Sashe 142
Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
ba kai ma sai kasha' duk kuwa da cewa har yau bai san da cikin ba. Ya ajiye basket din yace "bara in zagaya wajan perfumes, da akwai wani turare da nake ne ma ban sani ba ko zan samu anan" nasan babu wani turare da yake nema, ya gaji ne so yake in ce masa ai na gama mu tafi, na juyo nace masa "OK" ya saki baki da mamaki yana kallona yace "kin yarda in barki anan ke kadai" nace "I am 23 years old, ba zan bata ba" ya juya ya tafi, har yakai karshen lane din ya juyo, nayi masa alamar bye2 ya girgiza kansa ya sha kwana. Na juya ina dariya, a raina ina tunanin maybe tonight in gaya masa labarin cikin nan, I can't wait to see his reaction. Nayi murmushi na cigaba da kwasar sweets dina. Kamar daga sama naji an kama hannuna an fara jana da sauri, "let's go, babu wani abinda ba zaki samu ba a gurina, menene anan din wanda ni bani dashi?" Duk da banga fuskar wanda ya rike ni ba amma muryar sa ta saka na gane shi, hakan kuma ya saka ni wata irin faduwar gaban da har sai da naji daci a bakina, wani amai naji yana neman taso min, nayi kokarin kwace hannuna amma bai sake ni ba kuma bai kalle ni ba, cikin muryar fada amma kuma cikin rada saboda bana son inyi calling attention din mutane zuwa garemu nace "what are you doing?" Yayi sauri ya sake ni, lokacin har mun kai karshen lane din, a razane yake kallona, hakan ya tabbatar min ba wai yana sane ya aikata abin da yayi ba, murya kasa kasa shima yace "Maimunatu what are you doing here? Am very sorry na dauka Amina ce, tare muka zo da ita kuma itama bakar riga ta saka. Am very sorry" nace "am here with my husband, go away bana son ya gan mu tare" ya dan bata fuska yace "you look scared, why are you scared of your husband, is he mistreating you" by then gaba daya hankali na ya tashi, na juyo da sauri na matsa daga inda yake amma sai ya kuma zagayo wa gaba na, fuskarsa fal da concern, yace "Maimunatu please tell me if you are not OK" numfashi na ne gaba daya naji yana neman daukewa, Sultan na hango a farkon lane din a tsaye, da kwalbar turare a hannun sa, tun daga inda nake na hango jijiyoyi sun fito rado rado a goshinsa, farin idonsa ya kada yayi jajawur light brown din ciki kuma yayi bakikkirin, mara ta ce ta daure kamar zan yi fitsari, a hankali na furta "innalillahi wa inna ilaihir rajiun". Winter is really coming