← Book details Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 186 OF 190

Sashe 186

Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Episode Ninety Nine : New Little Love Sorry for the delay guys. Na ga sakon ku akan sunan baby, naji dadin yadda kukayi responding. Mutane sun zabi sunaye kamar haka : Muhammad, Abdullahi, Ibrahim, Abubakar, Lawan da sauransu. A lissafina wadanda suka ce Muhammad sunfi yawa dan haka zamu saka Muhammad din. Masu cewa Ibrahim, I salute your loyalty to Ibrahim amma bansan ta yadda zan yi convincing Sultan ya sakawa dansa sunan tsohon saurayin matarsa ba. Lol. Love you all. Shiru dakin babu wanda yayi magana. Ummee ce ta fara katse shirun tace "me ake jira ne wai? Ka bishi mana kuje ya dauka asaka mata" babu wanda yayi magana still. Doctor ya fahimci akwai tension a gurin sai yace "bara inje office, Ibrahim in zaka bayar din ka same ni a office amma da sauri saboda ina son in saka mata sai inyi mata allura tayi bacci, kafin ta tashi an gama saka mata" ya juya har zai fita Daddy yace "doctor bara inzo ka dauki nawa, blood group din mu daya da ita, ban san ana bukatar jini ba da tuni na bayar. Ita da Hafsat group din mu daya su kuma boys din suka dauko Mommyn su" doctor yace "that's OK" ya fita. Ummee ta mike tsaye, "NO daddyn Moon, da shekarunka zaka bada jini bayan ga matashi yayi matching?" Ta kalli Ibrahim "ko kaine bakason ka bayar?" Still idonsa akan sultan yace "it would be my honor to give my blood to her. But I think it is better a dauki na daddyn kawai" Ummee ta sake cewa "why? Ji nake kai mijin sister dinta ne? Doctor yace blood din is clean, so why?" A hankali sultan yace "I don't want his blood in her" Ummee ta juyo tace "me kace?" ya maimaita da dan karfi "I don't want his blood in her" na rintse idona ina gode Allah daya kasance babu bare a gurin duk 'yan'uwa ne, ya Walid yace "Sultan, it is just blood. Babu abinda ake transferring a cikin jini in ba ciwo ba, kuma doctors sunce the blood is clean, don't make a case out of it please" sultan ya mike tsaye idonsa akan Ibrahim yace "it is not just blood, it is HIS blood, and that's what makes it different. I am her husband and I said ba za'a saka mata jininsa ba. I would rather buy it from a total stranger than take HIS. I don't even know what the FUCK he is doing here" idanuna a rufe naji karar mari, na saka hannu na na rufe fuskata, ba sai na kalla ba nasan wa aka mara kuma nasan wa yayi marin. Ummee ce ta mari sultan. Shi aka mara amma ni naji zafin. Ummee ta fara fada muryarta har rawa take yi, na tabbata da zan iya kallon idonta da zan ga hawaye a ciki, tace "Sultan a gaba na? A gaban Daddy? I know you are spoilt but didn't knew you are this spoilt. Mijin kanwar matarka, yazo har asibiti ya dubata kuma yayi offering zai bata jininsa a saka mata amma ka zage shi? Wanne irin mutum ne kai?" Daddy yayi magana "Khairat, Ibrahim is Moon's ex boyfriend, wannna shi yasa sultan yake reacting this way" Ummee tace "dan yana tsohon saurayinta hakan bai kamata ace ya saka yayi treating dinsa this way ba. Karewar aure ji nake 'da ta haifa masa ma yanzu. Shi kuma sister dinta ya aura. Menene kuma saura a ciki? Yanzu shi baiji kunyar ganin idonka ba? Baiji kunyar Amina ba? Ko da baya so ai da akwai hanyar da zai bi yace baya so ba sai yaci mana mutunci ba. Wannan ai mu ya wulakanta ba Ibrahim ba. Ina lura da Ibrahim din tunda ya shigo bai kalli inda Maimunatu take ba har ina tunanin me yasa haka ashe shi wulakanci yake gudu" fada Ummee take kamar zata ari baki. Sai da tayi shiru Ibrahim yace "am sorry. Ban zo da nufin creating trouble ba, na kawo Amina, muna tare da su Habeeb aka kira su gurin daukan jini, at first nace banda ni doctor din yana min wasa yace ina rowar jini ne, I didn't know it will match, I didn't want to create a scene shi yasa na bari aka dauka" Daddy yace masa "it is OK Ibrahim duk mun fahimta. It was just a misunderstanding. A bar maganar haka ta wuce" Ummee tace "ya kusa wucewa dai" ta kalli sultan tace "tashi ka bashi hakuri, kuma ka raka shi da kanka gurin doctor a dau jinin sannan ka kawo a saka mata, that's your punishment for been arrogant" da sauri Ibrahim yace "No ma'am, that's not necessary. Na fahimci sultan sosai kuma banji haushin sa ba. Idan nine nasan I might do something worse than what he did. Bana son a kuma samun wata matsala akaina." Ummee tace "ba akan ka bane Ibrahim, akan sa ne, ina son yasan cewa idan yayi ba dai dai ba dole ayi punishing dinsa. So nake inga in an saka mata jinin ya zaiyi" ta juya tana kallon sultan tace "tashi ka bashi hakuri nace" Sultan ya mike kamar mai ciwon cinya, ya tsara a gaban Ibrahim kamar ba zaiyi magana ba, amma nasan sultan baya taba yiwa Ummee musu duk da kuma nasan zuciyarsa yanzu kamar zata fashe yake jinta, ya dan jima a tsaye sannan yace "am sorry. And thanks for offering your blood" ya mika wa Ibrahim hannu, Ibrahim yayi murmushi yayi shaking hannun sultan yace "it is OK. You are welcome" daga nan suka juya suka fita tare. Suna fita Mommy tana shigowa, ta kalle mu daya bayan daya tace "what did I missed? Me ya faru?" Daddy yace "tsegumi. Kin riga kinyi missing ya wuce ki" daga haka ya mika mata babyn da yake hannunsa ya fita. Ba'a jima ba suma su mommy suka fita suka bar mana dakin. Sunfi awa biyu a gurina, har akayi magrib, ana ta hira ana daukan pictures da baby, suna ta tsokanar Hafsat wai baby na yafi little khairat kyau saboda sultan yafi zayed kyau. Ita kuma ta dage sai kumfar baki take ita a dole zayed yafi sultan kyau. Sultan ya shigo ya zauna shima ya shiga cikin muhawarar, suka yi ta bugawa da Hafsat kowa yaki hakura, sultan yace zayed bama a class dinsa yake ba, yana class din kasansa, ita ma kuma tana class din kasana, dan haka ita da zayed ba zasu taba haihuwar 'ya'ya irin namu ba. Hafsat ta lakuce wa babyn hanci tace "akan wannan hancin ne dai ake wannan maganar, ita ma kuma khairat tana dashi wanda yafi wannan tsaho ma" sultan yace "kar ki bari ummee ta ganki kina lakuce masa hanci. Kuma ba maganar tsahon hanci ake yiba, maganar kyan hanci ake. Baki san in hanci yayi tsaho da yawa baya kyau ba?" Ina daga kwance nace "sultan don't forget about the lips" Hafsat ta juyo kaina "wannan bakin mai kama da danyen nama har wani kyau ne dashi? Daga ganin bakin irin na ubansa ne rashin kunya zai ringa yiwa yayun matarsa" Sultan yace "ke waye mara kunyar? Ko yayanki walid na girme shi ballantana ke" tace "amma dai baka girmi mijina ba" walid yace "ni din wata nawa ka bani?" Yace "na dai girme ka koma wata nawa ne, ko kwana daya na baka na girme ka" Habeeb yace "amma dai mun girmi matarka, dan haka dole ka bamu girma" Sultan yayi dariya yace "waye yace maka kun girme ta? Ai ni da ita soul din mu daya, gangar jiki ce kawai da ban, so technically she was born the day I was born, jikin ne dai sai daga baya aka haife shi. There is a strong chemical bond between us spiritually" Fadila tace "what kind of chemical bond? Covalent ko electrovalent ko hydrogen bond?" Ya dan bata fuska yana kallonta sannan ya juyo ya kalleni yace "which one is the strongest?" Duk akayi dariya, Aisha tace "ku da kuke da soul daya ai kamata yayi ace duk abinda ta sani kai ma ka sani ba sai ka tambaye ta ba" ya juya gurinta yana kallonta sai kuma yayi tagumi yace "kai Amir, yaushe ka koya wa matarka rashin kunya? Ka gaya mata idan manya suna magana yara basa saka baki shiru suke yi" nan kuma suka koma yi shida Amir. Suna ta sakani dariya gashi dinki na yana min ciwo idan nayi. Sultan sai famfa su yake, duk wanda ya fadi magana sai ya samu amsar da zai bashi. Hafsat ita kuma sai hawa take, har yanzu ta kasa gane halin sultan, a karshe tace wallahi sai an sake wannan hirar in zayed yazo. In kaga sultan a lokacin ba zaka taba cewa wani abu ya bata masa rai dazu ba, hirar sa kawai yake yana dariyarsa. Haka Sultan yake, akwai saurin hawa akwai kuma saurin sauka. Amaren mu ma duk sun ware suna ta hirar su, ina kwance ina dan saka musu baki kadan. Doctor ya shigo da ledar jini a hannunsa, yace su tafi za'ayi min allurar bacci in huta, nan suka fara fita kowa shida matarsa gwanin sha'awa, Amina ma ta kira nata a waya ashe ba nisa yayi ba dan haka yace ta fito gashinan a waje. Faruk yana shafa kai yace da sultan zai kai Huda gida suma suka fita, ya rage daga ni sai sultan da doctor, da baby kuma a kan gadonsa yana bacci. Doctor ya rataye jinin ya kamo hannuna zai saka min, na kalli sultan da ke tsaye kusa da doctor nace "doctor da ka bar jinin nan kawai" ya dakata yana kallona yace "why? Mun gwada red blood count dinki is low. Me yasa ba kyaso" na kalli sultan nace "Sultan ne baya so" sultan ya bude ido da baki yana kallona yace "ke? yaushe na fada miki haka? Sharri zaki yi min a gaban likita ko?" Doctor ya tsaya yana kallon mu yace "what is it doing to be? A saka ko kar a saka?" A tare muka yi magana da sultan, ni nace kar a saka shi kuma yace a saka, doctor ya tsaya yana kallon mu yace "ko in baku guri kuyi magana?" Sultan yace
Chapter 186 · 0% Book details