Sashe 46
Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Na karasa dai dai windown driver nayi knocking a hankali, da sauri ya sauke glass din fuskarsa ta bayyana dauke da murmushin mamaki "Hey, me kike yi anan?" Na daura hannayena akan windown nayi tagumi nace "unguwa zanje kuma an tare min hanya" ya kalli dandazon mutanen da suka taru a gefe sannan yace "lallai kice dara taci gida kenan" nayi dariya nace "dama ai hausawa sunce in zaka gina ramin mugunta ka gina shi gajere, yanzu kaga nice na rufta ciki" shima dariyar yayi yace "da fatan baki balla kafa ba" wani daga bayana yace "baiwar Allah dama kin rabu dashi, wannan mutumin bai san magiya ba, gashi nan an kira police zasu zo suyi mana maganin sa" Sultan ya leko da kansa yace "kafin suzo suyi magani na ni bara inzo inyi maganin ka, dan rainin hankali kawai" ya bude kofar motar ya fito da sauri, sai kuma ya kalleni ya ga yadda na hade rai sai ya koma yana cewa "kaci sa'a, amma na gane fuskarka, zamu hadu wata rana" ni kawai kallonsa nake yi da mamaki, shi babu abinda ya dame shi wai dan mutane suna zaginsa, kamar ma wani enjoying kansa yake yi. Yasa hannu ya bude min kofar kusa dashi yace "shigo in kaiki unguwar" na yi jim ina tunani, anya kuwa in shiga motar Sultan? Anya mutunci nane? Besides ba wani sanin halinshi nayi ba, kuma duk a halayensa da ake gaya min babu wani na kirki. Na sake kallonsa naga shima ni yake kallo pleadingly, oh God, kawai sai na zagaya na shiga. Mutumin da suke fada da Sultan ya saki baki yana kallon mu, ina kallon sultan ya mika hannunsa ta window yayi masa alamar fuck you. Daga nan ya daga windown ya tayar da motar muka tafi. Wani daddadan kamshi ne a cikin motar, irin kamshin nan da yake sa mutum ya lumshe idonsa, da gaske sultan dan gayu ne dan cikin motar tsaf yake, kujerun an lullube su da wani tattausan bargo wanda shi kansa kamshin yake yi. Shi kansa Sultan din gani nayi ya kara yi min kyau da kwarjini, yauma kamar kullum rigarsa body hug ce data kama jikinsa sosai amma yau 3 quarter wando ne a jikinsa, gashin kansa a hargize yake kamar kullum. A 20 yake tafiya da motar kuma gaba daya ba titi yake kallo ba ni yake kallo, har sai da naji kunya na rufe fuskata da mayafina. Motoci sai horn suke yi mana daga baya, duk wanda yazo wucewa kuwa sai yayi bala'i amma sultan ko kallonsu baya yi hankalinsa gaba daya yana kaina. Nace "wai wannan kallon na menene kuma" "duk sanda na ganki sai inga kamar kara kyau kike yi" kamar nima ince masa shima haka sai kuma dai nayi shiru nace "thank you" yace "ina zakije ne?" Sai yanzu na tuna na bar driver da mota a baya, da sauri na dauko waya ta na kira shi nace na tafi, ya danje yawo kadan sai ya koma gida yace ya kaini. A muryarsa naji alamar baiji dadin abin ba amma kuma babu yadda zaiyi. Mun danyi tafiya kadan nace "why do you do it?" Yace " me fa?" Nace "why do you block the road?" Kafin ya bani amsa wani ya danne horn a bayanmu sannan ya zo ya wuce mu a guje yana cewa "malam in ba zaka wuce ba ka bawa mutane hanya su wuce" Sultan yayi dariya yace "that's why" nima dariyar nayi nace "to kai me yasa ba zakayi saurin ba, kana tafiya a cikin abuja a 20 bayan kasan kowa a garin nan sauri yake" ya wani kwantar da kujera kashingida yace "sauri va gurin zuwa ba" da sauri nace "dan Allah ka rufa min asiri ka tashi, ya za'ayi mutum yana driving kuma ya kwanta" sai da yayi dariya sosai sannan ya tashi zaune, ni kuwa duk na rude, yana tashi wani ya yi masa dakuwa daga waje, ai kuwa ya sauke glass sukayi ta zage2 sannan muka wuce. Sai a lokacin na gaya masa inda zanje, yace "OK, inda kika tura mu rannan ko?" Muka yi dariya gaba daya. Muna tafiya a hanya ne yake tambayata me yasa nake yawo da driver? Nace masa "ban iya driving ba" yayi ta min dariya yana tsokana ta wai abin kunya kamata ban iya driving ba, yace "in kin yarda sai in koya miki" nace "not now, sai na gama school tukunna" yace "OK, Allah ya kaimu" mun danyi nisa na sake tambayarsa "yanzu dazu da kayi blocking hanya da mai martaba yazo wucewa fa?" Yace "kinsan kuwa hakan ta taba faruwa" na ware ido nace "haba? Ya akayi kuma?" Yace "kamar yadda nayi dazu, na rufe hanya nace ba shiga ba fita, na rufe glasses din mota na kunna AC na kwantar da kujera ta nayi kwanciyata, mutane suna ta hayaniyarsu da zage2n su, kawai sai ga Takawa nan ni ban sani ba, yana zuwa yaga an tsaya ya tambaya lafiya aka ce ai hanya a rufe take, yace aje a gano me ya faru, aka koma akace masa ai nine na rufe hanya da motata" yayi shiru, nace "me yace kuma?" Yace "dogarai ya aiko yace su farfasa motar su fito da ni suyi min duka su jani a kasa su kaini gida" na rufe baki na ina mamaki nace "ya salam, sunyi din kuma?" Wani murmushi ya jefa min yace "sun fasa mota alright, amma none of them will dare to touch me, duk wanda ya taba ni kuwa sai na kwantar dashi a asibiti kuma ya bar aikin sa kenan" nayi shiru ina jimamin maganar, it seems like there is crisis between the father and the son, does it has to do with Sultan not knowing who his mother is? Ina so in sake tambaya kuma bana so yaga kamar ina bi masa kwakwkwafi. Mun danyi gaba kadan sai naga ya sake hanya yabi wata hanyar daban, nayi sauri nace "ba nan ce hanyar ba fa" bai kalleni ba yace "eh na sani, sayar dake zanje inyi" nayi shiru yace "kinga kuwa zakiyi tsada" ni dai bance masa komai ba, sai a lokacin na fara lissafin babu wanda yasan tare da wa na fita, shi kansa driver din da muka fito dashi baiga sanda na shiga motar sultan ba, what if ya sace ni? Ina kallon shi ta gefen ido na yana min dariyar yadda na takure a gefe daya ina rarraba ido. Wata unguwa muka shiga irin unguwar talakawan nan, a raina nace me yake kawo sultan irin wannan unguwar kuma? I really hope he is not doing drugs kuma? Can gefe ya samu yayi packing yace "please two minutes dan Allah zanje in karbo sako" na gyada masa kai amma a raina ina cewa zaka je ka karbo drugs dinka dai. Ina kallonsa ya fita ya saka hannayensa a aljihu yana tafiya ya shige wani loko. Da sauri na dauko waya ta na kira Amira, "Amira gani na taho amma ba'a motar gida ba, ina motar sultan, in case in na bata a gurinshi zaku neme ni" na kashe wayar ina rarraba ido.