← Book details Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 140 OF 190

Sashe 140

Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Episode Seventy Eight : The Storm Bayan Wata Uku Rayuwa tana tafiyar mana sosai cikin jin dadi. Dan ni kam a bangare na bani da problem. Su Hajiya tun ranar da suka zo na kora musu bayani basu sake dawowa ba, su fa'iza su na dan zuwa kadan kuma sam ban taba daure musu fuska ba. Amira ma ta dawo twice, mu kan danyi hira kadan amma sam ba kasa sake wa da ita kamar da, mun koma kamar strangers. Kullum kuma in tazo bata da zance sai na aure, ta gaji da zaman gida yanzu aure take so dan yanzu kullum suna cikin samun sabani da mamanta. A bangaren Sultan kuma tunda ya koma aiki ya zama busy, dan kullum sai dai akai masa lunch dinsa office, sai bayan la'asar yake dawowa, amma kuma in ya dawo din in ba dole ba baya fita ko kofar gida sai dai in zashi masjid, kullum company sa kara habaka yake yi, dan yanzu da kansa yake karbar kwangilar gine gine yana yi, na government ko kuma na private mutane. Sultan ya rike addini sosai dan har mamaki yake bani yanzu, karatun qur'ani kam kullum sai yayi safe da yamma, wani lokacin na yamman muyi tare. Ni kuma babu abinda nake yi a gida sai koyon girki, dan a yanzu Asma'u tafara bari na ina yin abincin da kaina, sai dai ta dan ci gyarana kadan, a raina nakan ce 'ashe ma abin babu wahala, kawai sa kai ne' tun daga kan main dishes, snacks, drinks babu abinda asma'u bata koya min, tace so take yi in na fara yi wa Sultan girki duk abincin da yaci idan ba nawa bane ya ji ci salam. Duk abinda kuwa na dafa ko sultan baya nan sai na ajiye masa na bashi yayi tasting, Sultan kam ko abin bai yi dadi ba cewa yake yi yayi dadi duk da nasan wani lokacin alkunya kawai yake yi min. Soyayya tsakanin mu kuwa kullum karuwa take yi, ni da na dauka da anyi na dokin aure shikenan amma ashe ba haka abin yake ba, stamina din Sultan har mamaki take bani, dole na na yawo jakar magungunan daada na cigaba da amfani dasu. Mun je gida ranar da Daddy ya dawo daga England, tunda akayi biki na sai ranar naje gida, da gudu naje na rungume Mommy, ita kam kallo na kawai take yi dan gaba daya na chanja, nayi kiba na kara chika, fata ta har wani yellow take yi saboda haske. Sau da yawa in kawayena suka zo sukan tsokane ni suce ko ciki ne dani, amma ni nasan bani da komai, dan cikin wata ukun nan ko tsallaken period ban taba yi ba. Ranar a gida Sultan ya barni na wuni. A lokacin ne Amina take bani labarin yadda suka kare da Ibrahim, naji dadi duk da dai tace min yace bayason jin labarin sultan, kawai shi fatansa in am OK shikenan, nan take min complaint cewa he is becoming a little bit touchy, nayi dariya nace "then it is going more than I expected" ta bata rai tace "ya zaki ce haka, ina gaya miki cewa yana yawan tabani kuma kice min kina murna?" Nace "yi hakuri Amina ta, abinda nake so ki gane shine, Ibrahim was born and raised in yaroba land, they are Muslims and then they are yarobas, su a gurinsu it is nothing dan saurayi ya rike hannun budurwarsa" ta harare ni tace "waye yace miki saurayi na ne? We are just friends" Nace "OK let me rephrase my statement, su a gurinsu it is nothing dan aboki ya rike hannun abokiyarsa" yadda na fadi kalmar abokiyar ya saka mukayi dariya gaba daya, nace "nasan ki fa Amina, kuma nasan tun ranar da kika fara ganin sa kika zo kina santinsa" ta tabe baki tace "lokacin ai bansan waye shi a gurinki ba" nace "he is nothing a gurina yanzu, not even my friend, but he will soon be my brother in-law" tace "in ya daina taba ni ba" nace "ai ke zaki hana shi, next time ya rike miki hannu ki bata rai ki ce kar ya kuma ba kya so, daga ranar ba zai kara ba". Sai dare Sultan yazo daukana. Kamar ba zan fito ba saboda duk su yaya Walid suna gida ana ta hira da dariya, a nan na fara matsar kwalla wai ni dan Allah sultan ya barni in kwana sai gobe na koma, ni kaina da nake fada nasan it is impossible, dan in dai zan kwana a gida to tabbas sultan zai biyo ni mu kwana tare. Mommy ce ta rakani har mota amma ita ma kamar ba zata barni in tafi ba, muna jan mota na dora hannu aka na rusa kuka wai ni ya mayar dani gidan mu. Gefen titi ya samu yayi packing sai da ya tsotse hawayen fuskar tas sannan ya dashi motar muka tafi kuma yace in dai na sake wani kukan abinda yafi haka zai yi min ba ruwansa da cewa a titi muke. Na san zai iya aikatawa dan haka nayi shiru da baki na. Muna zuwa gida sai da ya tabbatar ya mantar dani 'yan gidan mu sannan ya rabu dani. Ranar wata Friday muna zaune palo da asma'u da baba gaji da wasu daga 'yammata na, baba gaji tana ta bamu labaran abin dariya muna ta darawa without a care in the world, ina yi amma ina kallon agogo, nasan sultan yana hanya by now, ai kuwa ba'a jima ba sai ga shi ya shigo. Yana shigowa duk suka nutsu, haka nan sultan yake da wannan kwarjinin, duk inda ya shiga sai kaga mutane suna shakkarsa ko da kuwa bai yi musu magana ba. Ya zauna a kujera, duk suka gaishe shi sannan suka fita, nayi masa sannu da zuwa, ya amsa a hankali yana jingina kansa a bayan kujerar, na tashi na dauko masa pineapple drink din dana hada dazu, na kawo na zuba masa a cup na mika masa, bai karba ba ya zauna yana kallona, nasan me yake nufi nayi murmushi na zauna a cinyarsa na dafa kafadar sa da hannu daya daya hannun kuma na dauki cup din drink din na fara bashi a baki, sai da ya shanye cup din tas sannan ya dauke kansa, na karo masa wani na sake bashi, wannan karon a hannunsa ya karba yace "let me guess, ki kika hada wannan drink din" na washe baki nayi fari da ido nace "you guess right, this drink was made by yours truly, Asma'u bata ma san nayi ba" yace "wow, wannan matar fa so kike ki fi asma'u iya girki, kuma it is like duk abinda kikayi yana da wani unique taste na musamman" naji dadi sosai nace "thank you Darling" ya juya wuyansa, kashin wuyan yayi kara alamar gajiya, nace "you are overworking yourself honey, ya kamata ka ke rage aikin nan kana hutawa fa" ya kwantar da kansa a kirjina yace "I know, shi yasa nake shirya mana tafiya zuwa Maldives, karshen watan nan in sha Allahu" na tashi tsaye na fara tsallen murna yana ta yi mini dariya, sai da na gama murna ta na zagayo bayansa na saka hannayena biyu akan kafadarsa na fara yi masa tausa, he feels so tense, a hankali nake matsa masa kafadunsa zuwa wuyansa, yayi ajjiyar zuciya yace "God, that feels so good" na cigaba dayi masa tausar har sai da naga yayi relaxing sannan na daina na zagayo gabansa naga kamar wani abu yana damunsa, nayi kneel down a gabansa na dora hannayena akan cinyarsa nace "me ya faru ne a office din yau? Ya dan saki ransa yana murmushi yace "why did I marry a psychologist?" Nace "because you are lucky" ya shafa fuskata yace "you are damn right I am" kamar ba zai cigaba da magana ba kuma sai yace "uncle galadima ne yazo office dina dazu. Dama tun dadewa yake cewa zai kawo min ziyara. To yau yazo muka zagaya dashi yaga gurin sannan aka zauna akayi addu'ah" yayi shiru, nace "then what's the problem?" Yace "kafin ya tafi ya kirani gefe yake ce min yana son in ringa zuwa fada ana zama tare dani, wai I belong there, a kusa da Takawa. Ni kuma na gaya masa NO, I am happy now, I have you, I have my job, bani da wani problem. He still insisted wai inje inyi tunani akai" na dan jinjina maganar a raina kafin nace "to yanzu wacce shawara ka yanke?" Yace "my answer is still no. Yanzu ina zaune lafiya Takawa ya dauke idonsa daga kaina, maybe ma ya manta da existence dina, amma ina zuwa kusa dashi shikenan na zama nama, ba lallai ne ma ya barni in shiga ba, zai yi disgracing dina ne a gaban mutane kuma ni na jawowa kai na. Besides, ina shiga gurin people will think kamar I want the throne" dariya na fara yi a hankali, ya tsaya yana kallona fuskarsa da mamaki, yace "menene abin dariya kuma?" Nace "since when did Sultan care about me mutane suke tunani akan sa?" Shima dariyar ya fara yi a hankali ina taya shi, sannan yace "na chanza da yawa ko?" Na mike na koma na zauna a cinyarsa ina shafa fuskarsa nace "yes ka chanza my Darling, and I am so proud of you. Amma yanzu ka ajiye Takawa a gefe, ka ajiye abinda mutane zasu ce a gefe, tell me what you really want" ya jima yana kallon gefe yana tunani sannan ya juyo yana kallona yace "lokacin da ina yaro, lokacin kakana yana da rai, there is nothing I want more than the throne. Kullum abinda yake gayamin shine the throne is mine, kullum idan yana zaune a fada zai saka ni in zauna a gabansa, telling me to learn, saying that one day I will rule. Wannan yana daya daga cikin abinda yasa na zama so furious lokacin da babana ya daina zuwa fada dani, a lokacin ina tunanin sarauta is what I was born for dan haka karbarta kamar an cire min purpose na rayuwata ne, amma as I grow up, musamman bayan haduwa ta da ke, na fahimci cewa there is more to rayuwata
Chapter 140 · 0% Book details