Sashe 54
Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read
Ban gaya wa sultan zancen tafiyar ba sai ana gobe zamu tafi, a tunanina ai in lokaci ya kure ba zai samu chance din bina ba, bawai inason rabuwa dashi bane a'a sam bana jin dadin yadda nake wa iyayena karya akansa sannan kuma har yanzu na kasa samun courage din zuwar musu da maganarsa. Tun da naje school muna tare dashi har aka zo daukana amma na kasa yi mishi maganar, sai bayan nazo gida nayi shirin kwanciya sannan na kira shi a waya, ya dauka da sallama kamar yadda ya saba, na amsa masa sannan yace "are you already missing me, love" nadan yi dariya sannan nace "magana nake so muyi, be serious please" yace "ina jinki" na dan sassauta murya nace "kana ji, dama wani dan course ne daga makaranta aka tura mu zamuyi a US, to gobe zamu tafi insha Allah, shine dama na ke so in gaya maka tun dazu a school kuma na kasa" shiru bai ce komai ba, na cigaba "Sultan dan Allah kar kayi fushi, ina taso in gaya maka wallahi tun tuni bansan yadda zaka dauki maganar ba, ba wani dadewa za muyi sosai ba, please say something" murya a duskure yace "for how long zaku kasance a can din?" Na yi shiru kalmomin sunyi min nauyi, sai da ya maimaita tambayarsa sannan nace "6-8weeks akace mana" nayi sauri na kara da cewa "amma ba lallai ne mu kai hakan ba, da mun gama zamu dawo" shiru bai ce komai ba amma ina jiyo numfashinsa ta wayar, sai da na gaji na kira sunansa "Sultan?" Yace "yaushe zaku tafi" nan ma amsar tawa ba mai dadi bace "gobe" ya maimaita "gobe?" Na daga kaina kamar yana kallona, "wato kina nufin dazu da muka rabu bye bye kika yi min kenan sai nan da wata biyu?" Na danyi dariyar yake nace "wata biyu ne fa kawai Sultan, kuma ai kullum zamu ke yin waya, kuma dana kammala wata biyun nan na gama project dina sai in rubuta report in yi submitting.... " kawai ji nayi ya katse wayar, na tsaya ina kallon wayar a hannuna, sultan dan rigima, text na rubuta masa da kalamai masu dadi cikin sigar bada hakuri na tura masa, shiru2 babu reply, lallai da gaske fishin yake yi, bamu taba fada da sultan ba, bai taba yin fushi dani ba, sai naji rai na duk babu dadi. Washe gari 12 jirgin mu zai tashi dan haka da wuri na tashi na kaya na da zan tafi dasu, bini2 sai in duba waya ta amma babu missed call babu message from sultan. Kudi sosai daddy ya bani kuma ya kira uncle Ben ya sake tuna masa yau ne fa zuwa na. Mommy har lokacin cewa take yi ita fa sam hankalinta bai kwanta da zancen tafiyar nan tawa ba, nima kuma haka, duk jina nake yi jiki a sanyaye ko dan ban taba yin tafiya mai nisa on my own ba. Gaba dayan su ne suka raka ni airport har mommy, har na shiga jirgi ina ta kiran Sultan amma yaki dagawa, duk sai naji kamar in fito ince na fasa tafiyar dan dai kawai babu yadda zanyi ne. Kira after kira nake ta jera wa Sultan kafin passengers su gama shigowa amma still no answer, na kashe wayar na jefa a jakata, hankali na duk ya tashi, anya kuwa nima zan iya jure wadannan satittikan ba tare da sultan ba? Especially in ya cigaba da kin daukan wayata. Muka sassaka seat belt din mu jirgi ya tashi, wani dan tsohon bature ne a kusa dani dan haka muna gaisawa na gyara kwanciyar kujera ta na saka earpiece ina jin karatu na lumshe ido na ina so inyi bacci ko Allah zai sa zuciya ta tayi sanyi. Nasan dole Sultan zai sakko dan kansa dan haka nayi alkawarin ko mun sauka bazan kira shi ba har sai ya kira ni da kansa. Jiki nane ya bani kamar ana kallona, to shi wannan tsohon menene nashi na kallon mutane kuma? Su turawa fa sam basu da kunya wallahi. Mayafi na naja na rufe fuskata ba tare da na dube ido na ba, ji nayi ansa hannu an bude fuskar tawa, da sauri na bude ido na zanyi bala'i amma se me? Sultan na gani zaune a kusa dani yana kunshe dariya "do you miss me, Love?" Na rasa dariya zanyi ko kuka, mamaki da takaici duk suka rufe ni shi kuwa dariya sosai ya ke yi, na dauki magazine din kusa dani na fara dukansa aka da ita, ya saka hannayensa ya kare yana cigaba da dariya, can dai na lura mutane da yawa a jirgin mu suke kallo, nayi sauri na ajiye magazine din hannauna na maze kamar bani ce nake yi ba. Sai da ya gama dariyarsa sannan ya juyo, "kin dauka fushi nayi ko?" Nayi banza na rabu dashi, ya cigaba da "ni na isa inyi fushi dake? Ai kin wuce wannan gurin. New York is not England. Bazan iya barinki ki tafi ke kadai ba, jiya bayan munyi waya na kira airport na tambayi wanne jirgin ne zai tafi America yau kuma karfe nawa zai tafi, sai kawai nayi booking na shirya kayana" nace masa "ya akayi ka samu visa daga jiya zuwa yau?" "Visa kuma? Legally ni dan America ne acan aka haife ni, i don't need a visa to go there" what a fool i have been, shaf na manta da wannan tsarin, na kasa tantancewa farin ciki nayi da zuwan Sultan ko bakin ciki. Earpiece dina guda daya ya cira ya saka a nasa kunnen shima ya kwantar da kujerar sa a haka muka yi bacci tare. Bamu farka ba sai da aka fara announcing jirgin mu zai sauka sannan muka tashi muka saka seatbelts din mu. Direct asibitin muka tafi, muna zuwa muka hadu da sauran students aka bamu keys din dakunan da zamu zauna sannan aka fara zagayawa damu za'a nuna mana duk inda muke bukatar sani, Sultan yazo ya ce in bashi key dina ba musu na mika masa ya tafi. Ina kallon yadda sauran students din suke kallona da alamar tambaya, a raina nace ina ruwanku? Mahdi ya dawo kusa dani yace "so..... I have seen you found your dark skinned man, Allah ya bar kauna" nasan magana yake gayamin dan haka na dauke kaina nace "amin" sai kuma yace "are you guys like living together kenan?" Na kalle shi ya hade rai nace "what do you mean?" Yace "naga ya biyo ki nan, kuma gashi har da wani karbar key din dakinki ya tafi zai shiga, ni dai a sani na ba'a gayyacemu daurin aure ba ballantana muce ai mijinki ne" na katse shi nace "dakata ya isa haka, kaya na ne da na zo dasu a cikin motar daya dauko mana shata daga airport, shima kuma da kayan sa a ciki, ya karbi key dina ne saboda ya sauke min kaya na ya tafi ya kai nasa masaukinsa. I don't even know me yasa nake maka bayani cos I owe no one an explanation" daga nan nayi gaba na barshi. Sai kuma naji a raina babu dadi saboda gaskiya ya fada min, sultan ba muharramina bane he have no business da shiga dakina. Bayan mun gama duk zagayen mu, a gajiye muka koma lodge din mu, one bedrooms ne a jere kowanne da number a jikinsa. Na duba nawa na tarar da a bude an dan saya kofar, a hankali na tura ne leka kaina ina sallama, babu amsa, na shiga ciki nace "sultan" nan ma shiru babu motsi, na sauke ajiyar zuciya sannan na kare wa dakin kallo, an gyara shi tas sai kamshin freshner yake yi, sabon bedsheet din da nazo dashi ne akan gadon tare da bargo, wato Sultan har kayana ya bincika ya dauko kenan ko? Shi sam baisan ma'anar boundary ba. Ya share dakin tas yayi mopping ya gyara gadon ya jera min kaya na a chest of drawers da suke dakin, ina dubawa naga har underwears ya saka su a drawer daban, kunyar duniya ta isheni yau Sultan yaga panties dina da braziers dina. Na duba toilet naga shima a gyare tas yana ta kamshi, sai a lokacin na lura har da karamin carpet ya siyo ya saka a gaban gadon. Tun ba yau ba nasan Sultan yana da tsafta sosai dan har mamakin tsaftar sa nake inna lura da irin yadda ya taso, koda yake ita tsafta a jinin mutum take, dan wani zakaga gidan su masu tsafta ne amma shi a kansa kazami ne. Komawa nayi nayi locking kofar, kayan jikina na chire na shiga wanka na tarar har kayan wanka na ya jera min a toilet din, na fito na shirya cikin riga buba na gyara gashina nayi packing a tsakiya kamar yadda nake yawan yi in ina gida, na fesa turaruka na sannan na saka hijab na fara ramuwar sallolin da ake bina. Ina idarwa naji anyi knocking nace "am coming" kafin in karasa kawai naga an bude kofa an shigo, na tsaya ina bin shi da kallon mamaki ganin key a hannunsa, wato spare key din dakin ya zare ya tafi dashi, as if dakin namu ne mu biyu, na hade rai sosai na rike kugu ina kallonsa, shi kuma yana murmushi, Allah yaso ma ban cire hijab din da nayi sallah dashi ba, "wannan bata ran kuma fa? Ni na kasa banbance yaushe kika fi kyau, in kin bata rai ko kuma in kina dariya" na kare daure fuska na ce "me yasa ka daukar min kex din dakina? Kasan hakan ai ba dai dai bane in kazo gurina sai ka kira ni a waya in fita in same ka ba wai ka shigo min daki ba" yi yayi kamar bada shi nake ba ya karaso dakin ya ajiye ledojin abincin da suke hannunsa sannan ya zauna a bakin gadk yana cewa "wash na gaji da yawa" na kara masa wata hararar nace "malam sauko min daga gadona, kuma ma waye ya baka damar ka bude min kaya? Kasan dai kayan mata sirri ne ko?" Ya sake share ni ya sauko yana bude ledar abincin da akayi sealing dinsa a cikin dan babban container, sai lemuka wanda ban taba ganin irin suba masu sanyi ya ajiye a gefe "malama in zaki zo muci abinci kizo, in kika tsaya iyayi kinsan ni bana wasa da abinci zan chinye ne in barki" daga haka yasa cokali ya fara cin abincinsa, ina kallonshi yana wani lankwasar da wuya yana lumshe ido nima naji yawuna ya tsinke kuma dama yunwa nake ji da gaske, a hankali na tafi kamar wadda ake jana da magnet naje na zauna na dauki cokali na fara ci dadin abincin yana ratsani, sai da muka kusa cin rabin abincin babu wanda yace wa kowa komai, can dai naji babu dadi tunda ni ban iya shiru ba nace "thank you for.... " na nuna dakin da hannuna, ya ajiye spoon din hannunsa yace "you are welcome" na ce "a ina zaka sauka ne kai?" Yana murmushi ya nuna kan gadon, na harare shi yayi dariya yace "relax 'yammata, garin mu fa kika zo, i have a house here duk da dai yanzu da akwai wadansu friends dina a ciki amma acan zan sauka" na gyada kaina alamar gamsuwa, a haka muka gama cin abincin mu yana ta yi min hida, nayi mamakin yawan abincin da naci, da zan sja drink din sai da na duba ingredients dinsa, ina kallon sultan yana yi min dariya na harare shi kawai bance komai ba. Yana gama wa "nace to atashi kuma asan nayi, sai da safe" ya mike yace "ba sai kin kore ni ba nima dama baccin nake ji" har ya kai bakin kofa nace "bani spare key dina" ya jiyo yace "na karfi ne, in kina da karfi ki kwata"