Sashe 146
Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Episode Eighty : The Skeleton in The Closet A lokacin da su David suka ajiye shi a kusa da motar sa, kasa tashi yayi daga gurin, jira yake mutuwa ta karaso ta dauke shi, dan shi a ganinsa bashi kuma da sauran rayuwa a gaba. To menene sauran rayuwa in babu Moon? Dama itace farin watan data haskakae rayuwar ta sa da hasken ta, to yanzu tunda babu ita kuma menene yayi saura in banda duhu, a cikin duhun zai yi ta lalube har yaje ya afka ga halaka, he is sure that he will be lost without her. Yana kwance yaji tsayuwar mota a kusa dashi, a tunanin sa ma robbers ne kuma he didn't care. Sama sama yaji muryar Amir yana yi masa magana, ya dan bude idonsa ya kalle shi ya mayar da idon ya rufe. What is this man doing here? Me ya kawo shi? Yana jin Amir ya fara kokarin tashin sa, ya kwace, Amir yace masa "Sultan menene hakan kake yi wai? Moon ta kira ni tace inzo gurin ka, me ya faru? I really hope you are not drunk kuma? Sultan ya bude ido ya kalle shi sosai sannan yace cikin murya kamar ba tasa ba "Moon ce tace kazo nan?" Amir yace "eh, me ya faru haka" Sultan ya fara kokarin tashi Amir ya taimaka masa ya bude masa mota ya shiga suka tafi. Me yasa Moon ta kira Amir? Shin hakan yana nufin she still care about him ko kuma just tana so a dauke mata shi daga kofar gida saboda bata son ganin sa?. Ya lumshe idonsa yana tunanin abubuwan dasu ka faru tsakanin su, she even said zata tabbatar da cewa dan da yake cikin ta bai san cewa shine mahaifinsa ba, she hates him that much kuma bai ga laifin ta ba, koma menene ya faru laifinsa ne. Na farko ta ya akayi ma zuciyarsa ta raya masa cewa Moon sun hada plan da Ibrahim zasu hadu? How can he even think that? Kishinsa ya rufe masa ido kawai ya fadi magana without thinking kuma wannan maganar ita ce tafi komai bata wa Moon rai. Shi shine mai bad past, amma ita ko yaushe tana kyautata masa tsammani, ya tuna case din khulsum, tun kafin ma moon ta tuntubeshi da maganar har ta yanke hukuncin karya suke masa, amma shi bai showing mata the same courtesy ba. Wannan shine babbar nadamar sa ba wai ture Ibrahim ba, that bastard, he deserve that, uban wa yace ya biyo su? Har cikin gidansa ya shiga gurin matarsa and he let him go, sannan kirikiri ya ganshi ya rike hannun matar sa a cikin store and he still ignore him, duk da cewa da kyar ya danne zuciyar tasa ya yi ignoring din nasa, dan a lokacin babu abinda zai bashi satisfaction irin ya ga ya zubar masa da hakoran da yake using yake smiling at his wife, amma ya danne zuciyar sa saboda a lokacin yana ganin laifin moon ne kamar ita ce ta bada hanya, bayan sun fita kuma ya biyo su, why will he follow them in ba rainin hankali ba, waye suna tafiya da matarsa zai ga tsohon saurayinta yana binsu a baya kuma ace ransa ba zai baci ba? Laifin sa daya a lokacin, bai kamata yayi playing with rayuwar moon ba, kamata yayi yayi packing motar ya fito da Ibrahim da ga tasa motar ya babballashi ya zubar a gurin sannan suyi tafiyarsu. Suna zuwa gida a part din Amir suka tsaya. Amir ya fito ya zagayo ya fito da sultan sannan suka shiga ciki, shi Amir duk a tunanin sa Sultan a buge yake, yana zuwa ya kwantar dashi a kan gado sannan ya debo ruwa mai sanyi ya kawo masa, yana fara sha yaji ruwan kamar madaci, ya furzar ya ajiye cup din a gefe. Amir ya zauba a gefensa yace "Sultan why do you do it? Ka samu good life with Moon why will you throw it all away saboda giya?" Wani takaici sultan yaji ya kama shi yace "fuck off amir" ya juya masa baya yayi kwanciyarsa. Amma babu bacci babu alamarsa sam, yadda jiya baiyi bacci ba haka yau ma da alama va zai yi baccin ba. Wata biyar kenan da aurensu da moon amma bai taba kwanciya ba tare da ita ba sai yau, bai taba tunanin kuma zai kwanta ba tare da ita dinba, amma yau gashi basa tare kuma duk suna raye, suna kuma gari daya. She even call the security on him tasa suka fita dashi ko kallon sa kuma bata yi ba, wannan ya tabbatar masa da cewa she means what she said, rabuwa zatayi dashi kamar yadda wadda ta haife shi ta rabu dashi, kamar yadda wanda ya haife shi ya rabu dashi, bai damu ba ko ya mutu ko yayi rai. Daddy daya ke kallo a matsayin sabon uba ma ya hade masa rai, daya gaishe shi kin amsawa yayi kamar yadda in ya gaishe da takawa baya amsawa. It is all over. He was a fool to even think it will work. Moon was right, rayuwarsu ba daya bace, they care about everyone hatta wanda ya bata musu, shi kuma va haka yake ba, they expect him to do the same, instead sai gashi ya kusa aikata kisan kai. He is a monster, shi ya riga ya dade da sanin hakan, idan zuciyarsa ta debe shi shi kansa abinda yake aikatawa sai daga baya yayi mamaki. Amma kuma yanzu har acikin zuciyarsa bai ji yayi nadamar abinda yayi wa Ibrahim ba, the bastard. Yanzu haka ma da zai ganshi da sai ya karasa shi, tunda shine yayi sanadin duk wannan abinda ya faru. Shi kam yasan rayuwarsa ta kare, a kan gadon nan zaiyi ta kwanciya har sai mala'ikan mutuwa ya tuno dashi yazo ya dauke shi. Sai kuma ya tuno da halittar da take cikin marar Moon, wani nauyi yaji zuciyar sa tayi masa, his baby, yaci burin ya haifi 'ya'ya ya nuna musu soyayyar shi da ba'a nuna masa ba. Amma kuma Moon ta gaya masa cewa idan bai chanza zafin zuciyarsa ba 'ya'yansa ma gudunsa zasu ringa yi. Yaji wani irin daci a zuciyarsa, just the thought of his children resenting him ya saukar masa da wani mugun zazzabi. Ya jawo bargo ya kudunduna, maybe the baby will be better off without him. Tun da assuba Amir ya taba shi yaji irin zafin da jikinsa yayi, da kyar ya tashi yayi sallah ya koma ya kwanta. Gaba daya hankalin Amir ya tashi, ya manta rabon da yaka Sultan a kwance babu lafiya, tun wata rashin lafiya da yayi suna America, sultan has always been healthy and energetic. Zuwa karfe goman safe yaga zagin jikin karuwa yake yi, duk uban bargunan daya loda masa amma karkarwa kawai yake yi hakoransa suna haduwa guri daya, a hankali yaji yana magana kasa kasa, ya sunkuyo da kansa dai dai fuskarsa yaji yana cewa "Moon am sorry, moon am sorry, dan Allah kiyi hakuri ba zan sake ba" wani irin tausayin abokin nasa yaji yana ratsa shi. Menene kuwa zai hada shi da Moon har haka? Shi yasan a rayuwarsa bai taba ganin soyayya irin ta Sultan da Moon ba, to menene kuwa zai saka su bata?. Ya dauko wayarsa yayi dialing number din Moon amma wayar a rufe, ya kuma kira har five times amma bai samu ba, yayi mata text "Sultan babu lafiya, kuma ke yake nema" ya tura mata. Daga nan ya kira number din doctor din gidan ya gaya masa halin da sultan yake ciki. Ba'ayi awa daya ba doctor din yazo ya duba sultan, shi kansa yayi mamakin zafin jikin sultan a take ya saka Amir ya taya shi suka cire masa bargonan daya lulluba suka cire masa riga da wandonsa suka barshi da singlet da gajeren wando sannan suka yi ta goge masa jikin sa da jikakken towel, amma suna dora towel din sai suga ya bushe saboda zafin jikin, a haka dai uka samu da kyar jikin ya danyi sanyi kadan, idan sultan gaba daya ya juye kamar ba nasa ba, doctor din da sauri yace a saka shi a mota su tafi dashi asibiti, suna zuwa aka tafi dashi private room likitoci suka hau kansa, Amir ya zauna anan shi kadai a waiting room, kawai ji yayi hawaye yana zubo masa, a ce mutum mai gata irin sultan, a Prince, da uwarsa da ubansa da matarsa a duniya amma an kawo shi asibiti babu kowa a gurin sai shi? Yana nan yana ta kukansa har doctor ya fito yana kallonsa yace "Haba Amir, kar ka badani mana, kana namiji kana kuka?" Amir bai kula da tsokanar da yake masa ba yace "doctor how is Sultan?" Yace "da sauki zamu ce. Fear dina shine brain dinsa, zazzabinsa yayi zafi da yawa in tsoron kar ya taba kwakwalwarsa, kuma yana tunani da yawa, wannan shi ya saka muka kasa stabilizing bp dinsa, amma for now mun yi masa allurar bacci, za mu jira kuma muga sanda zai farka. But please do your best ka ga ka kawo masa abinda zai faranta masa idan ya tashi daga baccin" Amir yayi masa godiya sannan ya shiga da sauri inda sultan yake kwance, tun kafin ya karasa kusa dashi ya hango irin ramewar da yayi da kuma farin da yayi, fatar bakinsa tayi purple alamar babu isashshen jini a jikinsa, kuma zazzabin ne ya kona jinin. Ya karasa ya rike hannunsa da yaji yayi sanyi kalau yanzu alamar zazzabin ya sauka, a hankali ya fara magana "Sultan ya zanyi? Me zanyi maka ka samu lafiya sultan?" Sai kuma ya mike kamar wanda aka tsikare shi yayi kissing hannun sultan ya fita da sauri, direct gidan su Moon ya dosa, tun daga bakin gate David ya tsayar dashi fuskar nan babu rahama a cikin ta ga bindiga a kugunsa yace "you are no longer welcome here" Amir yace "ba shiga zanyi ba ai, Moon nake son gani" David yace "bata son ganin ka ita" wata zuciya ta debi amir amma ya danne yace "ya akayi kasan bata son ganina, ka shiga ka gaya mata nine nazo zata fito" David yace "itace