← Book details Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 190

Sashe 43

Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Tun dana tashi da assuba ban koma bacci ba, muna ta hidimar kamu da mother's eve da za'ayi yau. Sam na manta da wani Sultan duk da jiya da daddare da kyar nayj bacci ina ta tuna abubuwan da suka faru a tsakanin mu. Anyi taro lafiya an gama lafiya babu wata matsala sai rigimar da akayi da Hafsat akan ita fa lallai ba za'a zuba mata nono aka ba, sai da aka rirriketa kamar mai aljanu sannan aka zuba mata, dan muguntar hajja kwarya guda ta juye mata. Mu dai muna ta dariya. Hajja ta juyo tace min "in naki yazo wanka zanyi miki dashi" Munir kam ya zamar min tamkar jela, cikin mata ko cikin maza duk inda nayi sai ya bini kuma sai yayi maganar da zata sa a gane akwai wani abu a tsakanin mu. Washegari da wuri jirgin su Zayed ya sauka shida abokan sa guda biyar, sai Waliyansa su uku. A ranar ne kuma zamuyi dinner da daddare, Zayed ya kawo mana kayan da zamu saka ni da Hafsat, dogayen riguna ne masu kyau, wadanda kuma suka rufe mana jikin mu ruf, iri daya ni nida ita sai dai banbancin color, ta Hafsat golden tawa cream. Ni samun wannan rigar yasa duk na manta da dinkin mu a gurin tailor ni da Amira wanda da muka yi niyyar zamuyi anko ni da ita. Ban tuna ba sai da muna shiryawa ta kira ni tace gata nan zuwa. Ai kuwa ina gaya mata ai ban karbo ba ni na samu wasu kayan ta hau bala'i daga karshe ta kashe wayar gaba daya. Nima nasan ban kyauta mata ba amma abubuwa ne suka yi min yawa shi yasa. Har muka gama shiryawa muka tafi Amira bata zo ba, nayi ta kiran wayarta kuma bata dauka, a karshe na hakura na rabu da ita.

Sultan

A hankali suke bin address din har suka zo gidan. Suna yin packing Amir yace "to munzo, now what?" Sultan ya dan sosa kansa yace "ya akeyi in anzo gurin budurwa?" Amir yayi tsaki yace "ideally kiranta zakayi a waya, to tunda kai baka da number dinta sai ka nemi yaro ka tura shi ya kirata" Sultan ya bude kofar mota ya fito yana ta zagaye ya rasa dan aike, sai da kyar ya samu wani yaro yace masa ya shiga yace ana kiran Hafsat, can yaron ya dawo yace "wai ance babu Hafsat anan gidan" ya juya suka dubi juna shida Amir, Amir ya kyalkyale da dariya yace "sai kazo mu tafi ai, yau dai ka barni inyi bacci tunda ka tabbatar yarinyar nan tayi playing dinka" sultan ya juyo jiki ba kwari ya shiga mota, har zaiyi mata key sai kuma ya dakata yana tunani, can yace "no, bazan hakura ba, tunda har tayi min kwatancen nan gidan to inhar ba gidan su bane ba to gidan 'yan'uwansu ne, ko kuma gidan su kawarta, yes, zan jira inga wanda zai fito daga gidan in tambayeshi ko ya santa" Amir binsa yake da kallo har ya gama sannan yace "you are not serious are you? Kana nufin zama zamuyi tayi a gurin nan har sai wata ta fito mun tambayeta? What if babu wanda ya fito har gobe?" Sultan yace "then I will wait har gobe, in kaga ba zaka jira ba kayi tafiyarka ban hana kaba" tsaki Amir ya sake yi ya kwantar da kujera tare da kunna kida, Sultan kuwa ya fito ya jingina da jikin motar idonsa na kan gidan. Shiru2 har wajan awa daya babu alamar wani zai fito, kuma unguwar shiru babu motsin mutane ballantana su nemi wani information. Amir har yayi baccinsa amma sultan yana tsaye kamar soja. Wannan shine kadai link din da yasan zai same ta dan haka ba zai yi wasa da wannan damar ba. Can kawai yaji motsi daga ciki, sannan yaga an bude karamar kofar gate din. Wata budurwa ce ta fito, doguwa, baka kyakykyawa. Taci kwalliya irin ta kure adaka dinnan, daga gani kasan gidan biki zata je. Suna hada ido da sultan ta danyi baya alamar tsorata sannan kuma ta maze ta rufe kofar tana gyara mayafin ta. Sultan ya karasa kusa da ita yace "Assalamu Alaikum" ta juyo ta watsa masa harara tace "alaikassam, ya akayi" kut, wannan badan information yake nema a gurin taba da sai ya babballata. Ya daure yace "please, wata ce ta bani address din nan gidan tace gidan su ne, sunan ta Hafsat" Amira ta sake yi masa kallon wulakanci tace "ko wacece karya tayi maka, nan babu Hafsat, oyo san inda dare yayi maka" lallai wannan yarinyar bata san hali ba. Daga bayansu suka ji ance "Hey, who do you think you are ana miki magana kina yiwa mutane rashin kunya, da wata mummunar fuskar ki anan, ko ki bashi amsar tambayarsa ko kuma wallahi.. " ta katse shi "ko kuma me Amir? Zaka dake ni ne?" Mamaki ne ya ishe shi yadda ta san sunan shi kuma ta mayar masa da magana ba tsoro. Har ta juya zata tafi Sultan ya sake binta "please, ko cikin kawayenki babu wadda kike tunanin zata bada address dinki?" Kamar ba zata kula shi ba sai kuma ta juyo fuskarta da murmushin mugunta tace "ya kamanninta yake?" Da sauri sultan yace "fara, fulani, very beautiful, tana da dimples manya guda biyu" murmushin mugunta Amira ta sake yi, Amir ya karaso yace "so? Do you know her or not" ba tare data kalleshi ba tace "shut off" Amir ji yayi kamar ya gaggaura mata mari, ko ba yau ba sai ya koya wa yarinyar nan hankali. Ta kalli sultan tace "na gane ta, yanzu ma tana gurin bikin da zanje" wata ajjiyar zuciya Sultan yayi yace "to shigo mota mana mu tafi" ta girgiza kanta tace "no way zan shiga motar ku, Allah ya raba gatari da saran shuka, in kuna son ganinta ku biyo ni" daga haka ta juya tayi gaba. Da sauri sultan ya koma mota ya tayar yana ta yiwa Amir horn dan yayi sauri ya shigo, Amir kuwa bakin ciki ne ya cika shi, wai ba zata shiga motar su ba, wacece ita?. Haka suka yi ta bin Amira a baya har ta fita titi ta samu taxi ta shiga, suka cigaba da bin taxi din har Sheraton. Amir yayi tsaki yace "maimakon kawai tace mana Sheraton, sai ta saka muka ringa binta a baya kamar wasu yaranta. Wannan budurwar taka should better be worth this in ba haka ba akanka zan huce" Sultan yace "believe me, she is worth morethan this" suna fitowa Amira tayi musu nuni da hall din da ake taron tayi shigewar ta ta barsu.

Moon

A matsayina na kanwa kuma babbar kawar amarya nice na ke zaune a kusa da ita a high table, sai Zayed da babban abokin sa Hamad. Ana cikin tsakiyar taron na hango Amira ta shigo, sai da ta gama shawaginta suna gaisawa da mutane sannan ta karaso high table, nan nayi introducing dinta a gurin su Zayed sannan muka dauki hotuna. Sai da muka gama sannan tazo dai dai kunnena tace "I brought a gift for you. Saboda bari na da kikayi babu kayan sawa yau" har ta juya kamar zata tafi nace mata "what gift?" Tace "Sultan, yana bakin kofa" nayi sauri na kalli hanyar shigowa, ga mamaki na kuwa sai naga masu gadin kofar suna ta hayaniya, har mutane sun fara tsayawa kallo. "Damn you Amira"

Episode Thirty Eight : The Shadow
Chapter 43 · 0% Book details