← Book details Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 190

Sashe 98

Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Hafsat ma kanta ranar dana zauna a kusa da ita sai da ta rinka shanshanani tana cewa ya akayi ita ba'a yi mata irin wannan ba lokacin bikinta, amma tace in dai tayi arba'in itama sai anzo anyi mata. Ranar kam kin zuwa gurin sultan nayi saboda bana son ya saka ni a gaba da tambayar wanne turare na chanza, shima kuma da yake yanzu kullum a gajiye yake sai bai wani matsamin inje ba, a waya dai muka karaci hirar mu. A hankali komai na ginin sultan ya kammala, Hafsat da aunty Maryam kawar Mommy da gwoggo Aisha, matar uncle Aliyu ne suka je suka gano gidan saboda siyayyar kayan daki, tunda suka dawo suke santin kyau da tsarin gidan, Hafsat har dare zancen gidan nan take yi har sai da Mommy tace "ya ishe mu haka, munji yayi gida mai kyau, congratulations to him" sannan Hafsat tayi shiru. Har yanzu Mommy ba wani son sultan take yi sosai ba amma dai ba kamar da ba, duk da yanzu ta daina ce masa tsagera da sauran sunayen da take kiransa dasu amma har yanzu bata ambaton sunan sa, sai dai tace masa wannan yaron. Dama tun tuni ni da Sultan mun tsara colors din da muke so ayi furnishing ko wanne daki dashi, da colors din yayi amfani gurin tiling da fenti, dan haka na zauna na tsara wa Hafsat komai yadda nake so ita kuma ta gaya wa Mommy, a cikin sati daya akayi order komai aka kawo, masu interior decoration aka dauko suka je suka saka komai, suka kuma kara abinda suke ganin ya kamata su kara. Ni kaina nasan Daddy ya narkar da kudi a kaina. Tun ana saura sati uku biki aka gama shirya gidan tas aka rufe.

Saboda tsabar gyaran da jikina yake samu gani nake yi kamar in aka tabani jini ne zai fito, fuskata har wani kalli take yi saboda tas din da tayi, idan na zauna a guri kuwa ko bayan na tashi kamshina yana nan. Dole na kara jan jikina daga gurin Sultan dan sosai yake nuna min kwalamarsa a fili, sau da yawa in yana zaune a kusa dani yayi ta shanshana ni har sai na tashi na gudu. Da kadan da kadan gida ya fara cika da mutane, daada ta iso da jama'ar niger, part dinta aka bude mata suka sauka a can, tana zuwa itama ta fara dura min tsumi, kullum da akwai abinda zata bani in sha, daga farko dariya nake yi mata dan ni gani nake duk wani maganin mata kawai fada ake yi, dan mu a likitance bamu san wannan ba, ban gane bani da wayo ba sai da na fara jin chanji a jikina, babu shiri na daina shan tsumin daada, inta bani sai inzo in ajiye a fridge in yi tafiya, data fahimci me nake yi ta tambaye ni dalili sai nace mata ta ajiye min in anyi bikin sai inke sha acan, sosai ta fahimci abinda nake nufi dan haka ta daina bani, sai da hado min su jaka guda kowanne da bayanin yadda zan yi amfani dashi ta bani tace in tafi dashi can, na karba nayi mata godiya, ni sai inta mamakin daada da Mommy, su da basa son sultan kuma me yasa suke yi tayi masa tanadi haka?.

Saura sati biyu biki aka kawo kayan lefe, akwati set goma aka kawo,different colors, ni har kasa tsayawa nayi in kalla saboda kayan sunyi min yawa, duk kayan kuma Yaya ce tayi su, tace tata gudunmawar kenan, dan haka da Daddy ya saka sultan a gaba da fadan kayan sunyi yawa sai ya gaya masa yace shi ko dan kunne bai saya a ciki ba. Kaya ne masu tsada daga gani kasan cewa akwai class. Sarkokin gold akwatin su daban. Kuma komai size dina, daga gani kuma kasan babu abinda aka saya a Nigeria. 'Yan 'yalleman dama basu zoba sai ranar da aka kawo kayan, daga nan suma suka bude part din su inna suka baje tasu hajar. Hajja kam sai yada magana take tana kunkuni 'ai dama sai da jikina ya bani, kudi suka gani shi yasa suka hana yaron nan, duk abinda kuwa aka saka bidi'a a cikin sa ba zai yi albarka ba. Shima Allah ya bashi arzikin da yafi wannan kuma Allah ya bashi matar da ta fita" babu wanda ya kula ta haka ta gama sumbatunta.

Inna kam tana zuwa ita tsarabar data kawomin shine na adduoi, tace "gidan sarauta zaki je dole kina bukatar tsari sosai, tsari daga sihiri, tsari daga mugun baki, tsari daga dukkan sharri na mutun kona aljan" ta babbani rubutu na sha, ta kuma koya min adduoin tsari sosai, sannan tayi min nasihu masu ratsa jiki akan kula da addini, tsarkake zuciya da iya mu'amala da mutane, tace as long as kana kula da addinin ka sosai, ka kuma tsarkake zuciyar ka baka nufin kowa da sharri to Allah ba zai taba bawa makiyinka nasara akan kaba. Shi kuma iya zama da mutane shi zai kara maka soyayyar miji ya kuma jawo maka soyayyar 'yan uwan miji. Naji dadin nasihohinta sosai, sai nake ganin kamar duk ita tafi kowa bani tsarabar gidan miji.

Kamar yadda akayi bikin Hafsat haka nawa ma zai kasance, su Mommy sun shirya kunshi, kamu da mother's eve, su kuma su Amira da Amir 'yan committee sun shirya bridal shower, luncheon, dinner, sai walima for girls, and bachelor's night for the guys. Sai kuma ranar da aka kai amarya Amir ya shirya mana welcome party anan gidan mu da Sultan. Ni already jina nake a gajiye, I have no idea yaya zan iya duk wadannan events din.

Har yanzu wasan buya muke yi da Siltan, dan sosai nake rikita masa lissafinsa in muka hadu, nima kuma tunda daada ta fara dura min tsumin ta na fara ja baya dashi. Yayi mitar har ya gaji, gashi gidan ya fara cika da mutane balllantana yace zai yi abinda ya saba ya shigo min daki cikin dare. Shima kuma yanzu ya dan fara ja da baya da zaman gidan saboda baki. Wani lokacin sai dare yake zuwa sai dai insa akai masa abinci office, da daddare kuma sai in aika masa dashi dakinsa.

Ten Days To The D- Day
Chapter 98 · 0% Book details