← Book details Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 128 OF 190

Sashe 128

Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sa da yawa, aka shirya musu party ana ta murna, aka gaya mana cewa ai murnar kammala karatunsa akeyi, muma mukayi ta murna muna taya shi farinciki. Bai dade da dawowa ba sai suka samu sabani da mahaifinsa, rana daya muka neme shi muka rasa a gidan nan, ba karamin tayar da hankali mahaifinsa yayi ba saboda kowa ya san duk cikin 'ya'yansa babu wanda yake so kamarsa. Yaya ta tada hankalinta, kullum ana cikin tara malamai da addu'ar Allah ya bayyana shi. Rannan muna zaune da daddare tare da Yaya kawai sai gashi ya shigo palon, hannunsa rike da hannun wata yarinya, balarabiya. Muka tashi da murna amma sai muka ga yaya sam bata murna sai ma tashin hankali da muka gani a tare da ita, aka aika aka gayawa sarki sai gashi ya taho da kansa, mu dai duk muka fita muka basu guri, basu fi awa daya ba sai gashi ya fito rike da hannunta ya bude motarsa ya shiga ya fice daga gidan. Sai daga baya muka samu labarin ainahin abin da ya faru, yarinya ce yake so balarabiya, ya nemi babansa ya nema masa auren ta amma baban yaki, wannan shine dalilin da yasa ya tsallake yayi tafiyarsa yaje ya nemi auren nata da kansa, aka bashi ita aka daura musu aure sannan ya dauko ta ya taho da ita, a tunaninsa tunda ya riga ya aure ta ai dole uban ya karba. Amma da suka zo maimakon uban ya karba sai ya kara tunzura yana ganin kamar ya nuna masa bai isa dashi ba tunda yayi aure ba da sanin sa ba. Hakan ne yasa shi kuma ya dauki matarsa suka yi tafiyarsu. Ba'a kuma jin labarin sa ba sai bayan shekara daya. Shima wannan karon muna zaune sai gashi ya shigo gidan, hannunsa daya rike da wannan balarabiyar, daya hannun kuma yana rungume da dan jariri. Wato tunda ya kawo musu suruka sunki karba shine yanzu ya kawo musu jika. Ai kuwa wannan karon yaci nasara, dan kallo daya kakan yayi wa jikan ya tattara son duniya ya dora masa. Tun daga nan Khairat ta tare a gidan nan. Yarinya ce nutsatstsiya sosai, tana da hankali da girmama mutane. Farkon zuwanta sam bata iya hausa ba, amma a hankali ta fara koya. Duk gidan nan, 'ya'yan gida da mu bayi, dama wadanda suke shigowa su fita, babu wanda baya son khairat, babu kuma wanda bai san irin son da mijinta yake mata ba dan baya boyewa ko a gaban waye kuwa. Shi kuwa wannan dan jaririn wanda daga baya muka fahimci babansa ya saka masa sunan sa saboda tsananin son da yake masa, sai ya zama an kasa ban bance waye yafi sonsa tsakanin iyayensa da kuma kakansa. Tun yana jariri muka fahimci cewa ba sunan babansa kadai yaci ba harda halayensa, duk duk kiriniyar da babansa yayi yana jariri shima ita yake yi, kamar copy dinsa ne aka ajiye, sai dai yafi kama da mahaifiyarsa. Karamin Sarki yana da shekara biyu a duniya rannan kawai muka tashi babu khairat babu alamunta, babu abinda ta dauka a kayanta, ko danta bata dauka ba, kuma babu wanda yace yaga sanda ta fita. Abinda kuma ya fi bamu mamaki a tafiyar tata shine, babu wanda ya neme ta" nayi sauri na katse ta nace "ban gane me kike nufi babu wanda ya neme taba, mijinta fa wanda kika ce yana yi mata soyayya kamar rai?" Tace "shine abin mamakin Allah ya taimakeki, duk zafin ransa, duk, duk taurin zuciyarsa. Mun dauka zai bita amma ko kofar gida bai je ba. Komawa yayi tamkar wanda aka chanza shi da wani, tamkar ba shi ba gaba daya yayi sanyi duk karfin sa babu. Kamar an zare masa ruhinsa an bar gangar jikin. A rana daya aka saka aka kwashe duk kayanta aka rufe dakinta. A ranar aka taramu aka umarcemu da ko sunan ta kada wanda ya sake ambata a gidan. Bamu tambayi dalili ba kawai dai munyi biyayya. Kwana biyu da tafiyar ta karamin sarki ya galabaita da kukan neman ummin sa da daddyn sa, har zazzabi yayi, ranar da safe ina gurin yaya ina ta faman rarrashin karamin sarki sai ga babansa ya shigo, yana shigowa yaron ya fara zamewa daga hannuna yana kokarin tafiya gurinsa amma abin mamaki ko kallon inda yake bai yi ba, tamkar bai san shi ba, ya shiga ya gaishe da mahaifiyarsa ya juya ya fice, yaron yana ta kiran daddy daddy yana kuka. Tun daga ranar abinda ya cigaba da faruwa kenan, kamar yadda aka goge duk wani abu daya shafi mahaifiyar karamin sarki a gidan nan haka ya zamo tamkar an goge duk wani digo na soyayya tsakanin karamin sarki da mahaifinsa" tasa mayafinta tana goge hawayen idonta, nace "amma hajiya fa, an auro ta lokacin?" Ta girgiza kai tace "ai Hajiya sam basu zauna da mahaifiyar karamin sarki ba, sai bayan da suka rabu da shekara biyu ma sannan aka yi aurenta" ji nayi kaina ya daure, saboda all this while abinda nake tunani shine Hajiya ce ta raba maman sultan da babansa, ita ce kuma ta raba tsakanin su ta saka kiyayya a tsakanin su, things are not always what they seem, na sake tambaya "to daga baya kenan Takawa ya hadu davita har suka fara soyayya suka yi aure?" Tace "Ranki ya dade ai babu soyayya, auren hadi ne, 'yar 'uwarsa ce ai, kakansu daya. Kawai kiransa akayi akace masa an hada shi aure da wance yace to, daga nan akayi auren, anayin auren suka tafi kasar waje tare wai itama zata yi karatu, shekarar su daya suka dawo da yarima Abbas yana karami" na danyi digesting maganar kadan, wanne karatu ne akeyinsa a shekara daya?. Taci gaba da labarin Sultan tace "daga nan sai kakansa ya dauke shi, ya mayar dashi dakinsa, hatta kayan sakawarsa a can suke, gata da soyayya sosai ya nuna masa, a haka har yaron ya saki jikinsa ya daina kuka, amma kuma duk da kankantarsa bai manta da mahaifinsa ba, dan duk inda ya ganshi zai tafi gurinsa da gudu, amma ko kallon inda yake baya yi, in yazo ya rike kafarsa sai ya ture shi ya fadi yayi tafiyarsa. A gurin sarkin lokacin kuma babu tamkar karamin sarki, dan har bacci akan gado daya suke yi, ko taba shi babu wanda ya isa yayi hatta su Yaya da Nani, abin ya dami yaya kwarai amma duk sanda tayi magana to ranar kuwa zata ga bacin rai. A haka har yaron ya shekara goma, ya sangarce sosai babu mai saka shi babu mai hana shi, ko tafiya zuwa kasashen waje tare yake tafiya dashi, a fada suna tare, in taro zaije tare zasu tafi. Rannan kawai da safe aka ga basu fito sallar asuba ba, aka shiga za'a tashe su amma sai jikan ne kawai ya tashi, kakan Allah ya karbi ransa a cikin bacci. Wannan mutuwar ta tayar da hankalin kowa a masarautar nan amma babban abin tausayi shine karamin sarki, bai saba da kowa ba sai shi bai san kowa ba sai shi, dan haka rasa wanda zai rarrashe shi akayi, kwata kwata ya hana a yi wa gawar sutura, sanda mahaifinsa yazo muka ji dadi cewa an samu mai rarrashinsa amma yana zuwa sai ya dauke shi chak ya tafi dashi wani tsohon store ya daure masa bakin sa, ya daure masa hannayensa da kafafuwansa ya rufe shi a dakin yayi tafiyarsa. Babu wanda bai tausayawa yaron nan ba, kuka biyu muka yi a lokacin, har yanzu ina iya tuno wani irin gunjin kuka daya ringa yi babu baki, kamar ransa zai fita, wallahi ban dauka yaron nan zai yi rai ba, na dauka zuciyarsa zata buga ya mutu, amma zuciyarsa mai karfi ce. Haka ya kwana anan sai da safe sannan ya fito dashi kuma ya gaya masa in ya kuma yin kuka sai ya kuma daure shi. Bayan anyi sarauta su Hajiya suka dawo nan mu kuma muka koma sabon guri tare dasu Yaya, nan Hajiya tace abar mata Karamin Sarki, Yaya sam bata so hakan ba amma sai ta barshi din wai ko hakan zai sa ya saba da mahaifanan. Mu dai daga nan bamu kuma jin labarin da yake ciki ba sai kawai muka ji labarin wai an kai shi Lagos gidan kangararru, Yaya ta tayar da hankalinta sosai, amma ko ta kira Takawa ta yi masa magana sai ya nuna mata kamar zai aika a dawo dashi amma shiru, sai da ya shekara biyu acan sannan Yaya ta aika galadima ya dauko shi, tace masa ya mayar dashi gidansa ya zauna acan, ai kuwa nan rigima ta tashi dan har saida Yaya tayi sharia tsakanin sarki da galadima akan me yasa galadima ya dauko karamin sarki daga Lagos, wannan shi yasa duk 'yan uwa kowa ya dauke hannunsa daga kan maganar karamin sarki har aka turashi kasar waje karatu babu wanda yayi magana, amma ni nice shaida, duk watan duniyar nan sai Yaya ta saka an sauke masa alqur'ani da niyyar ya zama kariya a gare shi a duk inda yake". Jin tayi shiru yasa na gyara zamana nace "to yanzu baba gaji, duk gidan nan babu wanda yasan ina ne garin su mahaifiyar Sultan?" Tayi shiru tana tunani, sannan tace "to mu bayi dai kam bana jin akwai wanda ya sani, amma Yaya ba zata kasa sani ba, amma kuma ranki shi dade bana jin zata gaya miki, dan da zata fada da duk tsahon shekarun nan da ta gayawa karamin sarki". Na koma na kwanta na lumshe ido na ina juya maganganun a raina, na samu wasu amsoshin, amma kuma amsoshin sun kuma tayar da wasu tambayoyin. Menene gaskiya dalilin rabuwar iyayen sultan? Menene dalilin da yasa soyayyar mahaifinsa ta koma kiyayya a lokaci daya? Menene kuma dalilin da yasa ake boye labarin mahaifiyar Sultan ba'a so kowa ya sani? Na tuna da labarin da Sultan ya bani na amsar da Yaya ta bashi sanda yayi mata irin wannan tambayar 'to protect the family name' but what kind of protection? Follow me on wattpad @maman_Maimoon
Chapter 128 · 0% Book details