← Book details Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 190

Sashe 30

Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Washegari da yamma muka fita shopping muka siyo kayan amfanin mu kaf, tun daga kan sutura, toiletries, cosmetics da sauran tarkace. Daddy tun yana biyan cash har ya dawo using credit card, daga baya yace "kai yaran nan so kuke kuga gudun ruwa na ko? To ya isa haka" mommy tana yi masa dariya tace "kai fa kace kar su taho da komai zaka saya musu anan, duk wanda ya sayi rariya kuwa ai yasan zata zubar da ruwa" ni da Hafsat dogayen riguna mommy ta sa muka dauka saboda zuwa makaranta, tace bata son shigar english wear, kar muga muna England muce muma mun zama turawa, mun dauki english wears din dai amma saboda sakawa a gida. Mun sayo sababbin sim cards muka saka a wayoyin mu muka cire na Nigeria muka ajiye. Nan muka fara kiran 'yan'uwa da abokan arziki muna basu numbers din mu. Kamar yadda nayi alkawari, Amira tana daga cikin na farkon dana kira.

A week after zuwan mu England aka fara maganar school din mu, ni dama daddy yasan me nake so, neurology, Hafsat aka tambayeta tace itama medicine din take so bangaren gynecology. Har daddy yace mu tafi sai nace "daddy, ina so kuma in dau some courses on psychology" yayi shiru kafin yace "anya Moon abin ba zai yi miki yawa ba? Medicine is not easy on it's own sannan kice zaki kara da wani abun kuma?" Nayi shiru bance komai ba, yace "OK, I will see what I can do, normally ba'a barin students su dau courses out of their field, amma tunda psychology is some how related to medicine zan nema miki" nayi godiya muka tashi muka tafi. Muna zuwa falon mu Hafsat ta fara tambayata "ke kuwa me yasa kike son yin psychology?" Nace "I want to know exactly what people are thinking, I want to be able to tell if someone is lying or not" tayi shiru sannan tace "is this about Ibrahim?" Nace "partly, yes"

Tunda muka koma England,duk sati sai na kira baba Habu maigadin mu na Abuja na tambayeshi ko Ibrahim yazo? Kuma duk sati amsar daya ce "bai zo ba tukun" rannan ina kiran sa kafin inyi magana yace "mai sunan daada" gaba na ya fadi nace "na'am baba" yace "indai har da gaske yana sonki zaizo, ni kuma in yazo zan bashi sakonki kuma zan kira ki in gaya miki yazo har in baki shi ma ku gaisa, idan kin ga bai zo ba, to ba son gaskiya yake miki ba ko kuma Allah bai kaddara alakar da take tsakanin ku mai dorewa ce ba, ki kwantar da hankalin ki, ki manta da batun sa, kiyi karatun ki" jikina naji duk yayi sanyi, kirjina yayi nauyi, nasan gaskiya baba Habu ya gaya min amma anya kuwa zan iya? Murya a sanyaye nace "nagode baba" daga nan ya kashe wayar.

Mun kama karatu sosai. Ita kanta makarantar abar kallo ce, dan zan iya cewa gari guda ce, with its ancient buildings, kowanne faculty kamar unguwa guda ne, dan saida daddy ya bamu maps yace muke tafiya dashi saboda kar mu bata. School of medicine duka muke ni da Hafsat, kuma first year komai tare za'ayi mana tunda kamar introductory courses ne, daga third semester kuma zuwa sixth kowa zai dauki individual courses din field dinsa, shekara ta hudu da ta biyar kuma zamuyi clinicals, kamar practical kenan inda zamu tafi asibitoci muna koyon aiki a gurin kwararrun likitoci, shekara ta shida kuma project. Tsarin makarantar tsari ne me kyau, lecturers dinsu sunsan me sukeyi, ga kayan aiki nan kamar banza, a raina nace dole a kira ta da second best university in the world.

Tunda muka fara lectures kawai sai naji nayi loosing interest a karatun, sam bana gane me akeyi. Ina shiga lecture hall zan tafi seat din baya in zauna in yi ta sake sake a raina ina tuno rayuwar sec sch din mu, sai inji gaba daya hankali na ya koma Nigeria. Sometimes sai inke ganin kamar a class din mu muke, Ibrahim zai iya shigowa anytime. Wani lokacin kuma sai inji kamar kamshin turarensa sai inyi ta waige waige. Duk sanda wani yazo yana son yayi min magana sai inji kamar Ibrahim yana kallona da lumsassun idanuwansa. It is like he is watching me. Sau da yawa in mun shiga lectures sai in kwanta inyi ta bacci har sai an gama sannan Hafsat ta tashe ni. Hafsat tayi fadan, tayi nasihar amma ina, sai da tace zata gayawa mommy bacci nake a class sannan na daina baccin amma still attention dina baya gurina. It is a million miles away. Only time da nake zama inji lecture sai a psychology courses dina. In homework aka bayar sai dai Hafsat tayi mana, kullum tayi ta min gori tana yimin bala'i amma bazan yi ba. It is as if spirit dina na karatu is gone.

A haka muka gama first semester, lokacin exams ma da kyar Hafsat ta tirsasa ni na danyi karatu tana koyamin wasu abubuwan. Hutun da aka bamu babu yawa dan haka daddy yace ba zamu je Nigeria ba, ranar har zazzabi nayi, mommy ta ga ciwona yana kokarin tashi ta kwashe mu muka tafi yawo banda daddy sai security daya hada mu dasu. Mune gari gari, duk garin da muka je sai mu samu hotel mu kwana, mune zuwa kallon London bridge, mune har Scotland da Wales. Na saki raina sosai nayi enjoying time dina.

Hutun mu yana karewa muka dawo gida. Muka cigaba da zuwa makaranta. Har yanzu bani da kawa ko aboki, in fact da yawa daga 'yan ajin mu basu sanni ba, wadanda duka sanni ma suna referring to me as Hafsat's sister, dan basu san suna na ba. It is like am afraid to get attached. Duk abinda akeyi daddy bai sani ba, tunda basu kafe result ba sunce sai at the end of the session. Mommy kuma tunda a gida ina nuna bani da wani problem itama bata taba tunanin ina da problem a karatuna ba. Ni dai kullum lissafin sanda zamu yi hutun session nake yi, dan wannan karon nayi alkawarin bincike zanyi sosai sai na nemo Ibrahim na gaya masa daddy yace bai damu ko wanne kabila ne shi ba, bai kuma damu da cewa he is not wealthy ba, gani nake yi hakan ne kawai zai saka ni in maida hankali na akan karatu na.

Second semester tana karewa aka fitar da result na both semesters din. Tunda Hafsat ta gayamin gaba na yake faduwa, nasan ban aikata abin kirki ba. Allah Allah nake mu tafi Nigeria kafin daddy yaga result dina in yaso in mun dawo ayi wacce za'ayi. Adduah ta bata karbu ba dan washegarin da aka kafe result muna main palo muna kallo sai mommy ta kira Hafsat tace muzo daddy yana kiran mu. Muna shiga palon su na san daddy yaga result dina. Bantaba ganin bacin rai a fuskarsa irin na ranar ba. Muna zama su yaya Walid suka shigo da fara'arsu, ganin yanayin fuskar daddy suma suka shiga taitayinsu. Muna zama ya jeho min takardar hannunsa yace "pick it up" hannu na rawa na dauka, yace "bude ki karanta a fili inji" nan na bude na fara karanta sakamakona. Tun daga first semester har second bani da B ballantana A. Mostly C ne har da D. Nan daddy ya fara fada, ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba, tun ina daurewa har na fara kuka. Yayi min wankin babban bargo mommy ta dora a inda ya tsaya. Su bakin cikin su shine sunsan ina da kokarin kawai karatun ne suke ganin banyi niyyar yi ba. Nan daddy yace dole ayi punishing dina akan abinda na aikata. Yace "punishment dinki shine, no holiday for you. Zaki zauna ke kadai a England ba zamu tafi dake Nigeria ba. Use the time to think about what you have done to your life. Sannan kiyi karatu so that you can catch up a inda aka barki a baya" daga haka ya mike ya shige cikin bedroom dinsa ya turo kofa

Episode Twenty Nine: The Message
Chapter 30 · 0% Book details