← Book details Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 164 OF 190

Sashe 164

Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

gidan su Zayed na gaishe su, sun karbe ni sosai a matsayin kanwar Hafsat, Zayed yace mu bar Khairat ta gaya musu da kanta when she is good and ready. Muna komawa gidan Ummee muka same ta ita kadai a zaune a palon ta, akan kujerar dana sameta jiya, idonta akan kofa, na lura ta dan rame kadan akan jiya. Muna shigowa tayi mana murmushi, tace tana kallona "na dauka kin gudu" na karasa da sauri nace mata "I will never" . Da daddare sai ka wayar sultan a wayar Hafsat, ta nuna min screen din, na daga kafada, ta dauka da sallama, daga ganin yadda Hafsat take yamutsa fuska nasan masifa yake mata, sai da ta barshi ya gama sannan tace "kana magana da Hafsat ne ba da maimuna ba" sun jima suna ta rigima daga alama cewa yake ta bani wayar ita kuma taki, da ta gaji ta kashe wayar tana kallona "he is really pissed off, yana neman ya kashe min dodon kunne" and my heart went out to sultan, yana can nasan ya hargitsa gidan mu gaba daya, poor Amir shi zaifi kowa dandanar zafin sultan. I hate hurting sultan amma shi zuma ne sai da wuta, he will never come to his mother in ba haka nayi masa ba. Duk hirar da muke yi Ummee tana jin mu amma tayi shiru, she seems deeply in thoughts. Sai bayan munyi sallama da Hafsat naje nayi shirin kwanciya na kwanta ina ta tunanin sultan sai gata ta shigo, ta zauna a bakin gado tana kallona tace "yana son yasan abinda ya hanani zuwa wajansa ko? Yana son yasan ko ina sonsa ko bana son sa? To ga labari zan baki ki gaya masa" na tashi zaune na jingina da jikin frame din gadon ina sauraron ta. Tace "bayan an dauko ni daga Nigeria, ban taho da komai ba, babu miji babu da, bani da ko hoton sa, daga ni sai kayan bacci a jikina sai abaya da hijab, babu wanda zai gane halinda na shiga a lokacin sai uwar da aka raba da mijinta da kuma dan karamin danta, suna farkon duniya ita tana karshe. Nayi kuka kamar raina zai fita, gaba daya family aka taru a kaina telling me cewa na basu mamaki, na zubar musu da mutuncin su a cikin jama'ar, saboda ba karamin abun kunya bane ace 'yarka budurwa ta gudu da saurayi, kowa abinda zai fada daban. Gashi an samu matsala da familyn wanda aka yi niyyar hadamu aure da shi. Aka sake sakani a daki aka rufe. Babu abinda yayi keeping dina alive a lokacin shine maganar sadiq da yace he will come for me, so I waited, not patiently but I waited. Kwana daya sadiq bai zo ba kwana na biyu shiru, a kwana na ukun ina dakina ina aikin dana saba wato kuka sai ga ummina tazo tayi kirana, ina zuwa palo na samu babana da uncle dina a zazzaune, na gaishe su sai suka miko min takarda suka ce daga Nigeria, da sauri na da bude ina so inji labarin Sadiq da Sultan amma me zan gani, wasika ce daga Sadiq cewa ya sake ni, bai yi stating dalili ba kawai dai ya sakeni, in his own handwriting, after all what we went through together, after irin rabuwar da mukayi da kuma irin alkawarin da yayi min cewa he will come for me, amma abinda na samu daga gare shi shine saki. I list everything, the trust of my family, my dignity, my husband and my son. I was totally broken. Na shirya akan lallai sai naje Nigeria na tambayi sadiq dalilin da yasa yayi min abinda yayi min, kuma in karbo dana, amma family na suna ganin yin hakan bashi da amfani, ya wulakanta ni ya yaudare ni ya rabani da iyayena, sannan kuma ya sake ni, to me zanje inyi masa kuma, sunce matsoraci ne shi, nusari wanda ba zai iya fighting for his family ba. Na nuna musu ni ba ta sadiq nake yi ba ta Sultan nake yi, amma still suka hana ni xuwa, abinda ummi na tace min shine inna je ma ba bani shi zasuyi ba, kuma nasan gaskiya ta fada ba zasu bani shiba, ta gaya min cewa inna dauko shi ba taho dashi gurina what kind of life zan bashi a matsayin dan mace babu uba? Duk abinda mutane suke fada akaina cewa yawon banza na tafi sai su tabbatar kenan in suka ganni da 'da babu uba, tace duk tsahon shekaru sultan shi zai neme ni da kansa. Duk na nuna musu kamar na yarda amma suna sakin jiki dani na gudu, unlucky for me wani friend din babana ya ganni a airport ya kira waya ya fada, aka zo aka sake mayar dani gida, nan take magana ta fara fita a cikin mutane, cewa khairat 'yar faisal abdallah ta fara yawon banza, ance na gudu da saurayi shekara uku sannan aka samo ni, fada da nasiha babu irin wadda ba'a yi min ba amma ni hankali na yana Nigeria, na gwada guduwa yafi a kirga, daga baya family na suka hadu suka yanke shawara, aka yi bannin dina daga fita daga kasar saudiyya gaba daya, ko baje airport da zarar anyi thumb printing dina shikenan ba za'a barni in shiga jirgi ba. Tun daga lokacin har yau ban taba taka kafata outside Saudi Arabia ba. I tried everything i can to get to sultan, I wrote him letters but they all turned back. My family made sure sunyi cutting duk wata hanya da zanyi contacting Nigeria. Su a ganinsu gurin sadiq nake son komawa, inna yi musu maganar sultan sai suce min zai neme ni da kansa. Da addu'ar da nasiha na fara hakura da zuwa Nigeria, amma ko dai da rana daya ban taba dauke hankali na daga kan sultan ba. Na yadda da abinda ummi na take gaya min cewa sultan zai neme ni da kansa, saboda nasan da ya fara hankali zai fara neman ina mahaifiyarsa take, kuma nasan Sadiq zai gaya masa labari na kuma nasan zai neme ni. I waited years in and years out amma shiru. Babu irin abinda ba'a yi min ba akan inyi aure amma naki, ba wai sadiq nake jira ba, bana son sultan yazo ya tarar na sake wani family din, kar yayi tunanin na manta dashi ko bana sonsa, I stayed alone for him, very lonely. Ina kallon 'yan'uwana maza da mata kowa yana yin aure yana barin gida amma ni naki inyi aure. Ina ta lissafa shekarun sultan, lokacin da na san cewa he is old enough ace ya mallaki hankalinsa ya fara nema na, a lokacin na kara saka ran zuwanshi, ban taba tsammanin cewa dana bai ma san wacece ni ba, ban taba tsammanin Sadiq ya manta dani ba. Da shekaru suka ja sai na fara tsoron ko wani abun ya same shi shi yasa bai neme ni ba har yanzu" kuka yaci karfinta tayi shiru, sai data tsagaita da kukan sannan taci gaba "I was so lonely and depressed, sai babana ya bani jari yace in fara business, it will keep me busy as I waited for my son, nan na fara kasuwanci, from small scale ina dan siyan kayayyaki ina siyarwa, Allah ya saka min albarka a ciki, nan take arzikina ya fara habaka, within few years na fara aikawa kasashen waje ana saro min kaya ina siyarwa, har na zama dealer nake supplying manyan shagunan garin nan da kaya. Amma dai dai da rana daya ban taba cire ran sultan zai zo ba, tunda na gina gidan nan na dawo duk sanda mota ta tsaya a bakin gate sai gaba na ya fadi ina saka ran shine yazo, amma shiru. Na kebe kaina daga cikin mutane ne saboda bana son maganganun da akeyi a kaina. Nasan Zayed yayi aure amma bansan wa ya aura ba, lokacin da yazo nan shida sister dinki naga cewa she is African kawai sai naji ina sonta, I told her about sultan. You have no idea how I felt sanda kika ce min ke matarsa ce" ta goge hawayenta ta juyo tana kallona "How long do you think zaiyi taking kafin yazo?" Nace "one week, at most, two weeks, shima saboda sai ya nemi visa ne" . Tayi murmushi tace "then we will wait for him, together".
Chapter 164 · 0% Book details