← Book details Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 143 OF 190

Sashe 143

Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Episode Seventy Nine : The Lightening and The Thunder Ibrahim ya juya shima da sauri yana kallon inda nake kalla, yace "ya salam" yayi two steps gefe, Sultan ya fara takowa a hankali yana tahowa inda muke, idanuwansa a kaina har ya karaso gabana ya tsaya, ko kallon inda Ibrahim yake tsaye bai yi ba, ga mamaki na sai naga yayi murmushi, amma murmushinsa bai rage min ko kadan daga cikin faduwar da gabana yake yi ba sai ma karuwa da yayi, I know that smile very well. Ya miko min turaren hannunsa yace "see, I got it" ban karba ba kuma bance masa komai ba, kawai kallonsa nake yi ina jiran bomb din ya tashi. Ya sali kwalbar turaren ta fadi kasa ta fashe, har yanzu murmushin yakeyi, jajayen idanunwansa har kwalli suke yi, yace "kin gama sayen chocolate din? Naga kamar basket din bai cika ba. Let me help you fill it up, in ma gaba daya sweets din gurin kike so sai in saya miki" a hankali nace "sultan not here, let's go home" yace "oh let's go home? Kin gama kenan ashe, oh na tuna fa ashe dama ba sayen sweets kika zo yi ba kin zo ne ki ganshi, kuma kin riga kin ganshi, mission accomplished, so let's go home" jin maganganunsa nake tamkar wuta a kirjina, na juya na kalli inda Ibrahim yake tsaye naga bayanan, na dawo da ido na kan sultan, yana kallona yace "baya nan ai, ya gudu, ko baki gaji da ganin sa bane inje in kira wo miki shi? Am sure bai bar building din nan ba by now" mutane sun fara tsayawa suna kallon mu, na ajiye basket din hannuna na juya nayi hanyar fita daga gurin, tafiya kawai nake amma bana ganin gaba na sosai, how can Sultan even think that? Babu komai a hannuna dan ko waya ta ban dauko ba ballan tana in hau taxi. Na tsaya a packing space din na rufe fuskata da hannayena ina kokarin dai dai ta numfashi na, kaina ya chunkushe bana iya tunanin komai. Tsayuwar mota naji a gaba na, na bude ido na naga Sultan ya fito daga seat din driver ya zagayo ya bude seat din gaba, ba tare da yace min komai ba ya chusa ni a ciki ya mayar da kofar ya rufe, ya zagaya seat dinsa ya shiga ya ja motar a guje muka bar gurin. Na hadiye dacin da nake yi a bakina nace "how can you even think that Sultan? How can you hurt me like this?" Ba tare da ya kalle ni ba yace "what do you want me to think ehh? Ke kika matsa lallai sai mun fito yanzu and you also insisted sai munzo sahad, wai zaki sayi chocolate, since when did you start eating chocolate? You also kept delaying us unnecessarily. And I also saw you holding hands and whispering to each other. Tell me what do you want me to think?" Da hannu daya yake driving din kuma a guje yake tafiya yana ta overtaking motoci. Na lumshe idona saboda kaina da naji yana bala'in sara wa nace "ya kamata a ce kasan ni by now, Sultan ya kamata a ce by now kasan me zan aikata da kuma menene bazan aikata ba" yace "I tot I know you, but when it comes to him am not sure where I stand. He is your first love, har hawan jini kika samu sanda ya gudu ya barki saboda irin son da kike masa, you waited for him years after years, sanda ya dawo it is already days to our wedding, ko kince kin fasa aure na ma kinsan it is impossible Daddy ya fasa....." Na katse shi nima cikin daga murya nace "duk wannan tsahon lokacin dama abinda kake tunani kenan?" Shima ya daga tasa muryar "what do you want me to think? Kullum mutane suna gaya min you are too good for me, and I also know you are too good for me, you always kept secrets from me..." Na juyo ina facing dinsa sosai nace "kasan dalilin da yasa nake keeping maka secrets? Kasan babban dalilin da yasa tun farko ban baka labarin Ibrahim ba? Because I know you will act exactly the way you are acting now. You always let your temper get in your head and stop you from thinking clearly. Kawai ganina kayi tare dashi, baka tambayeni nayi maka bayani ba, you just conclude and start making accusations, a cikin mutane a cikin kasuwa Sultan, I don't think koma menene nayi I deserve something like that from you, you make a fool of me and you make a fool of yourself" ban taba jin raina ya baci irin na yau ba, sam na manta da mijina nake magana, na koma na kwanta akan kujerar na dafe kaina da nake ji kamar zai tsage gida biyu, I can feel my blood pressure rising. Can kasan muryarsa naji yace "she now calls me a fool" a hankali nace "am sorry. Ban taba jin raina ya baci irin na yau ba, ban taba zaton a ranka za kayi tunanin ina son wani bayan kai ba. Yazo gurina ya rike hannuna ne saboda ya dauka Amina ce, tare suka zo gurin da ita, ba wai da gan gan yayi haka ba, bayan ya gane ni ce ya bani hakuri, he saw that I got scared and was wondering me yasa zan ji tsoron ka" da sauri ya kalle ni yace "are you afraid of me?" Nace "No sultan am not afraid of you, am afraid of your anger. In ranka ya baci you are not yourself, nasan gani na tare dashi zai sa ranka ya baci, I was afraid of what you will do" na dora hannuna akan mara ta nace "Sultan so kake ka zama mijin da matarsa take jin tsoron sa? So kake ka zama uban da 'ya'yansa suke guduwa idan sunji muryarsa?" Na juya na kalleshi amma sai naga hankalinsa baya kaina, he is busy looking at the central mirror, yace "can you now tell me why he is following us? Idan a store yayi miki magana saboda ya dauka Amina ce yanzu kuma ya biyo mu ne saboda ya dauka Amina na dauko a mota ta?" Na juya da sauri na kalli bayan mu, a las, motar Ibrahim ce a bayan tamu, na dawo da hankali na kan Sultan naga his rage is coming back, jan idon daya fara raguwa ya dawo yanzu, ya kara gudun motar, nace "Sultan please stop the car" ko kallo na baiyi ba, na koma na kwanta a kan kujerar na saka hannu daya na dafe kaina dayan kuma na dafe marata da nake jin kamar zata tsage gida biyu, a cikin zuciyata nace "hang in there baby, everything is going to be alright" na fara jero sunanyen Allah a hankali ina neman ya kawo min agaji, na jima a haka sannan na bude idona na kalli inda muke, mun dau hanyar barin gari, har yanzu gudu sultan yake yi a motar, duhu yayi sosai dan haka few motoci ne akan hanyar na juya na sake kallon bayan mu, motar Ibrahim tana bayan mu still, oh dear God, what is Ibrahim thinking, na kalli Sultan nace cikin dasashshiyar murya, "Sultan ko ma menene kake tunanin yi please don't, annabi ya hane mu da yanke hukunci idan muna cikin fushi, Sultan please don't do something da zakayi regretting for the rest of your life" bai kalle ni ba ya miko hannunsa ya saka min seat belt sannan shima ya saka nasa, danshi na fara ji a kasa na na rintse idona hawaye suna bin kuncina, yanzu titin ya zama babu kowa sai motocin mu guda biyu, suddenly Sultan ya daga handbrake din motar, a take ta fara katantanwa a tsakiyar titin, da karfi ta daki motar Ibrahim da take dab damu, motar tasa tayi adungure sau biyu akan titi sannan ta gangara gefen titin, sultan ya taka burki motar mu ta tsaya chak a tsakiyar titin, na juya ina kallon motar Ibrahim da har yanzu take ta adungure, a karshe ta fada cikin wani katon rami dake gefen titin, na juyo na kalli sultan wanda shima motar yake kallo, fuskarsa babu dariya ko kadan, a hankali yace "die, you bastard". Kara na fara ji kamar daga nesa da murya kamar tawa, amma kuma kamar bani nake karar ba, can nesa naji kamar muryar sultan yana kwalla min kira, a hankali na fara ganin duhu a idona, daga baya na daina ganin komai. A hankali na fara dawowa haiyacina, sanyin AC naji yana ratsani. Nayi kokarin bude idona naji yayi min nauyi sosai, na motsa hannayena kadan ina son in dawo da karfin jikina, muryar Mommy naji tace " Maimoon? Maimunatu kina ji na?" Na dan bude ido na kadan na kalleta, da sauri ta taho ta rike hannuna fuskarta tayi ja alamar tayi kuka, na danyi kokarin yi mata murmushi amma ciwon da kai na yake min yasa murmushin ya zama kamar gyatsine. Na fara duba dakin da nake, asibiti ne, ga drip a hannuna, Mommy tana zaune gefena, Daddy yana tsaye a gefenta, Sultan yana daga can baya ya jingina da jikin bango, tsantsar tashin hankali ne a rubuce a fuskarsa. Motar Ibrahim na tuno yadda tayi ta adungure kafin ta fada cikin ramin. A take hawaye ya fara kwaranyowa daga idona, innalillahi wa inna ilaihirrajiun, Allah kasa mafarki nake yi yanzu za'a ce min ba gaske bane ba, amma yanayin fuskar sultan ka dai ya tabbatar min da cewa ba mafarki nake yi ba, Sultan yayi kisan kai a gaba na, Sultan ya kashe Ibrahim. Allah sarki Ibrahim why? Menene kake tunani me yasa ka biyo mu? Nasan bacin ran daya gani a fuskar sultan da yadda sultan ya fara acting a cikin store din shi ya saka ya biyo mu, he was looking out for me, amma banda abin Ibrahim koma me Sultan zaiyi min ai munfi kusa ni da shi, ballantana ma Sultan babu abinda zai iya yi min. Yanzu shikenan Ibrahim ya bar duniya, because of me, Sultan yayi kisan kai, because of me, na tuna da little Moon, na tuno fuskarta a hotonta
Chapter 143 · 0% Book details