Sashe 103
Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
you still love me, i know you do, I just need you to give me a chance in dawo miki da soyayyata" ya sake dawowa gaba na "maimunatu please ki sake bani chance" na sunkuyar da kaina ina kallon zoben Sultan a raina ina ayyanawa idan da ace sultan ya san inda nake kuma yasan tare da wa nake, zai iya harbo igwa ta tarwatsa building din gaba daya, a hankali na sake magana nace "there is no time, bikina saura kwana goma" da karfi yace "what?" Na gyada masa kai, ya sake mike wa ya buga hannun sa a table din yace "NO" da dan karfi. "No Maimunatu, destiny brought us together today. Da Allah baya so mu kasance tare da ba zai kawo ki office din nan yau ba. Da in zamu hadu ma sai da auren ki tukunna. Please call off the wedding" na girgiza kaina da sauri nace masa "not possible. I can't do that. Ko da ma ace bana son wanda zan aura ai bani nake bada kaina ba, an riga an bashi ni, an gama komai, bazan taba zuwa in ce bana son auren sa ba. It doesn't work like that" ya sake tsugunna wa kamar zai dora hannayensa a kan lap dina nayi sauri naja kujera ta baya, ya dora hannayen aka, sannan ya shafo fuskarsa. Idonsa ya sauka akan zoben sultan da nake ta aikin murzawa. Ka kalle ni yace "his ring?" Na gyada masa kai, ya sake cewa "who is he?" Na sake amsa masa "it doesn't matter" kamar amsar tambayar sa sai waya ta ta fara kara, a tare muka kalleta, 'my sultan' a hankali ya furta "sultan" ban dauki wayar ba saboda bazan iya yin magana da Sultan a yanzu ba, har ta gama ringing ta katse ya sake kira, nasan halin Sultan in yaso abu, bazai daina kira na ba har sai na dauka. Na mike tsaye, Ibrahim ma ya mike yace "please don't go" na kalle shi for some seconds sai na juya zan tafi, hijab dina ne ya jawo wani frame din hoto daga kan table din ya fado kasa, na durkusa a hankali na dauki hoton ina kallo, wata yarinya ce zata yi shekara uku a duniya, naga fuskar Efi a fuskarta amma idon Ibrahim, she looks very cute a cikin English wears tana murmushin da yake bayyana cleft chin dinta just like her father's. Nace "she is very beautiful" ya zagayo ta bayana yana kallon hoton yace "yes she is, just like the Moon I named her after" da sauri na juyo na kalleshi, yace "yes, sunan ki na saka mata, maimunatu, and I call her Moon" da sauri na hadiye kukan daya taho min, her mother died giving birth to her, but he named her after me. Daya frame din da yake kan table din na dauka, numfashina ne ya tsaya chak, hoton mu ne nida Ibrahim, duk bama dariya, fuska ta kamar zanyi kuka, yana tsaye a bayan class din mu ni ma ina tsaye a kusa dashi, na dan kwantar da kaina a kafadar sa shi kuma ya juyo kadan yana kallona. I remember sanda aka dauki hoton, Hafsat ce ta dauke mu da wayar ibrahim ranar da zamu bar makaranta. We were so young then, and so much in love. Na kalle shi da sauri naga yana murmushi, it is like nothing has changed, but yet, everything has changed. Na ajjiye pic din da sauri na yi hanyar waje ina jinsa yana cewa "maimunatu please" exactly yadda yake cewa in yana ya son ya lallabani in yi masa wani abu. Da bibbiyu nake hada stairs ina sauka, idona almost a rufe na fita na doshi motar sultan da nazo da ita, na bude na shiga nayi mata key, a lokacin na hango shi ya fito daga building din yana nemana. Nayi baya na fita daga packing lot din ina ganin sa ta mirror yana kallon motar, yayi noticing sunan da aka rubuta a gurin number "Sultan 2" . Sai da nayi nisa da building din sannan na sauka daga kan titi nayi packing, na kifa kaina akan steering na kama kuka, what hurt me the most is the fact that Amira can betray me like that. Sometimes, the person you trust the most will hurt you the most. Masoyan Maimoon ina gaishe ku baki daya, nima kuma ina sonku irin sosai dinnan. Ina ganin sakonnin ku ta WhatsApp da Facebook, masu bina private da masu turo wa ta group. Ina so ku fahimci abu biyu. Na farko Moon guda daya ce ba za'a raba ta a bawa kowa ba, dan haka dole wani ya samu kuma dole wani ya rasa. Dan haka at the end dole wani zai ga kamar ba'a kyauta masa ba. Abu na biyu kuma shine, tun kafin in fara rubuta labarin Maimoon na riga na tsara yadda zai kasance, yanzu kawai details din nake filling, kada wani yaga kamar labarin ina rubuta shine yadda zan farantawa wani. Idan kuka cigaba da bin Maimoon na tabbatar muku karshrn labarin zaiyi satisfying kowa insha Allah. Duk da dai ance shi dan adam ba'a iya masa. I so much love you all