← Book details Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 190

Sashe 86

Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Uncle Aliyu bai samu zuwa abuja ba saboda aiyuka da suka yi masa yawa sai bayan sati biyu, yana zuwa baije gidan ba ya sauka a hotel, yaje unguwar a wayance yake tambayar mutane abinda suka sani tsakanin sultan da moon, amsoshin da yake samu sam basu yi masa dadi ba. A karshe dai ya kira ambassador inda shi kuma ya gaya masa ai yana gari ma. Da yamma yaje gidan, a compound ya tarar da ambassador tare da walid da kuma wani kyakykyawan yaro sun saka kaya iri daya shi da walid, har ya zauna yana kallon yaron dan sam bai san shi ba, suka gaishe shi tare shi da walid, uncle Aliyu ya dan tsokani walid sannan suka shiga gida. Sai a lokacin ya gaishe da yayan nasa, sannan yace "wannan yaron kuma fa yaya a ina ka samo shi?" Fuskar ambassador dauke da murmushi yace "Sultan sunan sa, shine babban dan mai martaba sarkin Abuja" da mamaki uncle Aliyu ya kalleshi yace "Sultan? Sultan din moon?" Daddy shima da mamaki yace "kasan shi ne?" Uncle aliyu yace "a'a bansan shi ba. Amma maganar sa ce ta kawo ni abuja. Sai dai kuma yadda ake gaya min labarinsa ba haka na ganshi ba" daddy ya gyada kai cikin gamsuwa yace "ai ba haka din yake ba, yanzu ne ya zama haka" nan ya fara bashi labarin sultan dalla dalla, a karshe yace "labarin yaron ne ya saka naji tausayinsa kuma nayi alkawarin gyara masa yaruwarsa" uncle Aliyu yanu tausayin rayuwar sultan sosai, amma duk da haka sai yace "gaskiya yaron abin tausayi ne, amma duk da haka yaya kana ganin ya dace mu dauki maimunati mu bawa yaron da yake da past kamar nashi?" Daddy ya gyara zama yace "shi aure wannan nufin Allah ne, yanzu ba maganar auren su ake ba tukunna, maganar chanzawa yaron yaruwa ake yi. Kuma ni sam ba domin maimunatu nake yi ba, ko da ace a yanzu sultan zai ce ya fasa auren moon to ba zan fasa ko daya daga cikin abubuwan da nayi niyyar yi masa ba". Suna cikin maganar sai ga sultan ya fito daga part dinsu, ya chanza wanka, yazo kusa da daddy ya durkusa yana shafa kansa yace "daddy zan dan fita" daddy yace "OK, Allah ya tsare. Make sure ka dawo kafin dinner" sultan yayi dariya yace "I won't miss it for the world" shima daddyn dariya yayi sanin halin sultan akan abinci, Sultan yayi wa uncle Aliyu sallama sannan ya fita. Har lokacin dinner uncle Aliyu yana nan, sosai yaji yana missing moon amma daddy yace kar ya kula mommy akan maganar ta, a dinner din duk su Habeeb har daddy suka saka sultan a gaba da tsokana shi kuwa ko a jikinsa sai zuba lomarsa yake yana kuma zuba surutu, sai dai in sun hada ido da uncle Aliyu ya dan sunkuyar da kai alamar kunya. Nan take uncle Aliyu yaji sultan ya shiga ransa saboda Sultan yana da shiga rai kamar Moon.

Daga Abuja direct yalleman uncle Aliyu ya koma, ya samu baffa ya tabbatar masa da cewa duk maganganun Munir karya ne, yace masa kawai yayi mata sharri ne dan yana so a tirsasa ta ta aure shi. Ai kuwa da baffa ya tisa munir a gaba da fada kamar zai dake shi da kansa, dan har hajja sai da fadan ya shafe ta. Shi dai munir yasan ba duk maganar sa ce karya ba, akwai 'yar gaskiya a ciki, amma fur kowa yaki sauraronsa. Yana fita waje kuwa suka kwashi 'yan kallo da nuraddeen wanda tun da yaji maganar yace wallahi duk sanda munir ya shigo gari sai jikinsa ya gaya masa tunda yayi wa Moon sharri irin wannan. Kaikayi ya koma kan mashekiya.

Wannan kenan;

Sultan yana kwance a daki daddy ya kira shi, ya daga da sallama, daddy yace masa "Maza ka shirya ka fito zamu tafi Niger mu dauko Moon" rasa masar da zai bayar yayi dan ji yayi komai ya tsaya masa, sai da daddy yace "kaji abinda nace kuwa?" Da sauri yace "yes, daddy" ya mike yana tunanin anya yaji abinda yace din kuwa? Ya daiji kamar ance Niger kuma ance Moon, sai a lokacin tunanin shi ya dawo, Moon zadu je su dauko a Niger, what? It means yau zai ganta kenan? Wani tsalle yayi ya sauko daga kan gado ya fito palo yana neman walid dan yayi confirming maganar, yana fitowa walid yana shigowa da sauri, ya kalle shi yace "a haka zaka je dauko amaryar taka" Sultan ji yayi kamar kafafuwan sa ba zasu dauke shi ba, da gudu ya koma daki, sai kuma gashi ya sake fitowa da gudu yace wa walid "yau zamu dawo ko kwana zamu yi?" Walid ya duba agogonsa yace "sai dai mu kwana ai, it is already late, dan dai daddy ya matsa tafiyar nan ne amma da mun bari kawai sai da safe" Sultan bai ji karashen maganar ba ya koma dakin, ba'afi minti biyar ba sai gashi ya fito ya shirya da jaka a hannunsa, babu walid a palon dan haka ya fita waje ya saka kayansa a motar da zata kai su airport, ji yake kamar yaje ya chichchibo duk wanda za'ayi tafiyar dasu suzo su tafi, gani yake kamar duk suna sane suke lakaki. It seems like eternity kafin su mommy su fito, yana ganin ta yaji jikinsa yayi sanyi, bata taba yi masa magana ba kuma ko sun hadu a compound in ya gaishe ta bata amsawa, bai kuma taba ganin ta a palo ba shi kuma bai taba tambayar dalili ba. Yaji dadi da ba mota daya zasu shiga ba, shi da daddy, ita kuma da Walid. Sai gab da magrib suka je airport, private jet din daddy suka hau, kafin isha suka sauka a Niamey, aka kai su wani gida shi da walid suka sauka, shi dai kawai jira yake yi suje gurin moon, sai da zasu kwanta walid yake masa bayanin moon fa ba'a nan take ba, tana agadaz amma sun taho suna hanya, goben ma sai wajen azahar zasu karaso. Ranar sultan yadda yaga rana haka yaga dare, wani irin farin ciki yake ji da wani irin son Moon a ransa, sannan kuma da fargaba, what if yanzu kuma tace bata son shi? Tunda shi ya jawo mata duk wannan wahalar da ta sha, yasan tana cewa bata son shi kuma daddy zai kore shi daga gidansa. He will then be back to square one. Washegari tunda yayi breakfast yake zaune, gabansa ne kawai yake ta faduwa, sai can bayan azahar Walid ya shigo yana dariya, sultan yasan me zai ce masa "sun zo, baka je kayi mata oyoyo ba" Sultan ya zauna akan kujera yana rikr kansa, Walid yayi dariya yace "jarumtar kenan? Kar ka bani kunya mana, ni da na saka ran zaka fita a guje kaje ka ture daddy ka rungumeta?" Hararar sa kawai Sultan yayi dan shi kadai yasan me yake ji a ransa. Walid ya sake cewa "kaga ni na fita yawo, in ga kama ragwantar ka fita driver zai kaika inda suke, zan same ku a can" Sultan bai iya fita ba har sai da daddy ya kira shi a waya yace sun kusa gama wa fa, su zo su same su. Da sauri ya dan watsa ruwa ko zaiji garau, ya chanja kaya yana kallon kansa a mudubi, maybe ma cewa zata yi bai yi kyau ba, ya chire hular ya ajiye sai kuma ya sake dauka ya dora. Sai kuma yaji haushin kansa, me yasa yake nin tsoron wannan 'yar mitsitsiyar yarinyar ne. Koma me zata ce ta fada din. Ya fita aka kai shi can gidan, ya fito ya jingina da jikin mota yana jiran fitowar su, wayarsa ya dauko yana daddan nawa amma sam ba wai yasan abinda yake yi bane, ji yayi ana kallon sa, kuma har cikin jinin jikin sa yasan cewa itace kuma yasan daga wanne side take, a hankali ya daga kansa, cikin idonta ya tsinci nasa. Ya Allah. He had no idea how much he missed her sai da ya ganta. Karfin zuciya ne kawai ya saka ya tsaya a inda yake, ji yayi kamar yayi abinda walid yace, yaje ya rungume ta, amma kuma anya rungume budurwa a gidan surukai dai dai ne? Ta rame, sosai, Allah ne kadai yasan abinda zai yiwa wanda duk ya takura mata da zai ganshi. Sama sama yaji daddy yana magana amma bai fahimci me yake cewa ba, sai da ya sake maimaitawa sannan ya fahimta, wayarsa ya dauko ya kira walid ya gaya masa sakon daddy sannan ya bude wa daddyn kofa ya shiga ya rufe da sauri ya juyo inda take tsaye, Allah yasa bata bace ba, tana nan kuwa tamkar wadda aka dasa, cikin kwayar idonta ya kalla ya fahimci cewa he have nothing to fear, kujerar mulkinsa tana nan daram a zuciyarta. Da sauri ta bar gurin ta tafi daya motar ta shiga, sai bayan data shiga sannan ya lura daddy ya sauke glass din window dinsa yana kallon shi, ya shafa kansa da sauri yana sunkuyar da kai kamar munafiki sannan ya shiga gaban motar ya zauna. Walid ya karaso suka hau hanyar airport.

Episode Fifty Eight : I Missed You
Chapter 86 · 0% Book details