin fuskarta na san akwai matsala, a palo suka zauna tun kafin mu gaishe da mama ta fara fada "gata nan fatima na kawo miki ita maybe ke in kika yi mata magana zataji, Amira taki aure, na rasa me yake damun yarinyar nan, taki samarin ma ballantana har ta samu na aure. Ni na gaji, gwara in tattara in koma gida in yaso acan a samar mata miji a 'yan'uwanta" nan Mommy ta samu abinda take so, daga yiwa amira fada ta hada har dani tayi mana tas tace kuma tace ta bawa Amira 3 months in bata fitar da miji ba da kanta da kanta zata kaita kano gidansu a aura mata duk wanda yace yana so. Ni dai bance kala ba, maman Amira tace "wani shegen yaro ta hadu dashi ya hana ta kula kowa kuma shi yaki ya fito ayi maganar aure, na rasa yadda zan yi in raba ta dashi. Nan Mommy ta fara tambayar Amira wanda take so din ita sai ta aika a gaya masa idan bai shirya auren taba ya rabu da ita, tambayar duniyar nan Amira taki magana, duk fadan Mommy haka ta hakura ta kyale Amira. Muka tashi muka tafi dakin Hafsat muka zauna, nayi ta tambayar Amita problem din ta amma tace min ita babu abinda yake damunta tace " ita fa mama duk abinda take dauka ba haka bane ba, shi wanda take magana akansa fa ba saurayi na bane, a makaranta muka hadu, he is my friend kuma haka kawai sai inje in ce masa ya fito ya aure ni? Kullum threats dinta shine zata kaini kano dan tasan bana son can to ni ya zanyi? Idan miji bai zo ba ni zan auri kaina ne?" Sai naji tausayinta na rungume ta ina lallashinta, Hafsat ma ta bata hakuri, nan muka zauna hira na bata labarin duk abinda yake faruwa tsakani na da Sultan, na dauka zamuyi rigima akan maganar amma sai naga tayi murmushi tace "Allah ya sa hakan shi yafi alkhairi" gaba daya muka ce "ameen". Mama anan ta tafi tabar amira ta wuni a gurin mu tana bamu labarin aikin data samu a aso rock, da irin kudin fa take samu tana saving, yanzu basu da wani problem na matsalar kudi. Na danyi tunani nace " Amira ni kuwa ina ma zaki gwada Amir abokin Sultan, he is really nice...." Kafin in karasa ta katse ni "Allah ya sawake, ai kwantan nawa bai kai har haka ba, ke dai da kika ga zaki iya da sultan sai kije kiyi tayi" nayi dariya nace "idan kuma Allah yayi mijin ki ne fa?" Tace "ai Allah baya dora wa bawa abinda yasan ba zai iya ba" tare muka yi lunch da ita, Sultan yana ta tsokanar ta wai Amir yana gaisheta. Bayan la'asar ta shirya tafiya muka je zata yiwa Mommy sallama, nace "Mommy zan raka Amira gida" tace "to sai driver ya kai ku" na dan yi shiru nace "Mommy da Sultan ne yace zai kaimu" ta jima tana kallona ni kuma na sunkuyar da kai kasa sannan tace "a dawo lafiya" Na kira Sultan nace an bar mu gamu nan fitowa. A motar sa muka same shi already yana jiran mu, na shiga gaba Amira ta shiga baya muka tafi, yace "Amira wai yaushe ne bikin kawar ki ne?" Tace "wacce fa?" Yace "wacce ki ka fi damuwa da ita" tace "sai ranar da ka shirya ranar za'ayi" yace "to ai ni already a shirye nake" ina jinsu na rabu dasu nasan neman magana yake yi, naga ya chanza hanya na tambaye shi yace "Amir zamu dauko" da sauri Amira tace "What? Please ku sauke ni in hau taxi, I can't tolerate that man" duk dariya muke mata tace "am serious wallahi, he is so annoying" muna yin packing ya bude ya shiga baya, yana ganin Amira a ciki ya ja tsaki yace "damn it, wannan yarinyar me take yi a motar nan?" Dariya muka sake yi, ni drama dinsu dariya take bani. Daga nan naga mun kuma yin wata hanyar daban, this time banyi magana ba Sultan yace "I want to show you something" Bance komai ba har naga yayi packing a gaban wani katon building duk muka fito na daga kaina naga an rubuta a saman ginin 'MOON CONSTRUCTION AGENCY" na kalle shi da mamaki yace "to ba kin ki gayamin sunan da kike so ba, shi yasa na saka sunan da na fi so" muka shiga gurin suna nuna mana ko'ina suna kuma yi mana bayanin komai,gurin ya tsaru sosai, I trust sultan in dai ta gurin tsari ne, aikin architecture yayi suiting dinsa sosai. Daga nan muka tafi gidan su Amira, a can mukayi magrib sannan muka fito muka kai amir gida shima. Finally daga ni sai shi, nace masa "thank you for the name" yace "I only hope it will shine as bright as you" nayi murmushi. Yace "wai har yanzu Mommy ba ta ce miki komai ba?" Nace "akan me fa?" Ya nuna kansa sannan ya nuna ni yana mischievous smile dinsa. Na gane me yake nufi, na dan bata rai nace "ni ban san akan me kake magana ba" yace "common, how much longer do I have to wait ne wai. Ni aure na ke so seriously" na rufe baki ina dariya nace "kai Sultan, baka jin kunyata kake cemin aure kake so?" Yace "ke din zanji kunya? Ke fa zan aura kuma sai inji kunyarki? Please ki dan tambayi Mommy mana kiji me ake ciki" nace "kai ma wasa kake, me zan ce mata? Mommy yaushe za'ayi min aure?" Yace "exactly" na girgiza kai nace "sai dai kai kaje ka tambayi Daddy" yace "OK, wato ke kina nufin ba kya son auren kenan?" Nace "wai what has come over you ne yau?" A lokacin muka shigo gida, yayi packing amma be kashe motar ba yace "ai na riga ma gaya miki me yake damuna, aure nake so, ai nayi kokari, ya kamata a bani medal ma. Kinga yanxu abinda za'ayi, irin in kuna magana da Mommy sai kike gaya mata ga abinda kike so ayi da bikin ki, zata dauki haske ai sai tayi wa Daddy magana" nace "wai ni na ce maka ina son aure? Kai da kake son auren ba sai ka fada ba?" Ya juyo yana facing fina yace "look into my eyes kice ba kya son aure na" na ki kallonsa, yasa hannu zai juyo fuskata na kara matsawa, yace "kin gani ko? You want it too" na girgiza kaina nace "I don't want anything" yace cikin murya kasa kasa "then look into my eyes and tell me you don't want me" da sauri na bude kofar motar na fita, shima ya bude ya fito ya sha gabana "au guduwa zaki yi ko?" Nace "kafi karfina yau. Yau mood dinka is not for me" yace yana
Chapter 90 · 0% Book details