Sashe 137
Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Episode Seventy Seven : Amina Kadan ya rage dariya bata kubce min ba saboda ganin reaction din fuskokin su. Sam ba haka suka yi tsammani, su a tunanin su babu matar da za'a gaya mata irin wannan maganar ta hadiye sannan ta bayar da amsa irin wacce na bayar. Hajiya tace "kin sani? Kina nufin ya gaya miki exactly wannan maganar?" Ita kanta tasan cewa nasan karya suke yi, Nace mata "eh ya gaya min, ai baya boye min komai. Ya gaya min komai na labarin sa har labarin asalin fara shan giyarsa" a take naga kalar idonta ya chanza, murmushin fuskarta ya kau. I got her exactly where I want her. Na gyara zamana na harde kafafuwa na irin zaman da Sultan yake yi, na cigaba da cewa "nasan komai akansa, nasan duk abinda ya aikata a baya nasan kuma wanda bai aikata ba, nasan kuma abinda zai aikata nasan kuma abinda bazai aikata ba" daya matar tace "kuma duk kinsan halayensa kika yarda kika aure shi? Shi fa aure ba abu ne na wasa ba, in kika auri mutum kamar kin zabe shi ne ya zama uban 'ya'yan ki" nayi mata murmushi nace "ai in kana so kasan mutum, ranki ya dade, ba wajansa zaka kalla ba, ko kuma abinda mutane suke fada akan sa ba. Abinda zaka kalla shine his inner self, deep down waye shi. Sultan deep down is a good person, very good person, ni na gani kuma nayi niyyar fito da wannan goodness din nasa waje yadda kowa zai gani. Alhamdulillah, na fara samun nasara, dan duk wanda yasan sultan shekara daya data wuce in ya ganshi yanzu yasan da akwai banbanci. Wata rana ina fatan kuma zaku ganshi kamar yadda nake ganinsa." Sai a sannan Khulsum tayi magana bayan tayi tsaki tace "tana magana kamar wata psychologist" na juya na kalle ta nace "I am a psychologist, I have a first class degree in psychology from the second best university in the world. I know exactly when someone is lying to me. I can read your mind as well as I can read time from an analog clock" na bi fuskokin su da kallo, kamar an tsiyaye musu jinin su daga jikinsu, na hango kiyayyata karara a rubuce akan fuskokin su. Kusan minti biyu babu wanda ya sake cewa komai a cikin mu. Hajiya ce ta kirkiro murmushi tace "ku tashi mu tafi, mun bar ango yana ta jiran amaryarsa" Khulsum ce ta fara tashi ta fita ba tare da ta kalli inda nake zaune ba. Har mota na raka su na daga musu hannu sannan suka tafi. At least nasan yanzu tsakanin mu is clear, babu munafunci babu yaudara. Ba zasu sake zuwa su ce zasu gaya min wata magana akan Sultan ba, amma kuma nasan na kunno wata wutar kuma. Na gaya musu nasan secrets din su dan haka na kara wutar kiyayyarda suke yi min. But am ready, Allah yana tare dani and am not scared. Na yarda da Allah na yarda da kaddara, nasan su basu isa suyi min komai ba, duk abinda ya same ni daga Allah ne ba daga gare su ba. Kuma komai nisan jifa kasa zai dawo, duk kuma abinda ka shuka shi zaka girba, in khairan khairan in sharran sharran. Ina komawa cikin gida na koma part dina nayi wankan da ban samu nayi ba, ba fito na shafa special mai na, na kuma fesa turaruka daban daban. Na shiga closet dina, na jima ina neman kayan da zan saka, daga baya na dauko wasu deep red kaya, robber, three quaters wando da half vest. Na saka su ba tare dana saka komai a ciki ba. Ni kaina dana kalli madubi sai da naji kunyar kaina, kayan sun bi jikina like a second skin, kalar ta kara fito da haske da kuma kyan fatar jikina. Na dauko deep red lip stick na shafa a lips dina. Na dauko dogon hijab har kasa na saka, sannan na fita. A palon sa na tarar dashi, yana zaune da fararen singlet da gajeran wando a jikinsa, ya kunna TV ya rike remote a hannunsa amma kuma ba kallon yake ba, yayi nisa a tunani yana kallon sama. Na jima a tsaye ina kallonsa amma bai ma san na shigo dakin ba. Na dan daga murya nace "wanne film kake kallo ne?" yayi sauri ya kalle ni sannan ya kalli TV din, ya daga kafada yace "I don't even know wanne film suke yi. Ba'kin naki sun tafi ne?" Ban bashi amsa ba, ya fara kokarin chanza station, na chire hijab din jikina a yar a gefe nace "pss" ya juyo da sauri yana kallona, a hankali remote din hannunsa ya zame ya fadi kan carpet, ina kallon idonsa naga duk wani tunani da wata damuwar sa suna disappearing har sai da ya zamanto babu saura. Ya saki ido da baki da hanci duk yana kallona, a hankali ya furta "ya Ilahi save me, wannan rayinyar so take ta haukata ni" sai kuma naji kunya nadan rufe idona kadan da hannayena wadanda suka sha jan lalle tun na biki na. Yace "come here" babu musu na taka naje gabansa na tsaya, tun daga fuskata ya fara kallona har 'yan yatsun kafata. Ya hadiye wani mugun yawu daya sa na kara jin kunyar sa. Ya gyara zamansa yace "sit here" yana nuna min cinyarsa, nan ma babu musu na zauna. Ina zama na fahimci sako na ya samu karbuwa dan message din yaje har inda nake so yaje, na danyi dariya kadan, ya saka hannu yana shafa bare fatar cikina, murya can kasa yace "dariya kike yi min ko? Zan rama ne nima" na saka hannayena duk biyun na zagaye wuyansa sannan nace "sai dai ka rame" yayi murmushin gefen baki yace "really? Wanna bet?" Nace "yes" ya dora hannunsa akan kirjina ya fara shafawa a hankali, na lumshe ido na jikina yana amsar sakonsa na bude su akan fuskarsa mai dauke da murmushin mugunta yace "you still wanna bet?" Wannan karon ban bashi amsa ba, ya cigaba da abinda yake yi, nace cikin sarkewar murya, "ka takura musu da yawa fa" ya dan bata fuska yace nine na takura musu ko sune suka takura min?" Ya saka both hannayensa ya kama straps din half vest dina ya jawo ta kasa ya dawo da ita kan cikina, yace "better, yanzu sai muga waye ya takura wa wani a tsakanin ni da su" ina kallon cikin rinannun idonsa nace "in suka rame bashi kenan ba" yayi replacing half vest din da hannayensa yana kara lumshe ido, yace "wa yace miki ramewa zasuyi? A cikin 'yan kwanakin nan baki ga har girma suka kara ba sabida kulawar da suke samu? Nine dai nake ramewa saboda takura min da suke yi, sun hanani sakat, sam bana iya dauke ido na daga kansu, bana samun nutsuwa sai ina tare dasu, in ido na biyi tunanin su nake, in bacci nake mafarkin su nake......" Tun ina jin abinda yake cewa ina kuma fahimta har na daina fahimtar abinda yake cewa, na daina fahimtar komai, shima kansa mai maganar bana jin yana fahimtar me yake cewa, daga baya ma maganar ta gagara gaba daya. Mun manta da duk abinda ya faru a ranar, babu Takawa and his threats, babu Hajiya and her hypocrisy, babu khulsum and her food, a lokacin hatta Mommy da Daddy basa gabana, Sultan ne kadai a gabana, only him existed in my world kamar yadda shima ni kadai ce a tasa world din. Sai da akayi first round aka zauna break sannan na bashi labarin yadda mukayi dasu Hajiya, ban boye masa komai ba na gaya masa duk abinda suka ce min da amsar dana basu. Kamar yadda nayi tsammani, bai nuna damuwar sa koya tada hankalinsa ba sam, sai nuna min jin dadinsa da yayi akan yadda nayi tackling maganar da kuma trusting dinsa da nayi. Daga nan muka bar maganar muka cigaba daga inda muka tsaya. Hint ga matan aure, irin wannan time din shine best time discussing sensitive issue da mai gida, especially mai gidan da yake da temper ko kuma wanda baya daukan shawara, a lokacin he is relaxed, in body and in spirit, kan sa is fresh,and he is very excited, da wahala ki fadi abinda zai bata masa rai a lokacin. Amma fa bance ayi using time din wajan roko ba, ko kai tsegumin kishiya ba, gwara ayi amfani da time din gurin bawa mai gida shawara mai kyau wacce zata kara kafa miki fadar ku a gurinsa. Washegari kamar yadda Sultan ya saba, in ya tafi masallachi baya dawowa sai gari ya waye, wanda na lura yana zama ne acan yayi karatun al'qurani, ni kuma wannan time din nake using in gyara dakunan sa, mostly daga nan bacci muke koma wa amma yau kitchen na tafi na barshi, yana ta mita wai shi bai ga amfanin in ce sai na koyi girki ba, tunda dai shi zan ke yiwa girkin nan kuma yace baya so ba shikenan ba sai in hakura. Ina shiga kitchen na tarar already Asma'u tana ciki, yau ma cewa tayi in cigaba da watching and learning, tana yin komai tana yi min bayani, ni kuma na bude kaina sosai ina fahimta, in naga abin tambaya in tambaya, har muka gama komai muka jera a dining sannan na tafi zanyi wanka. Ina shiga dakina wayata tana fara ringing na duba naga Daddy. Duk da cewa tun da nazo gidan kullum sai ya kirani ko kuma ni in kira shi mu gaisa amma yau sai da naji gaba na ya fadi. Nayi bismillah na dauki yawar, muryarsa naji wasai babu alamar damuwa a cikin ta, na sauke ajjiyar zuciya na gaishe shi, mun jima muna hira yana gaya min gobe zai tafi England kuma zai dan jima kafin ya dawo, nayi masa addu'ar fatan alkhairi, sai da muka gama maganganun mu sannan yace "jiya da daddare ai nazo palace, mai martaba sarki ya kira ni akan maganar ku, ya nuna min wasu pictures da banji dadin su ba, amma abinda na sani shine na yarda dake, tunda har baki kira ni kin gaya min menene ya faru ranar nan ba hakan na