Sashe 134
Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
jikinsa yake ba ne ba a mummurde, kina ji kuma rannan yace in ya kamani sai ya dake ni" Yaya tace "to ai tsoron nasa da kike ji ne ya saka ya ke miki hakan" ni dai dariya kawai nake yi mata, daga baya nace "kinsan abinda zakiyi ki daina jin tsoron sa? Shiryawa zaki yi mu tafi tare, in kina ganin sa kullum zaki saba dashi ki daina jin tsoronsa" tayi saurin girgiza kai tana zaro ido tace "in kin ganni a gidanki to yayi tafiya. Wai in tambaye ki, yana dariya kuwa?" A raina nace 'lallai Sultan wato tsare gida ne dashi a cikin 'yan'uwansa kenan, dan su Fa'iza ma tambayar da suka fara yi min kenan' nace "yana yi sosai ma, da kin shigo dazu da kin ganshi yana dariyar ai" tace "ban taba ganin sa yana dariya ba"mun jima muna hira da ita, anan na fahimci cewa cousin din sultan ce sunan ta Huda, tana secondary school bata gama ba, a gurin Yaya ta ke zaune. Sai bayan Magrib sultan yazo daukana, bai shigo ba kira na yayi yace in fito, nan kuma Huda ta fara nuna bata son in tafi, Yaya tace ta bari da weekend sai tazo min. Yaya ta saka aka zuba mana abinci a flask muka tafi dashi. Tun a hanya nake bawa Sultan labarin yadda muka yi da Yaya da kuma Huda, yayi dariya yace "tunda na dawo daga America yariyar nan take jin tsoro na wai na zama kato". Muna shiga palo na ajiye jakata ina kokarin in kira yara su dauko mana abinci a mota, sultan ya zagayo ta bayana ya dauke ni chak ya fara tafiya dani hanyar dakin sa, da mamaki nace "Sultan what are you doing?" Yace "It is pay back time" nace "ka manta yadda tsarin yake ne? Food, bath, and then it?" Yace "No, an chanza tsarin yanzu. Yanzu na samu abinda yafi food dadi, it will comes first, then birth and then food" mukayi dariya a tare sanda muka shiga dakinsa, kan gado ya kaini ya ajiye ni yace "fada min dame dame yaya ta baki" nace "ina ruwanka, sirri ne tsakanin mu" ya tashi yana cire kayansa yana kallona, nayi sauri na rufe idona, ina jinsa yana dariya, naji motsin sa ya hawo kan gadon, ya juya ni ya zuge zip din rigata, ban hana shiba amma ban bude ido na ba, ya zare rigar ya ajiye gefe, ya zare skirt underwear na shima ya ajiye, still naki bude ido na, ya kamo hannuna ya dora a kirjinsa yace "open your eyes" na girgiza kaina, yace "why?" Na hadiye yawu da kyar. Ya sake cewa "open your eyes and look at me" na dan bude ido na na kalleshi, ganin babu komai a jikinsa ya sa na saka hannayena na rufe fuskata, ya sake kama hannayen nawa ya dora a kirjinsa yace "it is OK, Daddy ba zai ce miki No ba Mommy ba zata yi miki fada ba" ya fara yawo da hannuna a jikin sa yace "kin gani baki kama da wuta ba. Nothing will happen idan kin kalle ni ko kin taba ni. I am made of flesh and blood like you, I am not made of glass or fire, in kin taba ni I will not crumble or break down, I drive as much pleasure when you touch me as I do when I touch you" ya cigaba da yawo da hannuna a jikinsa, ji na nake wani iri, ganin hannun yana tafiya wani gurin nayi sauri na kwace hannuna, yana dariya ya jawo ni muka zauna muna facing juna yace "you see?, it is perfectly alright. Try it" na dago hannuna na dora a kafadarsa na fara shafawa a hankali ina jin softness of his skin plus the hardness of his muscles, ya lumshe idonsa yana murmushi yace "do you feel that? Feels good, right?" Yes it does feel good amma ban fada ba, na cigaba da shafa jikinsa a hankali, tun yana guiding hannuna har ya barni na cigaba da kaina, sai da nayi iya yina sannan na dago na kalli fuskarsa, idonsa a rufe, fuskarsa tayi red, red lips dinsa sun kara ja, bakinsa slightly open, na kawo fuskata dai dai tasa na dora lips dina akan nasa na fara kissing dinsa a hankali, he let me, na dan sake shi naja baya kadan amma ko inchi biyu ban matsa ba ya jawo ni da karfi ya mayar da bakin mu ya hade, tun daga rikon da yayi min nasan yau kam sai yadda Allah yayi dani. Da safe bayan munyi sallar asuba mun koma, karar wayar sultan ce ta tashe mu, ya farka amma bai dauka ba har sai da ta katse, ta sake fara ringing yayi tsaki ya mike zaune sannan ya dauka, a hankali yace "abbas" a take naji baccin ya bar idona, ina jin su suka dan yi magana sai naji sultan yace "OK, zamu shigo an jima" ya kashe wayar ya ajiye ya rike kansa da hannu biyu, na tashi zaune ina jin ciwon jiki duk kuwa da cewa sai da na gasa jikina kafin in kwanta, na dafa shi nace "me yace Abbas din?" Ba tare da ya kalle ni ba yace "Takawa yana kiran mu wai in an jima" nace "ya dawo ne?" Yace "I don't even know ya dawo ma sai yanzu, maybe jiya da daddare ya dawo" ya mike ya shiga toilet. Ina lura dashi har muka zo yin break hankalinsa baya tare dashi, na hada masa tea na bashi amma naga ya zauna yana ta juya shi, na taso na zauna a cinyar sa dauki tea din ina bashi a baki amma still sha yake yi kamar mai shan magani. Sai da ya shanye sannan na ajiye cup din ina shafa fuskarsa nace "what's wrong?" Yana shafa bayana yace "bansan kiran da yake mana ba, bai taba kirana akan abin alkhairi ba" nace "amma dama ai zamu je mu gaishe shi idan ya dawo, tunda anyi bikin mu baya nan maybe albarka zai kira mu ya saka mana" ya danyi murmushin takaici yace "my Daddy is not like your Daddy, my Daddy baya saka min albarka. Am very sure there is something bad a wannan kiran" kawai nima sai naji zuciyata ta tsinke, haka muka shirya duk babu fara'a muka fita. Munayin packing ya fito ya bude min kofa, ina fitowa ya kama hannuna ya rike kam, tamkar wadda za'a kwace mishi ni, nayi kokarin kwacewa amma yaki shikawa, na kalli fuskarsa naga sam babu fara'a, ban taba ganin fuskarsa a haka ba. Muna tafiya mutane suna ta gaishe mu amma ko kallon inda suke bai yi ba ni ma kuma bai bani damar amsa gaisuwar ba saboda yadda yake jana da sauri. Wata katuwar kofa naga mun dosa, muna shiga na saki baki ina kallon haduwar gurin, hatta bangon gurin an kawata shi da zane irin na sarauta, ga manya manyan hotunan sarakuna nan generation by generation, ga bayi nan da dogarai a zazzaune suna ta gaishemu amma bamu amsa gaisuwar kowa ba, muka shiga wata katuwar kofar glass, nan babu kowa amma yafi inda muka baro haduwa, ni dai gabana sai faduwa yake yi kuma har yanzu sultan yaki ya saki hannuna. A bakin wata kofa naga ya tsaya, sai da yayi ajjiyar zuciya sannan yayi knocking ya tura kofar a hankali tare da sallama. Muryar mace naji ta amsa, ya bude kofar gabadaya. Yau ne ranar dana fara ganin Takawa ido da ido, yana zaune ya harde kafafuwansa irin zaman da sultan yake yawan yi, gabansa tray ne da fruits a ciki, fuskarsa babu annuri ko kadan a ciki, kallon fuskarsa kadai ya saka naji hanjin cikina ya kada saboda tsoro. Gefensa da dama Hajiya ce, fuskarta fal da fara'a kamar gonar auduga, kusa da ita saratu da fa'iza. Daga hannun hagun Takawa kuma Abbas ne kansa a kasa dan haka ban karanci tasa fuskar ba. Nayi kokarin karbe hannuna daga cikin na Sultan amma ya kara rikewa, ina kallon idon Takawa ya sauka akan hannayen mu sannan ya kalli fuskokin mu, nayi saurin sauke ido na kasa ina jin bugun zuciyata yana karuwa, a tare muka taka muka karasa gaban sa, muka durkusa a tare, Sultan ne ya fara gaishe shi sannan nima nayi yadda yayi, babu wanda ya amsawa a cikin mu, hakan ya kara sawa naji bugun zuciya ta ya karu, Hajiya ce tace "yaron kirki shiru kuma babu kai babu amarya?" Ko kallon inda take Sultan bai yi ba, na juya ina kokarin gaishe ta naji muryar Takawa kamar a tsakiyar kaina yace "Maimuna" nayi sauri na juyo jiki na yana rawa, kafin in amsa ya jefo min wata envelope gaba na yace "bude" ina kai hannuna zan dauka Sultan ya riga ni dauka ya zaro abinda yake ciki, ji nayi gaba daya jinin jikina ya kafe, wani daci ya taso bakina kamar mai shirin yin amai, hotuna ne a ciki, ranar da aka kawo ni gidan sultan, hoton farko Sultan ne a tsaye da kwalbar giya a hannunsa, gefensa Daniel ne shima da the same kwalba a hannunsa. Hoto na biyu Solomon ne yana mika wa Sultan bindiga, hoto na uku kuma nice, da bindiga a hannuna, sultan a tsaye a kusa dani ga Ibrahim a durkushe a gaban mu. Na kalli sultan naga bani yake kallo ba babansa yake kallo wanda shi kuma ni yake kallo, na mayar da kaina kasa na sunkuyar ina jiran abinda zai biyo baya, Takawa ya fara magana "babanki mutumin kirki ne, abokina ne, babu yadda banyi dashi ba akan kar ya hada auren nan amma ya dage sai ya hada. Na dauka kema mutuniyar kirki ce irin mahaifin ki, ashe ba haka bane ba" fada yake yi sosai yana daga murya. "Bindiga, a cikin gidana? Waye shi wannan da zaku harba din?" Sultan yace "It doesn't matter waye shi, kuma ba laifin ta bane, ni na bata bindigar, ko menene za kayi ni zaka yiwa ba ita ba" da tsawa Takawa yace "shut your mouth, ba da kai nake magana ba, ka sani ba tun yau ba, I don't care ko ma menene zakayi da rayuwar ka. Itama saboda nayi