Sashe 171
Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Episode Ninety Two and Three : Maldives 1 and 2 Riyadh; Three weeks after the gender reveal party. Sosai Takawa ya putting pressure a kan sultan, sultan ya kara saka ni nayi wa Ummee magana amma wannan karon ko kallon kirki ban samu daga gareta ba. Sai ma ce min tayi in gaya wa wanda ya turo ni yazo ya same ta da kansa. Sam yanzu sultan bashi da cikakkiyar nutsuwa, yana son komawa gurin babansa kuma baya son ya bata wa ummeen sa rai. Ina yin iyakacin kokarina gurin kwantar masa da hankali amma nasan sultan is a busy person, zaman banza da rashin aikin yi shi yake irritating dinsa, duk da ya samu Ahmad sun kulla abokantaka, kullum zai zo ya dauke shi su fita amma hakan is not enough for sultan. Yanzu har ya kai matakin in Takawa ya kira sultan sai yaki dauka, he is out of excuses. Rannan ina shiryawa zan shiga gurin Ummee sultan kuma yana kwance akan kujera ya rufe idonsa, nasan ba bacci yake ji ba, sai da na gama shiryawa sannan na durkusa a kusa dashi na hura masa iska a fuskarsa, ya dan bude ido yana kallona, nace "zan shiga gurin Ummee" ya mayar da idonsa ya rufe yace "zan shigo an jima" na tashi na tafi jikina babu dadi, bana son ganin sultan cikin damuwa sam, sai inji duk nima na shiga damuwar. I must do something about this. Ban sha wahalar hada sultan da ummeensa dan in cigaba da ganinsa cikin damuwa ba, amma kuma menene abinyi? A harkar da ta shafi iyaye dole mutum yayi taka tsan tsan. A bedroom na sami Ummee tana zaune a kan gado da system a gabanta, na shiga da sallama, ta amsa min idonta akan screen din system din, sannan tayi min alama da hannunta na inzo in zauna kusa da ita, ina zama ta juyo min da screen din system din, fuskarta dauke da murmushi tace "what do you think of this?" Na kalli abin da take nuna min, model ne na dakin baby, with complete furniture, crib, drawers, night stand da komai, dakin yayi kyau sosai, amma kuma sultan ya gama tsara mana baby room din mu tun sanda yake zana plan din gidan mu a Abuja. Na kasa bawa Ummee answer, ta cigaba da magana "ina tunanin bedroom din tsakiya ba part dinku za'a mayar baby's room, sultan sai yayi mana dan renovating dinsa kadan, yayi closet a ciki, sai mu fara order kayan baby kuma, furnitures first, sai electronics sannan sai mu dawo kan clothings" tayi ajjiyar zuciya, "we have alot to do, list ya kamata mu rubuta..." Sallamar sultan ce ta katse mata maganar ta, muka amsa masa a tare, yana kallon mu yace "yau hirar ta daki ce kenan" ta dan bubbuga kan gadon kusa da ita tace "come Abubakar, sit with us" ya karaso ya zauna yana satar kallona, tace "we were just talking about the baby, baby room muke so mu fara shiryawa, muna bukatar taimakon ka gurin renovating dakin babyn" ya dan dafe kansa kamar mai ciwon kai yace "Ummee babyn nan fa yana da atleast wata uku kafin yazo, besides already yana da room dinsa a Nigeria" take naga murmushin fuskarta ya kau, tace "Nigeria? I tot I made myself clear cewa babu zancan komawa Nigeria ko?" Sultan ya bata rai, he has reached his limit. Ya saka hannu ya dauko wayar sa yana dialing, kawai sai gani nayi ya ajiye ta akan table din gaban gadon, tana kara sai kuma mugaji an dauka, muryar Takawa, yace cikin fada "Sultan wato ina ta kiranka shine kaki dauka ko? Wannan wanne irin aikin vanza kake aikatawa haka? Kawai ka dauki iyalinka ka tafi dasu can wata uwa duniya ku zauna a can? Zaman me kuke yi har yanzu? Aikin da ka bari wa zai yi maka?" Sultan yayi gyaran murya yace "barka da yamma" Takawa yace "bazan amsa ba, me ya hanaka dawowa har yanzu?" Sultan yana kallon Ummee yace "bani na hana kaina tahowa ba, Ummee ce tace bazan dawo Nigeria ba a Riyadh zan cigaba da zama, na saka ka a speaker phone yanzu tana jin abinda kake cewa, sai kuyi magana a tsakanin ku" na kalli fuskar Ummee naga wani missed emotions, sama sama take numfashi, ta kasa magana, sultan ma ita yake kallo ita kuma wayar take kallo. An jima a haka sannan Takawa yace "Khairat, kin san dai bai kamata kice zaki hana yaron nan dawowa gidan su ba ko?" Ta hadiye yawu ta kara bata fuska tace "why not? Nan ma ai gidan su ne, kamar yadda yake da iko da gidanka haka yake da iko da nawa. Kamar yadda kake da iko dashi haka nima nake da iko dashi, in fact na ma fika iko dashi, nace ba zai dawo ba and that is final" yace "you can't do that. Aikin sa kuma fa?" Tace "wani zan samar masa anan" yace "'yan uwansa kuma fa da suke ta nemansa anan me kike so in ce musu? Mutanen gari fa da suka dogara dashi me kike so in ce musu? He is a Prince for God's sake khairat, he has a role here, ko anan ma zaki samar masa matsayin Prince din ne?" Tace "bazan mayar dashi Prince anan ba amma zan bashi rayiwa fiye da wacce zaka bashi a matsayin Prince din, zancan me zaka gayawa mutane kuma oho, that's your problem not mine, abinda na sani shine dana yazo gurina kuma babu abinda zai kuma rabani dashi sai mutuwa" ya kwantar da murya Yace "khairat wannan maganar tsakani na dake ce, ki bar sultan ya taho tare da iyalinsa, kin san dai halin da moon take ciki, she needs her family besides her, in yazo sai mu taho tare dani dashi mu zauna muyi maganar sosai" ta danyi dariya tace "am not a kid ballantana kayi min wayo, Maimunatu will remain here ita da abinda yake cikinta, idan family dinta suna son ganinta da kansu zasu taho nan su ganta, ai dama aure babu inda baya kai mutum, aure ne ya kawo ta Riyadh, kuma babu wata care da zaku bata a can wadda bazan bata a nan ba" yace "amma dai kinsan nima ina da right akan su ko? Yanzu abinda za'ayi tunda sunyi wata biyu a gurinki, ki turo su suyi wata biyi ana sannan sai su take dawowa, kinga shikenan kowa will spend sometimes with him babu wanda zaice an cuce shi" tace "wata biyu? Cuta? You must be joking, sai da yayi shekara talatin ban ganshi a idona ba, how can you tell me wata biyu? In so kake a raba sai ka bari in yayi shekara talatin anan sannan ya koma gurinka" da sauri yace "shekara talatin? Do you think zan kara shekara talatin a duniya? Me yasa kike nema ki zamo mai son kanki ne?" Tace "son kai? Ai sai dai inyi maka wannan tambayar, tunda har ka iya bugo waya kace masa ya koma gurinka, saying you will let him come back again, bayan you don't keep your words, you will keep me waiting and waiting till eternity" ya danyi shiru da alama maganar ta shige shi sannan yace yace "am sure sultan ya gaya miki duk abinda ya faru bayan rabuwar mu, so am sure kinsan ba wai a sona na barki zaman jira tsahon shekaru ba" tace "that's your problem" yace "yes, it is my problem amma let me ask you something, ke menene ya hanaki zuwa kiga dan naki har tsahon shekaru talatin, ki kina son kice daure miki kafa akayi duk tsahon shekarun nan, baki damu dashi ba tunda har baki neme shi ba" nan da nan hawaye ya taru a idon Ummee, ni dai ina zaune sai in kalli ummee in kalli wayar, sultan ya mike tsaye yace "wait, all of you, ya ishe ku haka. All of you are forgetting something, am not your little love anymore. Am not a toy da zaku ke playing around with har kuna lissafin zaku ke passing dina around for one one month or one one week. Wannan duk maganar da kuke is between the two of your, dani da iyalina ba zamu kasance in the middle of it ba, ba zamu zama ball ba balle wannan ya buga ya bawa wannan ya buga. We will go away. Duk ranar da kuka yi settling kanku just give us a call sai mu dawo, amma ku tabbatar a cikin settlement din babu zancan muje gurin wannan sannan mu sake komawa gurin wannan, we are not toys, we are our own people" ya mika min hannu na kama ya daga ni tsaye, babu wanda yayi magana a cikin su sai Ummee data fara ruwan hawaye, yace "daddy wannan waya tace kuke fada a cikin ta, kana iya kiran wayarta sai ku cigaba a fadan acan" Takawa yace "sultan listen to me, kar ka dauki yarinyar mutane da ciki kana yawo da ita gari gari, zanzo Riyadh din, we will talk thi gs out" sultan yace "in kun gama talking things out din just give us a call" ya kashe wayar yana kallon Ummee, ita din ma shi take kallo, ba tare daya ce mata komai ba ya ja hannuna da sauri muka fita. Muna shiga part din mu ya zarce bedroom ya fara fito da kayan mu yana zubawa a kan gado, sannan ya jawo akwatina yana jerawa a ciki, hada wa kawai yake yi da nawa da nasa baya ware wa. Ni dai kawai ina tsaye ina kallon sa, nace "are we really going?" Yace "yes, and don't try to talk me out of it" nace "i won't. Amma ina zamuje?" Bai kalle ni ba yace "am not stupid, so kike in gaya miki ki gaya mata ko? But know one thing, ba America zamu je ba saboda can ne inda Takawa zai fara neman mu. In sun gama fadan zamu dawo. Zamu bar wayoyin mu a bude yadda zamuke magana dasu" nace "idan haihuwa ta kama ni a can kuma fa, mu kadai ya zamuyi?" Yace "a haka suka haife ni su kadai. And believe me, ba zasu kai har lokacin haihuwarki basu shirya ba,