← Book details Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 190

Sashe 73

Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Titi babu kowa dan haka mommy ta ke kwarara gudu san ranta, ta gaban palace muka wuce, na kalli gate din ina lissafin ko Sultan yana ciki? Na lumshe idona knowing this is the closest I can get to him. Airport muka je, a raina nace kasar zamu bari kenan gaba daya. Muna zuwa muka fito muka shiga waiting room muka zauna, ni dai bance musu komai ba, sai da aka fara kiran flight naji an kira Niamey sai naga sun mike, zuciyata naji tayi min fari kal, dan dai Niamey ai bani da problem, wato mommy gidan su zata kaini kenan, ina zuwa zan karbi waya a gurin cousins dina na can in kira daddy in kira Sultan. Na mike da kwarin jikina, amma ban saku fuskata ba dan kar ta gane ban damu da zuwa Niamey ba. Wata jaka ta miko min tace "ga magungunan ki nan kullum zaki rinka shan dai dai" na duba naga magungunan hawan jini nane, watk mommy tasan sai jini na ya hau shine ta dauki precautions. Na rungume ta ina hawaye nace "am sorry I failed you mother" ta dan shafi bayana kadan sannan tace "it's ok, Allah ya kiyaye hanya" daganan ko fuskata bata kalla ba ta juya ta fice daga gurin. A jirgi hankali na a kwance muke tafiya, ni ce har da bacci, dan nasan 'yan Niamey sosai dan haka bani da matsala. I will come back to Nigeria in less than a week. Hmm

11 na safe a Niamey tayi mana, muka dauko kayan mu muka fito, muna fito wa na fara wara idon ganin motar da zata dauke mu, dan nasan duk sanda muka je Niamey wani cousin din mommy ne yake zuwa daukan mu, babu shi babu alamar sa. Taxi naga daada tana tsayarwa, na karasa gurinta naji suna magana da mai taxi din da yaren da ban sani ba, abinda na fahimta kawaj shine kudin da ya gaya mata, kudi ne masu yawan gaske, ya fito ya fara zuba kayan mu a mota, nace "daada ina zamuje ne?" Tace "zaki gani ne ai" nace "daada ko ma ina zamuje mu fara zuwa gidan su Ahmodou mana mu gaisa, kinga sai mu huta acan" bata kulani ba ta tura keyata cikin mota sannan itama ta shigo. Tun muna tafiya ina gane titunan da muke bi har muka fara shiga inda ban sani ba, daga baya muka dau hanyar barin gari, ni maimunatu na shiga uku, ina zamuje ne? Ni in banda Niamey ban taba zuwa wani gari a Niger ba, na sake cewa "daada ina zamu je ne?" Direct tace min "Tahoua" na kwantar da kaina a jikin window ina kallon jefi jefin bishiyoyi suna wucewa, Tahoua, nasan sunan garin amma a iyakacin sani na bamu da 'yan'uwa acan. Lallai mommy da gaske take, na danyi murmushin takaici nace a raina 'tace bazan dawo ba sai na manta da Sultan. Bata san sai da ya dauke ni shekara biyar ba kafin in chire Ibrahim daga raina ba? Sultan kuwa nasan kuwa nasan zan tafi dashi ne a raina zuwa kabari na' a haka bacci ya dauke ni, can naji daada tana tashina, na dauka munzo ashe tsayawa mukayi sallah, cikin sahara, dan gurin da muka tsaya ko 'yan bishiyoyin babu, ni dai a tsorace nayi sallar na koma mota. Bayan mun kuma daukan hanya daada ta dauko wata food warmer da soyayyun kaji a ciki ta hado min da ruwa da lemo ta miko min, na diba na zubawa drivern na mika masa. Ni lemon kawai nasha dan sam bakina babu taste.
Chapter 73 · 0% Book details