Sashe 179
Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Episode Ninety Six : The New Bride Riyadh; bayan tafiyar su Moon; A hankali Ummee ta juya ta koma cikin gida, tana shiga palon kawai taji gaba ki daya ta tsani gidan kuma, ta tsuguna anan bakin kofar tana jin hawaye yana fitowa daga idanunta. Ta jima a haka sannan taji karar wayarta kamar daga sama, da bata yi niyyar tashi ta dauka ba dan she is in no mood for chitchat, sai kuma tayi tunanin ko moon ce zata gaya mata wani abu, dan haka ta tashi da sauri ta karasa gurin yawar ta dauka, number din Nigeria ta gani, bata san number din ba amma jikinta ya bata ko waye, ta ajiye wayar bata dauka ba a ranta tana cewa 'duk laifin ka ne ai, muna zaman mu ka jawo gashi nan sun tafi sun barni ni kadai' ta zauna akan kujera tana lissafin abinda zata yi kuma, sai ta sake jin karar wayarta, wannan number din ce dai, Sadiq ne, tun da suka rabu ranar nan da daddare a abuja shekaru talatin da suka wuce bata kuma jin koda muryarsa ba sai dazu. Da taso shi kamar rai, son da ya saka har ta guji iyayenta ta aikata abinda bata taba tunanin zaya iya aikatawa ba, amma ta aikata saboda shi. A lokacin daya aiko mata da takardar saki kuma ji ta yi a ranta kamar duk duniya babu wanda ta tsana kamarsa, amma duk da haka duk tsahon shekarun nan, babu wani namijin data taba kalla da sunan namiji, ga larabawan nan, kyawawa na ajin karshe, amma duk kallon mata take musu a idonta, bata jin da akwai wanda zata iya sakawa a matsayin data sakashi a da. Sai kuma ga Maimunatu tazo mata da labarin cewa duk abinda ya faru baya cikin hankalinsa, sakin da yayi mata ma bai ma san ya sake tan ba, asali ma, bai ma san da ita ba all these years. Ga kuma labarin wahalar da sultan yasha a hannunsa. Sai ya zama ta kasa tantance taka mai mai me take ji a dangane dashi. Shin haushinsa take ji, ko tsanarsa tayi ko tausayinsa take ji. Wani kiran ya sake shigowa, ta daga wayar a hankali ta amsa, ta saka a kunnenta amma kuma sai ta kasa magana, to me zata ce masa? Shima daga daya barin maganar ya kasa, sun jima a haka suna sauraren numfashin juna, shekara talatin ba kwana talatin bane ba. Ya lumshe idonsa yana picturing dinta a ransa, sannan murya cikin makogwaronsa yace "how are you, Khairat?" Taji kiran sunan ta da yayi har cikin ranta, da akwai wani tone da yake kiran sunan ta dashi wanda shi kadai ne yake kiranta da hakan, all those thirty years melted in her heart. Ta dan gyara muryarta kadan dan kar ya fahimci yana da wani effect a kanta yace "They are gone, sultan and Moon, bansan inda suka tafi ba" yace "Sultan is a big boy, He will take care of them. Am asking how are you" ta goge hawayen idonta tace "am fine. Am a strong woman now. I have been taking care of myself for thirty years, I can take care of my self now, I don't need you" bai damu da abinda tace ba yace "then why are you crying?" Tayi shiru dan bata dauka zai gane kuka take ba, ya sake cewa "why are you crying, Khairat?" Nan take kukan ya taho mata gaba daya, tayi tayin kayanta bai hana ta ba, har da sheshsheka, sai da ta gama kayanta ta goge hawayenta sannan ya sake yin magana, muryarsa tayi masa nauyi sosai, yace "do you want me to come?" tace "I want my son. I want Sultan. I am tired of living alone. Sultan yayi fushi sun tafi sun barni ni kadai. Ban san inda suka tafi ba" kamar baiji abinda ta fada ba ya sake maimaita tambayar da yayi mata "do you want me to come?" A hankali tace "yes, yes I want you to come" yace "then I will come, I will come for you like I promised. Am sorry I kept you waiting" tace "Sultan ban san inda suka tafi ba" ya dan jima yana tunani sannan yace "zan saka a duba su anan airport din, duk inda zasu je dai nasan jirgi zasu hau, in kuma basu hau jirgi ba to suna cikin kasar nan. Daga nan zamu san inda suka tafi sai mu neme su a can" ta gyada kai kamar yana kallonta, yace "shikenan hankalinki zai kwanta ko Ummeen Little Love?" Bata ce komai ba, yace "I will come to Riyadh jibi insha Allah" ji tayi zuciyar ta ta fara bugawa da karfi, ta kashe wayar tana kallon screen din wayar, jibi? Two days kenan? Anya kuwa zata iya ganin sa? Ya yake yanzu? Ta tuna cewa yanzu shi sarki ne, yayi aure bayan rabuwarsu har ya haifi yara biyu, how much has he changed? Is he still the Sadiq she knows ko kuma ya koma total stranger? A cikin kwana biyun da tayi tana jiran zuwansa har sai da ta rame saboda tunani, wani lokacin sai zuciyarta ta gaya mata ta kirashi kawai tace masa kar yazo yayi zaman sa, tunda in yazo ma mai zai yi mata? Babu wani abu a tsakanin su yanzu, ta tabbatar babu sonsa yanzu a zuciyarta, bata jin haushinsa dai irin da amma bata sonsa, duk sanda tayi wannan tunanin kuma sai ta tsaya ta tambayi kanta, anya kuwa? Amma kuma tana da tabbacin cewa shi babu wani abu a ransa a game da ita, zai zo ne dai akan maganar dan su, amma koma menene a tsakanin su is now over. Ya gaya mata yayi tracing su sultan, dan haka yanzu bata da fargaba a kan su, tasan they are safe. Ranar da zai zo ta gyara masa guest room, amma kuma sai ta tsaya tana tunanin bai kamata ta sauke shi a gidan ta ba tunda ita kadai ce a gidan, sai kuma tayi tunanin mai yasa take wannan tunanin a kansa bayan babu komai a tsakanin su. Bai gaya mata karfe nawa zai baro Nigeria ba dan haka bata san karfe nawa zai sauka ba, ita kuma bata tambayeshi ba, so she get ready, sits down on the sofa and waited, with her hands between her thighs. Akayi asahar ta tashi tayi sallah ta dawo ta zauna, akayi la'asar ma haka, magrib tazo itama ta wuce, sai da taji ana kiran sallar isha sannan hawayen da take ta rikewa ya fara gangarowa daga idonta, he is not coming, he is never coming. Ta mike a hankali ta koma bedroom dinta. Tana idar da sallah taji karar wayarta, sai da taji kirjinta ya buga, ta mike ta dauki wayar tana saka ran ganin 'sultan's dad' kamar yadda tayi saving number dinsa, amma sai taga number din mahaifiyarta. Ta zauna a bakin gado ta dauka da sallama. Tace mata "ki zo yanzu ki same mu a gidan babanki Umar" daga nan ta kashe wayar. Ta ajiye wayar ta rike kanta da hannu biyu, ya salam, me ya faru kuma? Kar dai ace sun gano cewa sun shirya da Sadiq zai zo gidanta, tasan halin uncle Umar sosai, abu na farko da zai fara yi shine zai karbe gidanta yace ta koma gidansa da zama. Amma kuma sanda ta kai masa sultan ai bai nuna wani abu ba, nuna wa yayi kamar komai ya wuce. Bata da zabi, duk da shekarunta amma bata kinyin abu in iyayenta sun gaya mata. Dan haka ta tashi ta tafi. Babu kowa a kofar gidan dan haka ta shige cikin gidan direct, tana gaisawa da matan gidan suka gaya mata ta shiga palon uncle din nata ana jiranta, ta gyara lullubin ta ta shiga da sallama. Gabanta ne ya fadi ganin mutane da dan yawa a palon, ba tare data tsaya kallon waye da waye ba ta shiga, ta zauna daga nesa akan carpet ta fara gaishe su. Sai a lokacin ta lura da akwai bakin fuska a dakin, ta tsaya da gaisuwar da take yi tana kallon su, duk da sun dan juya bayansu daga inda take zaune amma ta gane shi ta yana yin zamansa, ya harde kafafuwansa ya zauna a kansu, tun sanda ta san shi haka yake zama duk sanda zai zauna a kasa ba'a kan kujera ba haka yake zama, kuma taga sultan ma haka yake zama, Sadiq ne, he is here. Bata gaishe su ba daga shi har abokin rakiyar tasa , ta karasa gaishe da iyayenta ta zauna kanta a kasa tana jiran taji ta ina za'a fara yi mata ruwan bala'i. Abokin tafiyar Takawa ne ya bude taron da addu'ah, ya nemi zabin ubangiji akan duk maganganun da za'ayi a gurin sannan kuma ya nemi tsarin ubangiji daga shaidan da mukarrabansa. Yana gamawa Takawa ya fara magana cikin larabci da jefi jefin turanci, yace "sunana Sadiq Abdallah. Ni bakar fata ne mutumin kasar Nigeria. Ni tsohon mijin 'yarku ne Khairat kuma ni ubane a gurin tilon danta, Abubakar. Nazo ne gabanku yau ina neman afuwar ku akan abinda na aikata na rashin kyautawa a gare ku shekaru talatin da uku da suka wuce, sannan ina neman alfarmar a mayar mana da auren mu ni da matata idan kun amince" ya juya ya kalle ta cikin ido, yace "idan itama ta amince" shiru dakin yayi na tsahon lokaci. Khairat kam gaba daya kanta ya toshe , what is he doing? An jima bayan ya gama uncle Umar ya fara magana wacce take cikin larabci mai chakude da turanci "assalamu alaikum. Babu abinda zan iya cewa yau sai Alhamdulillah. A lokacin da Sadiq yazo neman auren khairat a gurina yazo ya nema, amma a lokacin na shafa wa idona toka ba tare da na bashi dama ba nace bazan bashi ba, saboda ina ganin zai zama abin kunya mu aurar da 'yar mu ga wanda ba balarabe ba, ban duba cewa a cikin abubuwan da ubangiji yace a duba kafin a bayar da aure babu kabila ko kalar fata ba, na tauye hakkin sji Sadiq din sannan kuma na tauye hakkin ita khairat din, dan haka zan iya cewa duk abinda ya faru nine sila, saboda