Sashe 170
Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
ta karaso palon kamar wadda kwai ya fashewa a ciki, ya kalli Amina da sauri yace "what is she doing here?" Amina ta yamutsa fuska tace "dama ita ce mai son ganin naka bani ba" Amira ta karaso ta durkusa a gaban Ibrahim, da sauri ya matsa yace "tashi daga kusa dani kar kisa inyi amai" Amina taji wani takaici ya kama ta, ta rike kugu zata zazzaga masa masifa kuma sai ta dakata tana so taga yadda zasu kare kafin ta yanke hukunci, Amira ta fara magana muryarta na rawa "Ibrahim dan Allah ka yafe min. Nasan na munanawa rayuwarka, wallahi sharrin shaidan ne da son zuciya suka kaini ga aikata haka, dan Allah ka yafemin, ni yanzu yafiyar ka ita kadai nake bukata, ka yafemin ko na samu Allah ya yafemin ko rayuwata zata yi kyau" ya kalle ta ya dauke kai, sai kuma ya kalli Amina, ba dan abinda Amirar tayi ba da bai hadu da Amina har yayi mata wannan son da yake yi mata yanzu ba, ya tuna da little Maimunatun sa, ba dan abinda Amira tayi ba da ba'a haife ta ba, ya kuma tunawa da cikin dake jikin Moon, dan Sultan, shima badan Amira ta raba shi da Moon ba da ba za'a haifeshi ba. Babu wanda ya isa ya raya ko ya kashe sai Allah, kamar yadda babu wanda ya isa ya wuce kaddarar sa. Ya kalli Amira yaga yadda take kuka daga dukkan alamu va karamar nadama tayi ba, ya dauke kansa yace "na yafe miki, Allah ya yafe mana baki daya" ba Amira kadai ba, hatta Amina sai da tayi mamakin saurin yafiyar da yayi wa Amira, ya kuma kallon Amirar da take durkushe har yanzu a gabansa yace "tashi ki tafi, na yafe miki nace" da sauri ta mike tana kallon Amina sai kuma ta fita, ya dawo da kansa kallon Amina yace "I now have the most precious jewel in the world, why will I be unhappy?" Murmushi taji ya subuce mata, sai kuma ta sake bata rai, ya karaso kusa da ita yace "ko nima sai na durkusa a kasan ne?" Ta juya kamar zata fita sai ta tsaya ta juyo tace masa "ka dawo ku sake magana da Daddy, wannan karon da izini na". Dadi kamar ya kashe Ibrahim, sai kuma wani tsoron Allah ya kama shi. Haka fa Allah yake kallon mu idan munyi masa laifi mun roke shi gafara, sai ta duba yaga cewa mu din masu gafara ne ga 'yan'uwan mu? Kafin ya yafe masa ko akasin haka. Wannan ma wani darasin ne.