← Book details Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 152 OF 190

Sashe 152

Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

tayi ciki, saurayinta yayi ya yaudare ta da sunan aure yayi mata ciki ya gudu, basa son zubarwa saboda suna gudun hukuncin ubangiji, kuma basa son magana ta fito saboda kar sunan zuri'ar su ya lalace. Shine suke son su hada shi aure da ita, za'ayi fake aure anan fadar, daga nan sai ace sun tafi kasar waje zatayi karatu, za'a tura ta dangin mahaifiyarta ta gama renon ciki ta haihu, shi kuma sai ya tafi wata kasar ya zauna a can, in ta haihu yaron yayi dan wayo sai a sake daura musu aure na gaskiya kuma amma a boye sannan sai su dawo a matsayin miji da mata da kuma dansu. Yana tuna yadda yaji zuciyarsa tana yi masa zafi kamar zata kona kirjinsa amma bashi da spirit din da zai yi musu, ranar kwana yayi yana kwana yayi yana kukan takaici amma da baban ya kira shi da safe zancen buga IV sai yace "to" yana ji yana kallo aka kakaba masa auren ta, both fake and real din, suka dawo gida kuma ya cigaba da zaman aure da ita ya kuma rike mata danta kamar yadda mahaifinsa yayi umarni da yayi. Ya dago jajayen idanuwansa yana kallon Yaya yace "yanzu da kuka saka ni na rike shege me kuke tunanin zai faru idan bana duniya, kuna nufin zai ci gadona ne ko kuma kuna nufin zai karbi masarautar nan be ya mulka?" Yaya ta girgiza kai tace "babu ko daya, babanka ai ba fool bane ba, ya rubuta a rubuce ya saka hannu cewa duk sanda babu ranka, Sultan shine magajin ka, idan kuma babu ran Sultan to wani daga cikin kannenka ne zai karbi mulki, yace bai yarda da duk 'ya'yan da zuwaira zata haifa ba, ya bada copy din takarda ga dukkan king makers na masarautar nan, maganar gado kuma kuma ya rubuta ya bawa alkalin da yake raba wa familyn nan gado cewa bayan ranka Abbas bashi da gadonka, amma abar maganar a secret, idan babu ran alkalin next alkali shi zai karbi takardar" ya jinjina maganar, his father is really something. Ya tuna da irin rikon da yayi wa Abbas, da irin rikon da Hajiya tayi wa Sultan, ya tuna maganar giyar data rika feeding Sultan kuma Yaya ta gaya masa amma yayi burus da maganar. Ya juya ba tare da ya ce da yaya komai ba ya fice, mota ya shiga ya karasa palace, su kansu masu bude gate basu gane shi ba motar kawai suka gane, direct part din hajiya ya wuce mutane sai kallon sa suke yi sai in sun gane shi suyi saurin zubewa a kasa. A bedroom ya same ta ta fito daga wanka tana shiryawa, bayinta suna ganin sa suka watse, ta juyo da sauri itama tana kallonsa da mamaki, baya shigo wa part din ta ita take shiga nasa part din. Ya tsaya yana kare mata kallo, how can he have marry this? Ya tuna da khairat, da rayuwarsu together, da sauri ya kawar da tunanin daga ransa dan gap yake da hawaye. Ya ce "how dare you? How dare you treat my son like this? Duk abinda nayi miki, duk rike miki danki da nayi amma ke shine kika wulakanta min nawa dan" da tsananin mamaki take kallonsa, cikin rawar murya tace "Ranka ya dade ban gane maganar ka ba? Wanne dan naka? Wanne dan nawa?" Ji yayi kamar yaje ya zabga mata mari amma yasan dukan mace ba girmansa bane ba, yace "kinsan maganar da nake yi ai. An hada ni dake tare da shegen danki na hada na rike ku tikon amana amma ke kika wulakanta min nawa dan, magaji na, me kike so kiyi archiving? Wato plan dinki shine ki lalata rayuwar yaro na yadda naki yaron zai gaje ni ko? Is that your plan? Ke kika zuga ni na kai shi Lagos gidan kangararru saboda kina so ya lalace, ke kuma kika zuga ni na kaishi America tun yana da shekara goma sha biyu a duniya, burinki ya zama tantagaryar dan iska yadda babu yadda za'ayi a bashi sarauta, abinda baki sani ba shine Allah ya fiki, Allah ya kare min shi burinki bai cika ba, kuma ki sani plan dinki duk a banza kike yinsa, babana daya hada auren nan dan ya rufa miki asiri ba jahili bane ba, yasan me yake yi, ya rubuta ya bayar cewa danki ba zai gaje ni ba, dukiya ko sarauta" da baya ta tafi ta zauna akan gado tana rike zanin jikinta, ta shiga uku ta lalace yau menene yake faruwa, me ya samu Sadiq yau kuma? Tunda akayi auren nan bai taba furtawa cewa Abbas ba dan sa bane sai yau, kuma bai taba kiran sultan da sunan dansa ba sai yau. Me ya faru? Ko ma menene ya faru tasan da sa bakin wannan munafukar matar ta sultan, dama tace tana reading minds yanzu haka ma matsafiyace tazo ta tsafe mata miji zata raba su. Cikin rawar murya tace "wacce magana kake yi ne haka yau kuma. Abinda duk akayi a baya baya wuce ba? Ya zaka taso da wannan maganar bayan ga 'ya'ya muna dasu" ya katse ta yace "ta yaya zan tabbatar da cewa su din ma 'ya'ya na ne?" Da sauri tace "wallahi 'ya'yanka ne, wallahi tunda muka yi aure ban kuma kallon wani namiji ba sai kai" ta durkusa a gabansa ta rike kafarsa, zaninta yana neman kwancewa yayi sauri ya dauke kansa, tace "dan Allah baban Abbas ka daina wannan maganar, ka rufa min asiri yadda Allah ya rufa maka naka" yace "ni kuma kika tona min nawa asirin ba? Ki gaya min abinda kika yiwa dana idan ba tonon asiri ba menene?" Ta dago kai tace "to amma dai ai sanda nace a kaishi lagos din baka musa min ba, kai ka fara wulakanta shi ai, me yasa dana ce maka kayi sai kayo ba za ka yi min musu ba? Ko sau daya baka taba nuna wa kana son yaron nan ba to ni menene laifina dan na taya ka kinsa?" Yasan anan kuma ta fishi gaskiya, amma ko kusa da yana cikin haiyacinsa ba zai bi shawarar ta ba. Ta fara share hawaye tana cewa "dan Allah mu bar maganar nan haka, yadda iyayen mu suka rufe ta to kar mu bude ta dan Allah" ya sunkuyo dai dai fuskarta yace "da ace kin rike min dana da mutunci, da babu wanda zai san waye Abbas, da ace kin kula dashi a lokacin da ni na wulakanta shi, da nima yanzu sai in cigaba da kula da naki dan, d'a na kowa ne amma kika nuna nawa ba naki bane ba, dan haka nima yanzu naki ba nawa bane ba" ya mike tsaye yana kallonta cikin ido yace "na sake ki saki biyu, amma in banda ni da waliyan mu babu wanda zai sani in kin ga dama, zaki cigaba da zama a dakunan ki tare da 'ya'yanki. Abbas kuma ki tattara shi ki kaishi gurin ubansa, ki sanar masa bani ne mahaifinsa ba, in ba haka ba ni zan sanar masa da kaina a fada" ya juya ya fice ba tare da ya kuma kallonta ba. Wani relief yake ji a ransa, ya yarda kwallon mangwaro ya huta da kuda. Hajiya kuma mutuwar zaune tayi a gurin, bata taba tsammanin abin yayi zafi haka ba, saki? Ita din? Da girman ta da komai? Yau wacce irin rana ce? Ita yanzu ta ina zata fara fadawa Abbas cewa shi shege ne? Yau ta shiga uku ta lalace. Ina fatan 'yan'uwana mata mun dauki darasi daga darasin Hajiya. Indai kika bari wani ya lalata ki to shi tafiyarsa zaiyi kamar baiyi komai ba, ke kuwa ke zaki kasance cikin takaicin abin har karshen rayuwarki, dan in kinyi aure ma kullum mijin zargin ki zaike yi. Ballantana ace kinyi cikin shege, in kin zubar alhaki a kanki, in kin barshi kin bar tambari har abada, shi kansa yaron har ya mutu ba zai ji dadin rayuwa ba, gori kullum, sai an tashi aure ma a rasa wanda za'a hada auren dashi tunda kowa yana son auren mai asali. Darasi na biyu kuma shine, d'a na kowa ne, in kika rike dan wata to kuwa tabbas za'a rike miki naki ko kina raye ko kin mutu. Ki sani zaki iya mutuwa a koda yaushe ki bar 'ya'yanki, za kuma ku iya rabuwa da mijinki ki bar 'ya'yan a gurinsa. Mu shuka alkhairi 'yan uwa, in mune yau ba mune gobe ba.
Chapter 152 · 0% Book details