Sashe 163
Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
MAIMOON By Maman Maama Episode Eighty eight :Khairat Ta sake ni ta kama hannuna muka karasa kan kujera, ta zaunar dani sannan ta zauna a kusa dani still tana rike da hannuna, tana min murmushi from ear to ear, na dan sunkuyar da kaina saboda kallon da take min, ta saka hannu ta dago habata, tace "masha Allah, you my dear are very beautiful" naji kunyarta na sunkuyar da kaina. Ta dora hannunta akan cikina tana dariya excitedly, tace "wata nawa?" Ni dai duk kunya ta ishe ni, na kasa bata amsa, tace tana karkata kai "please kar ki yi min haka mana, talk to me, ki dauke ni kamar kawar ki kinji?" Na gyada mata kai, ta sake dora hannunta akan cikina tace "wata nawa?" Ina murmushi nace "almost four" ga mamaki na kawai sai naji babyn yayi motsi, itama taji a hannunta, ai kuwa murna kamar me, tace "shima yasan yazo gida, welcome home my little love" ni dai sai taya ta dariyar ta nake yi, sai da ta gama murnarta sannan tace "how is he?" Na san wa take nufi da he din, to amma na kasa sanin ta ina zan fara bawa uwa labarin danta wanda rabonta dashi shekara talatin? Jin bance komai ba yasa tace "ya kamannin sa suke yanzu" na dago kai na kalle ta nace "you just need to look in the mirror, he looks just like you" ta fadada murmushinta tace "but he has his father's built and temper" nace "yes, he do" ta sake juyo wa tana kallona tace "har yanzu yana da hot temper kenan? Sanda yana baby in yana son abu na hana shi sai yayi ta buga kansa a jikin bango, in na bashi abin ma daga baya sai ya karba ya jefar wai yayi zuciya" nayi murmushi, ta sake cewa "tell me menene yafi so duk duniya" na san me yafi so duk duniya amma am not going to tell her that, dan haka nace "food" ta bude baki da mamaki tace "har yanzu bai daina son abinci ba? Sultan har cikin dare yake tashi yaci abinci, sanda ina feeding dinsa sai da na hada masa da madara saboda tsabar cin sa, da ya fara yawo kuma babban abincin da yake so shine nama, daga nan sai fresh milk" nace mata "har yanzu ma, yana son nama sosai" tace "is he still making troubles? He was a trouble maker as a baby, yana da kiriniya sosai dan sanda ya fara crowling duk abinda nake so sai dai in dora a sama, a saman ma in ya samu abin takawa sai ya dauko, yayi ta faduwa yana jin ciwo amma sai ya koma" ina jinta ina ta murmushi a raina ina hango baby sultan yana ta kiriniya da wannan thick gashin kan nasa, tace "please tell me all about him, nuna min pictures dinsa in gani" na dauko waya ta na zare sim card din dan kada sultan ya kira, na kunna na nemo mata wani hoton sultan wanda yake looking very good and decent, na mika mata, tana karba tasa hannu ta rufe bakinta tace "Ya Allah, he is so grown up and handsome" sai kuma hawaye ya fara zuba a idonta "my son, my darling baby" daga hoton dana nuna mata maimakon ta dawo min da waya ta sai ta fara scrolling tana kallon pictures din mu, mostly na sultan ne da ni, sai few na yan gidan mu, in tazo kan wanda bata gane ba sai ta nuna min ta tambaye ni in bata amsa, har yanzu hawaye bai daina zuba a idonta ba, kuka take kuma tana dariya duk ita kadai, ni dai ji nake kamar in karbe waya ta saboda da akwai hotunan da bai kamata ta gani ba, amma ita babu ruwanta, kalli take yi kawai tana dariya, ta dago kai ta kalleni tace "he really loves you, I can already see it in his eyes" na gyda mata kai nace "yes, he does" sai can kuma ta ajiye wayar tace "oh dear, ko ruwa ban baki kin sha ba" nayi dariya kawai bance komai ba, hannuna ta kama ta jani har dakin da na fahimci cewa bedroom dinta ne, ni dai kawai kallonta nake yi, she is really beautiful and amazing, in ka ganta daga nesa ba zaka taba tsammanin babba bace ba, sai in kun zauna da ita ka kalle ta sosai sannan zaka ga shekarunta a fuskarta, jikinta kam babu alamar girma a tare dashi. Anan dakin nayi sallah, ina idarwa sai ga Hafsat tazo kirana in fito muci abinci, sai a lokacin na kalli Hafsat sosai, nace "yanzu Hafsat dama ciki ne dake baki gaya min ba" ta murguda min baki, nace "yanzu khairat din watanta nawa har zaki ji mata sibling" tace "ke watanki nawa aka haifi faruk? Ni wata na nawa aka haife ki? Me ya ragu a jikin mu? Ko wani mugun ciwo babu wanda yake dashi a cikin mu, itama khairat babu abinda zai same ta" na bita muka tafi ina tambayar ta "wai duk wannan gidan ita kadai take zaune?" Tace "sai ma'aikata, sai kuma 'yan'uwa duk wanda yake so zai iya zuwa ya zauna" ni dai har yanzu kallon gidan nake yi, Hafsat ta dan dakeni tace "kar ki bamu kunya mana, ke tsiya ta dake kyauyanci" muna zuwa dining naga an cika shi da kayan abinci, nan take kwadayi na ya tashi, ina zama Ummee ta taso ta fara serving dina, komai sai da ta zuba min tace dan ni ta dafa dan haka komai sai naci, yi take kamar zata bani a baki, ni kuwa na saki jiki nayi ta zurin abinci, sai kuma naji ina missing sultan, ina ma dai yana gurin nan da sai dai a dauke shi saboda yawan abincin da zai ci. Muna gama ci Hafsat tace min ta kai min akwatina dakin da take, nan take Ummee ta bata rai tace zayed yaje ya dauko ya dawo dashi dakinta, tace yau a gado daya zamu kwana babu mai raba ta dani. Bayan mun tattare gurin muka tashi muka zagaya gidan, ita take tayi mana bayanin ko ina na gidan. Kafin mu gama na gaji sosai, dama ga gajiyar hanya, muna shiga mukayi sallama da Hafsat muka tafi dakin ummee, ina zuwa tace min inyi wanka inyi sallah sai in kwanta, ai kuwa hakan nayi dan Sallar da kyar nayi ta dan idona har rufe wa yake yi saboda bacci, amma ina kwanciya sai na tuna sultan, na tabbatar yau ba zai yi bacci ba, bana nan kuma na kashe wayata ballan tana ko murya ta yaji. Nima sosai naji ina missing dinsa, kamar in dauki wayata in kira shi kuma sai na daure zuciya ta, na runtse idona ina addu'ar bacci yazo amma ina, Sultan kawai nake so. Ranar ba karamin yaki nayi ba kafin in samu bacci ya dauke ni. Ban farka ba sai kusan assuba, na tashi zaune naga ummee a kusa dani tana bacci, abinda ya fara fado min a raina shine sultan, ko zai iya tashi sallar asuba yau? Dan nasan ba bacci zai yi ba kar yazo kuma yayi missing masallaci. Na tashi nayo alwala nazo na dauki alqurnin dana gani a gurin sallah na fara karantawa a hankali dan kar in tashi ummee, har sai da naji anyi assalatu sannan na tashe ta ni kuma na tayar da sallah. Da safe duk jikina babu dadi, na dauki waya ta da niyyar kiran sultan yafi a kirga ina ajiyewa, daga karshe dai na bawa Hafsat sim card dina nace to nace ta bani kar ta bani, tana dariya tace "ai kuwa ba zan baki ba ko zakiyi kukan jini". Tare muka shiga kitchen da Ummee, she is an amazing cook, muna aiki muna hira, nan na bata labarin cewa kafin inyi aure ban iya girki ba, sai daga baya na koya, ai kuwa tayi min alkawarin sai ta mayar dani kwararriya a girki. A kitchen din muka zuba abincin a kwano daya muka ci, ban san me yasa ba kawai naji na saki jikina da ita, ji nake yi kamar dama can nasan ta all my life. Bayan nayi sallar azahar, ina zaune a dakin ummee ina tunanin ko me sultan yake yi yanzu? Sai ga ummee ta shigo, ta samu guri ta zauna a bakin gado, na dan juyo na kalleta tayi min murmushi. Tace " maimunatu so nake ki bani labarin sultan, tell me all about him, I want to know everything bana son ki boye min komai" na gyara zama na ina tunanin ta ina zan fara ne, she is his mother, she deserves to know everything. Nan na fara daga labarin da Takawa ya bamu na abinda ya faru bayan an dauke ta daga gidan, na gaya mata abinda sarki abdallah yayi, tun anan ta fara sharar hawaye, na dora da bata labarin rayuwar da sultan yayi tare da mahaifinsa, ban boye mata komai ba har zamansa a gidan kangararru da rayuwarsa a America, na gaya mata past drinking habit din sultan amma na tabbatar mata cewa yanzu ya daina, amma ban gaya mata dalilin fara shan giyar tasa na, na gaya mata haduwata dashi da yadda Daddy ya dauko shi ya dawo dashi gidan mu, amma ban gaya mata kiyayyar da Mommy tayi masa faga farko ba, na bata labarin auren mu da kuma sanadin karyewar asirin Takawa zuwa halin da muke ciki a yanzu, na dora da cewa "Sultan is emotionally not stable, shi yasa yaki zuwa, har yanzu kullum yana tunanin cewa mutane basa sonsa, da kyar ya yadda cewa Takawa yana sonsa da gaske, kema kuma yana tunanin ba sonsa kike ba saboda yana ganin kinyi abundaning dinsa tsahon shekaru baki taba neman sa ba, he is just scared to get his heart broken" bata cemin komai va saboda kukan da take yi, ta tashi ta fita daga dakin. She needed to be alone and I understand. Har bayan la'asar ban kuma ganin ta ba. Zayed yazo ya dauke mu ni da Hafsat muka tafi yawo, ya nuna min birnin Riyadh, garin ya hadu fiye da tunani na, lallai larabawa karshe ne gurin dukiya, ga tsari ga doka. Da magrib muka je