← Book details Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 182 OF 190

Sashe 182

Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

na gaya masa duk abinda nake so, wajan azahar yazo muka sake yin maganar dashi, na cire pages din dana keso na bashi a flash, na dauko kudin dana san zai bukata na bashi amma yaki karba ya tafi. Da daddare sultan yana gurin Takawa ni kuma ina zaune ina cin abincin da Ummee ta aiko min dashi sai ga wayar Mommy, na dauka na gaishe ta tace "Moon mai ya faru ne?" Nasan maganar da take nufi amma nace "Mommy akan me fa?" Tace "The whole of Abuja is on fire akan sultan. Yanzu friends dina sunfi uku da suka kira ni suna tambayata" a raina nace 'sako na ya isa kenan' a fili kuma nace "me ya faru ne Mommy" tace "dazu da yamma helicopter yayi ta yawo a gari yana watso takardu, unguwa unguwa, takardun zanen project dinki" sai kuma tayi shiru, jin bance komai ba tace "Moon, did you do it?" Nace "yes Mommy" tace "why?" Nace "Mommy just ke da abokan aikin ki a office ku shirya, you will have alot of cases this week". Hakan kuwa akayi, kusan duk garin Abuja lungu da sako, unguwannin masu kudi da kuma unguwannin talakawa babu wanda bai samu sako na ba. Nan take 'yan jarida suka samu abinyi, sultan kin zuwa yayi office a satin, Takawa kuma yace a rufe gate din palace kar abar wani dan jarida ya shigo. Kamar yadda nayi tsammani, talakawan duk da sultan yake taimakawa, wadanda nasan labarinsu da wadanda ban sani ba, haka suka ringa fitowa suna gaskata maganganuna na cikin takarda ta, wadansu ma shi kansa sultan ya manta dasu, haka aka ringa dauko dukkan files dinsa na gurin police ana resolving cases din. A haka har zancen orphanages dinsa ya fito shima, 'yan jarida kam sun samu abin yi, nan suka dukufa bincike har suka tonawa dan majalissar da yace shine yayi orphanage din asiri. A satin, kusan duk jaridar daka dauka hoton sultan ne a front page dinta, anyi masa title 'Our Prince' wadansu kuma su rubuta 'Our Lion'. Sultan kam har yanzu bai ce komai ba, in ma na kunna TV ana maganar sai ya chanza channel. Ni kam babu abinda nake yi sai godiya ga ubangiji da yasa plan dina ya zama successful. Sultan's name is now clear a cikin mutane. Babu wanda in sultan ya wuce zai zage shi, ko an samu mai zagin ma, to kuwa tabbas za'a samu masu kare mishi. 'Ya'yana ba zasu tashi ana musu gorin babansu was a criminal ba. Wannan kenan. Satin biki ya kama. Gidan mu ya chika kamar yadda aka saba in za'ayi biki. Ballantana wannan da yake bukukuwa ba biki ba. Hatta zainab din ya walid an dauko ta an dawo da ita abuja, anan za'ayi bikin baki daya. Hafsat ta dawo gidana, tace can yayi hayaniya da yawa, dan haka daga nan muke shiryawa mu fita tare. Sultan ma tunda bikin yazo kullum suna tare da su Ya walid, amma kuma hankalinsa gaba daya yana kaina, dan badan ummee ta saka baki ma ba da ba lallai ne ya barni zuwa bikin bama gaba daya. Yanzu ma kuma babu kwana, sai dai inje in wuni da daddare in dawo gida. A tare muka hada amaren mu da angwayen mu muka kama su rana daya duk a gida. Akayi mothers eve ranar thursday, ranar friday kuma za'ayi wuni, Saturday a yi daurin aure, da yamma akai amare sannan da daddare ayi dinner. An kai dinner din dare ne saboda ana son Fadila amaryar ya Habeeb ta samu damar halarta itama. Tun a ranar Thursday da daddare na lura kafafuwana sun fara kumbura, nasan wannan normal ne ga mai tsohon ciki musamman kuma ga hidimar biki da muke yi, dan haka da daddare na kwanta da wuri na dora kafata akan pillows, sam ban nunawa sultan ba saboda ba karamin aikinsa bane yace bazanje ranar wuni ba, ranar wuni muka shirya da sassafe muka fita, aka wuni ana shan shagali, sai dare sannan muka dawo gida. Muna zuwa gida Hafsat ce tayi min maganar yadda kafa ta ta kumbura suntum, tace "Moon you should stay home tomorrow, ki huta, daurin aure ne sai kai amare, dinner da daddare za'ayi kafin nan kin huta" nasan gaskiya take gaya min, I already have high bp, wannan kumburin nawa is not normal edema, it may be pre-eclampsia, amma sai nayi tunanin ai in naje goben ba wani abun zanyi ba, zama kawai zamuyi, in za'aje kai amare da dauko amarya zan iya zama na inki zuwa, sai da daddare in je dinner. Na riga sultan kwanciya dan haka na rufe jikina bai ga kumburin ba, kuma da sassafe ya fita, zasu fara zuwa bauchi daurin auren yaya Habeeb sannan a dawo abuja a daura na ya Walid da na Amina. Banbi shawarar Hafsat ba saboda ina ganin babu yadda za'ayi in zauna a gida bayan ana can ana shagali a gidan mu. Sultan yana tafiya nabi Hafsat muka tafi gida. Komai lafiya lau yake tafiya har aka yi daurin aururruka aka gama, aka zo hidimar kai amare. Dama already wadanda zasu dauko Fadila sun riga sun tafi, sai aka tafi kai zainab tunda ita ta gida ce ba sai an jira anzo an dauke ta ba. Basu dade da tafiya ba sai ga masu daukan Amina sun zo, nan fa kallo ya koma sama, duk aka fito compound ana kallonsu dan wani sabon bikin suka bude, sun yi shigar su irin ta yarabawa sunyi kyau sosai, sun taho da kaya sukace a bawa Amina ta saka, ina daga kwance naga kallo zai barni dan haka na mike nima na fita, wata 'yar matashiyar budurwa ce tazo ta tsaya gaban Amina ta karanta wata doguwar takarda mai dauke da dogon jawabi akan irin soyayyar da Ibrahim yake yi mata da alkawarin da yayi na zai rike ta amana, inta amince to ta bisu su tafi, in kuma bata amince ba to ta zauna a gida. Daga haka ta mika wa Amina hannu, Amina ta saka hannunta a cikin na yarinyar, nan take guri ya kaure da murna. Hayaniyar gurin ce tasa naji kaina yayi wani mugun sarawa, na rike kan da sauri, ganin babu wanda ya lura dani ya saka na lallaba na koma daki, ina duba hannayena naga sun kumbura suma, na kwanta akan gado na lumshe ido na ina jin ciwon kaina yana karuwa ga kide kiden da akeyi tamkar a cikin kaina suke kadawa. Na lalubi wayata na kira Hafsat amma wayar tana ta ringing bata dauka ba. Na koma na kwanta. Cikin hikimar ubangiji aka daina kidan, ina jin karar motoci alamar an tafi kai amina itama. Take naji gidan tsit dan kusan babu kowa a manya, babu kuma wanda yasan ina dakin, kowa zai dauka na tafi kai daya daga cikin amaren. Na danji kan ya rage ciwon, na tashi na nemi jakata na sha magungunana sannan na koma na kwanta. Take bacci mai nauyi ya dauke ni. Muryar Mommy ce ta tasheni, tana tabani tace "Moon dama kina gida? Ya akayi kika zauna ke kadai? Da wani abun ya faru fa?" Ni dai bance mata komai ba, tunda wani abun bai faru ba ai shikenan. Har yanzu akwai ciwon kan, na tashi zaune ina rike kaina Mommy tana ta jera min sannu, na kalli agogo naga har anyi magrib, dan haka na shiga toilet nayo alwala, ina dawowa dakin na kalli fuskata a madubi naji gaba na ya fadi, gabaki daya fuskar ta kumbura, na kalli hannayena naga har kyalli suke. I really need to go to the hospital right now amma bana son in tayar wa da mutane hankali ana cikin biki. Na tayar da sallah, nayi magrib da isha gabaki daya, ina kallon mutane sai shirin tafiya dinner sukeyi amma ni kam nasan wannan dinner din babu ni a cikin ta. Na koma nayi kwanciyata. Mommy ta shigo ta samu guri ta zauna tana kallona. Nace "Mommy baki fara shirin tafiya ba?" Tace "Moon ina zanje baki da lafiya? In naje ma ba zanji dadin dinner din ba, dan hankali na biyu zai rabu" sai naji babu dadi a raina, dan nasan kawayen Mommy da yawa zasu je gurin kuma za'ayi ta nemanta, nace "Mommy kiyi tafiyar ki kawai, ai ba wani abin ne yake min ciwo ba, kawai dai ina bukatar in huta ne shi yasa ba zanje ba" ta jawo pillow tana murmushi tace "nima ina bukatar hutun ai" nayi murmushi, dan nasan babu abinda zan gaya wa Mommy wanda zai saka ta tafi gurin dinner din nan ta barni a gida, God bless our mothers. Hafsat ma ta shigo tayi tayi Mommy ta tafi ita ta zauna amma Mommy taki yarda. Ni dai daga nan na koma bacci. Karar waya ta ne ya tashe ni, na duba naga 'my Sultan' na dauka ina jin ciwon kaina yana karuwa, yace "Moon baki fa lafiya me yasa baki kirani ba?" Ji nake kamar a cikin kaina yake maganar, nace "ai muna tare da Mommy, babu wani abu, kayi zamanka in an tashi sai kazo mu tafi gida" yace "you dey craze? Ya zanyi in zauna anan babu ke? Am coming right away" daga nan ya kashe wayar. Mommy tana zaune tace "zuwa zaiyi?" Nace mata "eh, dama ki shirya, in yazo kawai sai mu tafi gida ke kuma sai ki tafi gurin taron" ta gyada kai tace "bara yazo din tukunna sai in shirya. Ina baba gajin ki? Anan gurinki take kwana ko?" Nace "eh, anan take kwana. Ummee ma ta karo min wata baba Sa'a". Muna tare da Mommy sultan ya aiko a gayamin yazo, Mommy tace ace masa ya shigo dakin, ita kuma ta fita ta tafi nata dakin. Ina kwance ya shigo, ya tsaya a bakin kofa, na tabbatar ya lura da yadda jikina ya kumbura, yace "menene yake miki ciwo yanzu?" Nace "ciwon kai ne, sai jiri da nake ji inna tashi" ya karaso ya zauna a bakin gadon ya taba wuyana yace "your temperature is also high. BP din ne ko?" Na gyada masa kai. Yace "dama abinda nayi ta lissafi kenan. Wannan hayaniyar da zirga zirga is not good for you" na kirkiro murmushi nace "an
Chapter 182 · 0% Book details