← Book details Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 147 OF 190

Sashe 147

Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

tace in kazo kar a barka ka ganta" Amir ya sake cewa "can you at least tell her that her husband is sick kuma yana bukatar ganin ta? Am sure in ka gaya mata haka zata ganni" ko kula shi David baiyi ba ya koma kofar gidan kawai ya tsaya yana kallonsa hannunsa a rike da bindigar sa. Amir yayi wishing ina ma yana da karfi irin na sultan da sai ya farfasawa david baki ya shiga gidan ya dauko moon aka ya kaiwa sultan ita. Amma babu damar yin hakan dan yasan tunkarar David will be like a suicide, kuma yasan bashi kadai bane akwai sauran a ciki. Dole ya koma yaja motarsa ya tafi, yanzu ya zaiyi kenan? Ya zaiyi da Sultan idan ya tashi? Wani tunani ne yazo masa, ya juya kan motar sai palace, yana shiga fada ya tafi direct, mutanen gurin sai kallonsa suke yi, sun san shi amma kuma basu taba ganin shi a fadar ba, ya tsaya yana facing Takawa da yake harde akan karaga, ga Abbas a zaune a hannun daman sa, ga sauran hakimai duk kowa ya juyo yana kallon Amir, da karfi amir yace "Your son is dying, yana asibiti kuma yana nemanka" kafin ya rufe bakinsa fadawa sukayi kansa, suka jashi suka fitar dashi waje, amma ko babu komai Amir ya isar da sakon sa. Ana fita da Amir Hakiman gurin suka fara magana, 'dama Sultan bashi da lafiya?' 'Me ya same shi?' 'Allah sarki yaron ya nutsu sosai wallahi' 'ni kam kwanan nan kullum na ganshi sai yayi ta bani sha'awa' da sarkin bai da makama, da madaki, wadanda sune ake kira da king makers, suka kalli juna suka mike a tare suka durkusa a gaban sarki "Allah ya taimaki sarki ai ya kamata muje muga jikin nasa" idon takawa ya kada yayi ja saboda bakin ciki, a ransa yana cewa "wannan yaron Amir yake kowa? Zaman sa ya kare a gidan nan" amma kuma a fili ba zai iya musa wa hakiman sa ba, musamman king makers, sune kamar shugabanni dan dattijai ne sosai, sune suka nada babansa, suka nada shi, sune suke da alhakin zaba da nada sarki. Dole Takawa ya mike, gab daya sauran hakimai suka mike, Galadima ne akan gaba. Amir yana ganin su yasan tarkon sa yayi kamu, ya shiga motarsa yayi gaba su kuma duk suka biyo bayansa. Gaba daya mutanen asibitin ranar sai da suka fito kallo, ga sarki da hakimansa gaba daya sunzo dubiya, direct dakin da sultan yake kwance suka nufa. Dakin bai dauke su gaba daya ba dan haka wasu ta taga suka leka suna gano sultan a kwance har yanzu yana bacci, Amir yaje kusa dashi yana shafa kansa yace "Sultan ka tashi ga Takawa yazo duba ka" a hankali idon Sultan ya fara budewa kadan kadan yace murya can kasa "Daddy? My Daddy?" Galadima ya rike hannusa yace "eh Sultan, babanka ne yazo ya ganka. Ya jikin nasa" Sultan ya kalle shi, ya dan hadiye yawu sannan ya fara kallon mutanen dakin, idonsa ya tsaya akan Takawa da yayi kicin kicin da fuska, ya karbe hannu sa daga na galadima ya mika gurin sarki yace "Daddy?" Gaba ki daya kowa idonsa yana kan Takawa dole ya karasa ya kama hannun sultan ya rike, hawayene ya fara gangarowa a idon Sultan, amir yaji wani iri a jikinsa, tun da suka girma, tun sanda aka kaisu lagos, bai taba ganin hawayen sultan ba sai yau, masu raguwar zuciya a gurin sai da suka taya sultan kokawa saboda babu wanda bai san kiyayyar da sarki yake yiwa sultan ba kuma babu wanda yasan dalili, a hankali sultan ya fara kukan kuma sai kukan ya fara karuwa har da sheshsheka, ya rike hannun Takawa yaki chikawa. Wani abu takawa yaji ya tsaya masa a zuciyarsa ya tokare, ya kasa hadiye koma menene, ya kasa fahimtar me yake ji. Muryar sultan yaji yace "Ummee na, Ummee na". Kan Takawa ne yayi bala'in sarawa, ya cika hannun sultan ya rike kansa da hannu biyu yana ambaton sunan Allah, ummee na, ummee na, a ina ya taba jin wadannan kalmomin, wani dan karanin yaro ya hango a idanuwansa wanda bazai wuce shekara biyu ba a hannun baba gaji yana ta zunduma kuka yana miko masa hannu yana cewa "Daddy na, Daddy na, ummee na, ummee na" a lokaci daya komai daya faru ya dawo masa tas a cikin kansa, take ya yanke jiki ya fadi sumamme a gaban gadon da sultan yake a kwance. Hmm. Things are not always what they seem.
Chapter 147 · 0% Book details