← Book details Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 190

Sashe 74

Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Sai bayan magrib muka isa Tahoua. It is worse than I imagine. Gidan da muka je gidan kasa ne rufin azara, cikin wata chakudaddiyar unguwa. Ji nayi gaba daya hankali na ya kuma tashi, yanzu mommy tana nufin anan zan zauna har sai ranar da ta waiwayoni? Muna shiga muka tarar da wata tsohuwa tana kirki a itace, da mamaki ta taso ta tari daada, suka rungume juna suna ta murna, ni dai 'yar kallo ce, ta kaimu wani daki mai dan girma wanda ko siminti babu sai kasa. Ta shimfida mana tabarmar karauni muka zauna na gaisheta tana kallona tace "tubarkallah, daada ina kika samo 'yar kyakykyawar yarinya haka?" Daada tace "diyar bintou ce fa" tace "hidijan, yanzu bintou ke da diya kamar wagga?" Daada tace "laa wagga ita atta hudu" matar tace "alqur'an daada wagga ya kamata a amra mata dan'uwa ta zamna a Niger" ina jika na mike nace "ina ne bandaki zan zagaya?" Matar ta taso ta rakani, shaddar kasa, na kasa tsugunnawa na fito nayi alwala nazo na tayar da Sallah. Ina yin sallar isha na shimfida zanina na kwanta na lulluba da hijab dina, ba bacci nake ba, so nake inji hirar su daada dan insan halin da nake ciki, ga mamakina ko zance na basu yiba, labarurrukan da kawai suke yi suna dariya. A cikin hirar naji daada tace ai akan hanya muke, tsayawa mukayi mu huta, Agadaz zamu je. Zumbur na mike daga kwancen da nake nace "Agadaz daada? Daada Agadaz fa karshen duniya kenan?" Cos haka muke cewa sanda muna yara. Daada ta harare ni tace "dama ba bacci kike ba ko?" Nace "dan Allah daada Agadaz zamu? Wa muke dashi a Agadaz? Mommy ma da kanta tace bata taba zuwa ba saboda nisan garin? Daada me laifi na har ya kai girman haka?" Sai kuma kuka. Ina jin matar tana ta yiwa daada tambayoyi amma bata ce mata komai ba, aka kawomin abinci naki ci, daada ta dauko min magani na ta bani tasa lallai sai da na sha. Ranar sam banyi bacci ba, ga gajiya ga tunani, da zarar baccin ya daukeni kuwa zanyi ta mafarke mafarke, most of them na Sultan ne kuma duk basu da dadi. Daga karshe dai na tashi zaunr na hade kai da gwuiwa nayi ta rera kuka na. Babu abinda ba zan iya bayarwa ba a lokacin dan insan halin da Sultan yake ciki. Ni kaina ina tsoron zuciyarsa. Sai ya hargitsa garin Abuja gaba daya. Sai gab da assuba sannan nayi bacci, cikin baccin naga sultan a cikin gidan mu yana bi daki daki yana nemana, yana bude dakin mommy ta dauko bindiga ta harbe shi. Na farka a tsorace ina ta jero adduoi. Naji ana kiran sallah na tashi nayo alwala nazo na fara nafiloli ina ta jero wa Sultan addua, ni ban damu da kaina ba, duk abinda mommy zatayi min nasan ba zata taba chuta ta ba, amma shi bashi da kowa sai Allah. Mommy lawyer ce, zata iya creating case against him wanda dole alkalin ya dauke kansa daga ganin cewa dan sarki ne ya rufe shi, babansa kuwa ko dan yatsa ba zai daga ba ballantana ya damu. Hope dina kadai shine daddy, shi kadai ne zai taka wa mommy burki. Amma bansan shi kuma yadda zai dauki al'amarin ba, saboda shi daddy baka ta ba gane inda ya sa gaba saboda kwarjinin sa. Ana yin assalatu na tashi daada sannan na tayar da sallar, na idar ina azkar naji tana gayawa matar ta aika a samo mana mota shata. Karfe shida muka shiga motar, kawar daada ta hado mu da kunu da kosai wai ma ci a hanya. Motar hilux ce saboda sahara. Muna baya ni da daada kayan mu kuma suna gaba tare da driver. Tun karfe shida muke tafiya har karfe uku na yamma sannan muka tsaya muka yi Sallar azahar da la'asar muka cigaba da tafiya. Lallai Agadaz akwai nisa, nayi baccin har na gaji, nayi tunanin har kaina yana neman bugawa. Ko bishiyoyin ma babu, inka leka ta window yashi kawai zakayi ta gani babu iyaka. Daada tayi tayi dani inci abinci naki ci. Rabona da abinci tun wanda mommy ta takura min naci ranar da zamu taho. Mun daga nesa na hango garin. Babban gari ne babu laifi amma ko irin 'yan kauyukan kan hanya din nan babu kawai sai dai ka ganshi a gabanka a tsakiyar sahara. Muna shiga garin daada ta gaya wa drivern in da zai tsaya, ya tsaya amma maimakon inga mun fito sai naga mun zauna a mota muna jira, can sai ga wata katuwar Jeep ash color ta tsaya a kusa damu, wani saurayi ne ya fito ya kara so windon da nake yace "baki daga Nigeria?" Hausar shi tas kamar dan kano. Na dauke kaina kamar ban ji shi ba dan ni kowa ma haushi yake bani. Daada ce ta amsa masa da murmushinta tace "eh mune, mustapha ne ko musbahu?" Yayi dariya yace mata "Mustapha ne daada" ya kalleni yace "Hafsat ko Moon" ya sake bawa iska ajjiyarsa. Daada ta kama fada ni bama abinda take cewa nake ji ba, ya bude min kofa shima yana magana amma bana gane me yake cewa. Ina fitowa daga motar jiri ya debe ni sai kasa. Da sauri ya zo zai rike ni na daga masa hannu nace "Don't touch me" ni na manta ma 'yan Niger basa turanci, amma ga mamakina sai naga ya ja baya yace "just trying to help" daada ta zagayo da sauri ta rike ni muka tashi tsaye, muna tashi kuwa nayi mata wanka da amai, babu komai a cikin aman nawa sai ruwa. Sama sama nake jinsu suna ta yi min sannu. Daada tana cewa "bata taba yin tafiya me nisa irin wannan ba ne shi yasa, kai wannan gari naku da nisa yake" ni dai aka sakani a mota na kwanta ina jin dadin sanyin ACn motar. Ina jin alamar muna tafiya amma babu damar in dago kai in kalli gari saboda jirin da nake ji. Naji horn kuma naji an bude gate, daganan naji mun tsaya. Daada ta riko ni muka fito tare, inajin saurayin yana yiwa wata yarinya French sai naga tazo ta kamani itama muka shiga cikin gidan. A palo suka kwantar dani akan doguwar kujera. Mustapha ya sake aiken yarinyar sai gata da cup din tea mai zafi ta kawomin, na karba nace "graciers" na ringa kurba a hankali har sai da na sanye. Sai a lokacin na samu idon kallon palon. Yana da girma kuma an cika shi da kayan alatu, daga dukkan alama mutanen gidan basu da matsalar kudi. Daada ta shigo daga alama sallah tayi. Mustapha shima ya shigo daga masallaci. Nan aka nuna min inda zanyi sallah na shiga nayi. Daki ne babba da katon gado da wardrobe a ciki, sai toilet shina babu lefi mai kyau. Kayan mu na gani a dakin, anan kenan zamu zauna. Ina idarwa yarinyar ta dawo tayi min alama da ana kira na. A palon na tarar dasu suna cin abinci, daada da wata mata da maza samari su uku. Na karasa na zauna daga dan nesa dasu. Matar ta dago ta kalleni fuskarta a hade babu murmushi. Na gane ta. Aunty Zaliha. Kawar mommy ce tun muna yara, gurin aikin su daya da mommy. Tana zuwa gidan mu muma kuma muna zuwa gidanta tare da mommy, muna secondary school mommy tace mana sun tashi daga Nigeria amma sam bamu san Niger suka dawo ba ballantana insaka ran ganinta a agadaz. Tana da yara maza uku. Twins, Mustapha da Musbahu, sai kuma gambon su Musaddiq. Musaddiq shine sa'an Hafsat su kuma twins din sa'annin yaya Walid ne.
Chapter 74 · 0% Book details